NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Kallon Salahadeen tayi dan ya sake mata gwaro gwari yanda zata fahimta, ba tare daya kalli idon Mamar ba yace “K’orafi take me yasa kika barta.”

Kallonta tayi da murmushi tace “Kiyi hak’uri kinji, wannan ne ya aike ni k’auye.”

Yanda ta nuna Salahadeen yasa Sarah kallonshi, shima da sauri ya kalli Mama jin tace wai ya aiketa, cikin daka wata uwar fuska ya kalleta, dauuuuu! Yayi saurin rintse idonshi saboda yanda idonshi suka dakeshi, fararen ido amma k’wayar kalar yanda gashinta yake bak’i bak’i da ratsin k’asa, fuskarta ta fito tass a cikin hijab d’in daya mata kyau kamar dan ita aka d’inka shi.

Mayar da kallonta tayi ga Mama wacce ke shafa fuskarta tana kallon ciwon dake goshinta tana fad’in “Me ya same ki anan? Ba dai fad’uwa kikayi ba ko?”

Duk da bata ji ainihin me tace ba amma dai ta gane tambayar ta take yi, da sauri ta nuna mata d’aki ta shiga alamta mata da hannu tana fad’in “Na fito daga wanka ne kawai na fad’i anan.”

Hancinta Mama ta kama tana fad’in “Ki rage k’iriniya.”

Iffa dake tsaye haushi ya isheta ne tace “Malama ki d’an gyara mana mu gaisa da mahaifiyarmu ko.”

Wani irin kallo ya wurga mata da yasa ta yin k’asa da ido, Mama kuma kallonta tayi tana nunata da yatsa tana kalkad’ashi da fad’in “Iffatu, Iffatu ki kiyaye ni wallahi ki kuma kiyaye duniya.”

K’wafar da yayi ce tasa Sarah sake kallonshi, bai kalleta ba sai haramar mik’ewa da yayi ya tashi tsaye, kallonshi Mama tayi tace “Kaje ku dawo ku fara shirin tafiya k’auyen nan kuma.”

Cikin kasala yace “Cikin sauri haka Mama? Da mun barshi har na kammala sabgar nan dake gabana.”

Kallo ta mishi mai kama da harara tace “Sabgar ina kuma? Kaga kar ma ka yarda ku fara sani yawan surutu wallahi, shiryawa zakuyi k’arshen satin nan ku tafi dukanku har da matar taka.”

A hankali ya kai kallonshi kan Farha, ido biyu sukayi hakan yasa shi d’auke idonshi ya kalli Mama yace “To.”

Juyawa yayi ya saka takalminshi ya fita daga gidan, sai lokacin suka shiga gaisawa da Mama da tambayar ya k’auye da mutanen, ciki suka shiga dan cire kayansu inda Sarah kuma ta gyara durk’ushinta da kyau ta shiga fad’awa Mama “Mamie nima zaki sakani, malamin yace wai idan ina son zuwa kullum sai an kaini, Mamie ina son zuwa.”

Mama ce ta d’auki wayarta ta sake dannawa Salahadeen kira, yana d’auka tace “Idan ba kayi nisa ba ka dawo dan Allah, da alama wani abu take fad’a mai mahimmanci kuma bana fahimtarta.”

Can k’asan mak’oshi yace “Mama ki rabu da yarinyar nan, ba zai wuve shirmenta bane take fad’a.”

A hankali tace “Ni da ita muke shirmen Salahadeen?”

Da sauri yace “A’a Mama, yi hak’uri gani nan zuwa.”

Kashe wayar tayi sai lokacin su Mamuh suka fito, zaune sukayi sai Mamuh data shiga duba kayan da Mama ta shigo dasu tana dubawa tana fad’in “Mama me kika kawo mana?”

Yana shigowa da sallama Farha ta mik’e cikin jin haushi ta shige d’aki, shima cikin jin haushin ya kalli Sarah dake ta lagudar masa uwa yace “Ke menene kike fad’a?”

Kallonshi Mama tayi tace “Ahhh, miye na b’acin ran?”

Da k’yar ya saita fuskarshi yana ci gaba da kallonta, tashi tayi tsaye saboda sanyin da k’afafunta sukayi, cire hijabin tayi ta aje kan tabarma tana shirin zaunawa hannun kujerar da Mama ke zaune, wata uwar harara ya wurga mata tare da fad’in “Baki da tarbiyya ne? Ya zaki zauna k’ugu d’aya da ita?”

