NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL


Zaune yake bakin gadon rik’e da take-away d’in da yayi yana ci, sai Richard dake kan kujera da computer a k’afafunshi yana ta cakula, sun jima haka yana bashi bayanai kafin ya aje computer gefe ya taso ya karb’i abincin hannunshi ya zauna yana kallonshi yana fad’in “Yanzu haka sun dawo gida, na bibiyi cctv cam茅ra dake kan layin Churchill 172 har zuwa cam茅ra dake k’ofar shiga gidan, ina tabbatar maka matarka na cikin aminci yanzu a cikin gida.”

D’an k’aramin tsaki yayi ya mik’e tsaye yana zuba hannaye aljihu yace “Ya zanyi na dinga ganin duk wani shige da ficenta? Ina so na dinga sanin inda ta je? Inda ta zauna? Da wa ta had’u? Su waye a bayanta da kuma gabanta? Ina so na san komai Richard ya zanyi?”

Mik’ewa yayi yana saka lomar taliyar a bakinshi yace “One minute.” Wata jaka ya bud’a ya shiga dubawa wani abu, da sauri ya juyo yana mik’a mishi abun yana fad’in “Yes i found it.”

Karb’a yayi ya shica kallon abun kamar botir d’in riga, wani murmushi ya saki yace “Ka tabbatar zaiyi aiki?”

Cike da tabbaci yace “Why not? Try.”

Murmushi ya sake yi yace “Thank u.”

Fita yayi daga d’akin yana fad’in “Zamiyi waya.”

Daga nan gida ya koma inda ya sameta tare da kaka zaune, bata d’aga kai ta kalleshi ba, tsaf suka gaisa da kaka har ya kalleta yace “Ya jikinki?”

D’aga kai tayi ta kalleshi, ba yabo ba fallasa ta amsa da “Fine.”

Juyawa yayi zai wuce duk sai yaji ya tsargu bai jin dad’i, a take kuma tunanin barin gidan ya fara mishi yawo a zuciya. Yana shiga da sallama ya same ta hawaye kawai take yi, zaune yayi yana fuskantarta bai ce komai ba, yanda taji yana kallonta kuma bai ce komai ba yasa ta d’ago kanta ta kalleshi, share hawaye ta sake yi tace “Ka dawo kenan?”

Ba tare daya daina kallonta ba yace “Um.” Tab’e baki tayi tace “Ina so na koma gida, yaushe zaka mayar dani?”

Tagumi ya zuba yana kallonta kamar mai son gano wani abu, ajiyar zuciya ya sauke yana d’auke hannun yace “Farhanatu kin san me? Kin bani mamaki sosai, ban tab’a tunanin zaki iya yin abinda kike yi yanzun ba.”

Girgiza kai yayi yace “Kinsan dalilin zuwanki garin nan kuwa? Shin kinsan dalilin da yasa Abba yace zaiyi hushi dani idan har na b’ata miki rai?”

Girgiza kai ya sake yi yace “Duk baki sani ba? To bari kiji dalilin Abba, a sanin da Abba daya miki yarinya ce ke mai hankali nutsuwa da ilimi da sanin takamata, bai tab’a tunanin zaki jefar da tarbiyar daya miki ba, amma gashi yanzu kina kunyatashi ba tare da kinyi tunanin cewa duk abun tsiyar da kikayi sai an nunawa Abba dake k’abari ba, Farha me yasa kika canza haka? Saboda so na ne?”

D’orawa yayi da “Kinsan me yasa na turoki garin nan? Burina kawai shine ku had’a kanku ke da ita, saboda a gaskiya in fad’a miki ba zan iya sakinta ba, har yanzu tana d’auke da cikina a jikinta, na d’auka idan kika ga inda take rayuwa da yanda ta tarbeki da mutuntawa zaki cewa baki kyauta ba kuma ki d’auri niyyar gyarawa, amma me kike aikatawa yanzu? Sai kike abu kamar wacce bata da hankali ko bata san hallici da daidai ba.”

Girgiza kai yayi ya mik’e tsaye yace “Girmamaki a matsayin yer uwa da kuma kasancewarki uwar gidana yasa na jima ina guje miki ranar da zata zo ki kaita bango, banji dad’in abinda ya faru ba d’azu, amma ke kika jawa kanki Farha, idan zaki nutsu kiyi hankali komai zai zo miki da sauk’i, idan kuma kin k’i zaki wahala, tunda ni dai d’an adam ne mai yawan tawaya da kasawa, yanzu haka na so zamanmu anan gaba d’aya, amma abinda ya faru yasa dole zan d’aukeki daga nan, amma fa sai kiyi hak’uri da duk abinda zaki gani.”

Hanyar fita ya nufa yana fad’in “D’auko kayanki ki same ni a waje.”