Cikin tsawa yace “K’asa malama.”

Da sauri ta durk’ushe k’asa tana rik’e da hannun Mama, kallon Mama tayi da ke fad’in “Tashi zauna ke rabu dashi.”

Ganin kallon da yake mata yasa taji d’ar d’inshi dole tayi k’asa da kanta, kallonshi Mama tayi tace “Salahadeen anya ba amanata ka ci ba? Alamu bai nuna min ka kula da ita ba.”

Shiru kawai yayi sai Sarah daya kalla yace “Nace me kike son fad’a ma Mama ne?”

Kallon Mama kawai tayi tace “Mamie ina son zuwa wajen karatun nan nima, amma malam yace sai dai wani babba ya kini kuma a min uniforme, sannan Mamie naji dad’i sosai karatun da malam ya mana, kinsan me ya koya mana?”

Kallon Salahadeen tayi hakan yasa shi cikin dakakkiyar murya yace “Wai tana son zuwa makaranta ita ma kuma malam yace wani babba ya kaita, kuma tana tambayarki kinsan abinda ya fad’a mata?”

Da sauri ta kalleta tace “Ba dai kina so ba, zakije insha Allah, asabar d’in nan dake za’a fara.”

Salahadeen ne yayi saurin cewa “Mama ba zai yiwu ba fa, ina tunanin turata garinsu ne yau ko gobe.”

Da mamaki ta kalleshi tace “Ban gane turata ba? Sai kace wata jaka, kuma me akan me zaka turata ita kad’ai, ba ma wannan ba komai yayi daidai ne?”

Cikin jimami sosai yace “Mama mahaifinta ya rasu, tana so tayi jana’izarshi da kanta.”

Da k’arfi ta kalleshi ta zaro ido tace “Kuma ta sani? Yaushe?”

Jinjina kai kawai yayi alamar eh, kallonta tayi da tausayawa wacce ita ma ke kallon bakin mama tace “Allah sarki baiwar Allah, kuma kaga bata damu ba kamar bata sani ba.”

A hankali ya d’an saci kallonta, sai yaji yanda mama tayi maganar ma ya k’ara tusa mishi wani mugun tausayinta, shi kanshi ya jinjina juriyarta sosai, kallonshi Mama tayi tace “To yaushe zata tafin?”

Saida yayi huci yace “Idan dai yau bai samu gobe insha Allahu tana barin garin nan.”

Langab’e kai tayi tace “Allah ya tabbatar da alkairi to, Allah ya kaita lafiya.”

Da sauri Iffa tace “Yaya Salahadeen yanzu zaka saketa kenan?”

Wata harara ya zuba mata k’asa da sama ya d’auke kanshi, Mama ce ta kafe Sarah da ido tace “To ba dole ba, baiwar Allah bata da damuwar komai.”

Tabbas taji me Maman tace, wani murmushi ta saki na jin dad’in yanda ta iya nasarar b’oye damuwarta cikin mutanen da har yanzu bata gama saninsu ba.

Har zai juya ya fita yaji tace “Malam ya fad’a mana mu dinga girmama iyayenmu muna musu biyayya, sannan idan sun mutu mu musu addu’a, amma Mamie nima zan iya yiwa Abhi na?”

Juyowa yayi ya kalli Mama ya fad’a mata abinda tace, d’aga mata kai tayi alamar eh saboda jikinta da yayi sanyi sosai, juyawa ya sakeyi ya fice a gidan saboda kiran sallah magriba da aka fara.

Yau kam tare da Mama ta ci abincinta suna ta zancensu kamar yaro da babba, sai bayan isha’i dasu Zeid suka dawo mama ta fad’a musu abinda ya faru, ance dai za’a saka gonakin biyu kasuwa kamar yanda suka buk’ata, amma kawun nasu ba haka ya so ba.

Sannan ta k’ara jadadda musu maganar tafiya ko basa so saboda sun kwana biyu rabonsu da can, Salahadeen ma daya dawo har yanzu baije ba.

Suna cikin tattaunawar Sarah ta shigo ta kwanta ta d’ora kanta a saman cinyar mama data mik’e k’afafu, murmushi Mustafa yayi ya kalli Salahadeen yace “Amaryar yaya fa ta zama autar Mama.”

Da sauri ya kalleshi fuska kicin kicin yace “…

Alhamdulillah

Na cika alk’awari
13/04/2021 脿 04:12 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button