Gum tayi kamar babu rai a jikinta, maganar data fi tafiya da ita ita ce ta Abba, duk jikinta ne taji yayi sanyi tana jin kunyar Abba, dan bawan Allah nan ya sota fiye da yayan daya haifa, ya fifitata a cikinsu ya d’aukakata da girmama maraicinta, ya mata tarbiyya ta addinin islama, lallai sai taji kamar tana wulak’anta tarbiyyar daya mata ne. Sarah kuma ta tabbatar gaskiya ya fad’a ta kaita bango ne, to ya zatayi?

Had’a kayan ta shiga yi jikinta a sanyaye tana ci gaba da tunani akan abinda ya fad’a mata, tana mamakin canzawarta sosai, amma tayi niyyar zata tsaya gabanshi ta fad’a mishi cewa son shi ne ya jawo hakan, kishinki take sosai saboda da soyayyarshi ta girma, haka ta gama had’a kayanta sai wanda Sarah ta bata jiya ta saka, aje su tayi kan gadon ta juya ta fito jiki duk a mace babu k’wari. Ta hangesu zaune tare da kaka Sarah na waya, har ta juya ta kai bakin k’ofa sai kuma ta aje jakarta ta juyo, tunkarosu tayi cikin takon nutsuwa ta shigo falon, Sarah na ganin haka ta sauke k’afarta dake kan cinyarta ta kashe wayar tana kallon a tsiyace. Kallon kaka tayi duk da tasan bata jin hausa amma haka ta dage tace “Ku gafarce ni dan Allah, ni zan tafi nagode da kulawarku akai na.”

Kallon Sarah tayi a harshen french tace “Je doit mon aller, merci 茅norm茅ment, vraiment tu est gentille plus que moi, oublie toute ce que je te fais pour toi et excuse moi, merci ma puce.”

Kallonta Sarah tayi ta mik’e tsaye, matsawa tayi kusanta ta kamo hannunta tace “Ki yafe min nima na mareki ba da son raina ba, ki gafarce ni.”

Girgiza mata kai tayi tace “Karki damu da wannan ai ni na ja komai, dan Allah ni dai ki yafe min.”

Girgiza kai tayi ita ma tace “Ba komai, amma me yasa zaki tafi? Ko dan abunda ya faru ne? Ki zauna mana hakan ba zai sake faruwa ba.”

Cikin sanyin jiki tace “Shine yace na shirya mu tafi zai canza min gida, na b’ata mishi rai ne shiyasa.”

Allah sarki Sarah sai taji Farha ta bata tausayi, jawota tayi jikinta ta rumgume kamar d’iyarta tana fad’in “Kiyi hak’uri kinji ki yafe min na shiga tsakaninki da mijinki, ba’a son raina haka take faruwa ba nima, k’addara rayuwata ce ta zo a haka.”

Da fari kasak’e tayi tana sauraron yanda take daddab’a bayanta, amma kuma har k’asan zuciyarta sai taji wani tausayinta ita ma da kuma k’aunarta a ranta, a take ta iya tunawa da maganganun malamnsu idan suna musu wa’azi akan kishiya, suna fad’a musu kishiya yer uwa ce, idan ka kyautata niyyarka da zuciyarka ka kumayi fatan samun ta gari saika dace da ita, sannan ba duka aka taru aka zama d’aya ba, wasu ne ke b’ata wasu, haka ma suna fad’a musu idan mata sun had’a kai mijinsu zaiyi farin ciki ya kuma so su ya girmama su. Rumgume Sarah tayi ita ma tana fad’in “Ba komai ma puce, a yanzu ni na amince mu zauna tare, ke ma ai mijinki ne.”

D’agowa Sarah tayi tana sunkuyar da kai da fad’in “No no no! Ki manta da maganar nan ma, zan bar miki mijinki ke kad’ai.”

Dariya Farha tayi ta kamo hannun Sarah tace “Wallahi ba zan yarda ya rabu dake ba nima, haka kawai na yarda na sara mutuniyar kirki irinki.”

K’ok’arin zame hannunta ta shiga yi tana ja baya tana cewa “A’a fa, A’a fa bana so, mijinki naki ne ke kad’ai, ki rik’e kayanki.”

Biyota Farha tayi suka zauna tare kan kujerar suna dariya da kace-nace inka gansu a lokacin saika rantse tun fil-azal dama haka suke. Acan k’asan zuciyarta ji take dama abun haka yake da sauk’i, idan dai har zaka saka Allah to komai zai zo maka da sauk’i, ba zata yarda tayi sake yar daraja da mutumci da soyayyar da suka rage nata a zuciyarshi su k’arasa kwab’ewa tayi ba uwar ba ribar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button