NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Duk kallonshi sukayi inda Salahadeen ya had’e fuska sosai, dawowa yayi da baya ya kama hannun Sarah dake kallon mai aikin tace “Kina da lafiya kuwa? Uncle d..”

Bata kai k’arshe ba saboda hannunta daya kama yana kallon mai aikin yace “Baki fad’a masa ina tare da ita bane?”

Da sauri tace “Na fad’a masa amma yace sai ya shigo.”

Wani dogon tsaki yaja ya wuce yana fad’in “Wannan ai rashin sanin kimar mutane ne da darajar aure da kutse a cikin rayuwar ma’aurata.”

Jin zata tsayar dashi saboda yanda take taka k’afar yasa shi juyowa ya saki hannunta yayi wuf ya d’auketa kai tsaye ya shige d’akinta. Wani bahagon mamaki ne ya nemi kashe Kabeer daga nan tsaye, to wai me yaron nan ya d’aukeshi ne? Kakanshi ko me? Har rainin dake tsakaninsu ya kai haka? Rik’e k’ugu yayi yana sauke ajiyar zuciya, jinjina kai yayi ya juya a fusace ya fita.

Suna shiga d’akin ya zaunar da ita kan gado ya juya zai fita tace “Wai me yasa kake mishi haka? Babban mutum ne fa karka ga yana zuwa wurina sakaka haka ka nemi ka raina shi, babban mutum ne shima kamar dai mahaifina.”

Tab’e baki yayi can k’asan mak’oshi yace “Ki nisance shi kawai shine kwanciyar hankalin kowa.”

A hassale tace “Na k’i d’in, a matsayinka nawa zaka bani wannan umarnin?”

Juyowa yayi da kyau yana kallonta, gefen leb’enshi ya shiga taunawa a hankali yana aunawa da fassarawa yana kuma taushewa, k’aramar ajiyar zuciya kawai ya sauke ya sake juyawa zai fita, mik’ewa tayi tsaye tana fad’in “Ba zaka hanani mu’amula dashi ba saboda shi kad’ai ne ya rage min wanda yake so na, ina ganinshi kamar Abhina ne.”

Juyowa ya sake yana wani murmushi mai kama da kuka yace “So dai? So fa kika ce?”

Cikin d’aga murya tace “Eh so, kai ai baka san miye son ba bare ka fahimci yanda ma’abota son suke ji, ba zaka tab’a so ba kai kam sai dai mugu…”

Tsawa ya daka mata ta hanyar fad’in “Ke?”

Takowa yayi da sauri hakan yasa ta komawa ta zauna tana kallonshi a tsorace, saida ya tsaya kanta sosai yace “Ke kinsan miye so kuwa? Kinsan me masoyi ki iya aikatawa akan wanda yake so? Wannan banzan son da yake nuna miki ne har kike ganin so ne na gaskiya?”

Gyara tsayuwa yayi yana nunata da hannu yace “Wai ke mahaukaciyar ina ci? Me yasa baki tab’a tambayar kanki yanda akayi wannan Jhon d’in yasan inda kike har ya sameki a airport ba a Niamey? Ko sau d’aya kin tambayi kanki ya akayi ya zille miki sanda jirginku ya sauka baki sake ganinshi ba bayan yace ya zo rakaki ne har gida? Ko kuma kina so kice tunaninki bai tab’a kaiki ga tambayar kanki yanda akayi kika had’u dashi a k’asar Mekka ba a bazata?”

Girgiza kai yayi cike da jin haushi yace “Shin da kike cewa yana sonki kinsan wane irin so yake miki? Baki ji ana cewa abokin b’arawo b’arawo ne ba? Ba kiyi tunanin yanda akayi yasan kina da ciki ba kuma nawa alhalin bake kika fad’a masa ba? Ko kina so kice baki mamakin abinda ya faru dake ba sanda kika ja kuka had’u dashi a mall d’in nan? Wa ya dawo dake gida sannan taya kika shiga masaukinki? Ki zauna kiyi tunani akan rayuwarki Saratu, karki d’auka haka kawai nake son shige miki ko dan daularki ne, had’ari na hango ga da ga a tare dale shiyasa nake son zama kusa dake, ruwanki ne ki taimaka min ta hanyar bin umarni na dan ki sauk’ak’a min, maysalarki ce kuma kiyi taurinki ni kuma na nuna miki bana son wasa da raini.”

Ficewa yayi ya barta tayi shiru ta bishi da kallo, sannu sannu ta shiga sauke numfashi tana jujjuya kalamanshi a kanta, sala sala ta shiga binsu daki daki, kaf a iya nazarinta da tunaninta bata ga abinda ba daidai ba, hak’ik’a gaskiya ya fad’a mata kuma tayi sakarci sosai data zama marar maida hankali akan al’amura musamman wanda suka shafeta, me yasa bata tab’a tunani kan abinda ke rayuwa da ita ba? A kullum sai dai tayi kuka da bak’in cikin kasheta da Abhi ya so yi? Sai dai ta zubar da hawayen rashin iyayenta da kuma abinda ya faru a lokacin har ya saka ta kuka, amma zaunawa tayi tunanin ya akayi? Me yasa Abhi ya so kasheta? Hakan zai iya faruwa ba tare da sanin uncle Kabeer ba? Sai bata tab’a yi ba ko sau d’aya! Wani tsaki taja saboda jin haushin kanta da tayi, fad’awa tayi kwance tana kallon sama, a hankali ta saki murmushi na jin dad’in wasu kalamanshi data tuna cewa “Karki d’auka haka kawai nake son shige miki ko dan daularki ne, had’ari na hango ga da ga a tare dake shiyasa nake son zama kusa dake…” Dariya tayi wacce ta bayyanar da kyawunta tana lumshe ido da rumgume hannayenta a k’irji.

Yana fita saida ya d’auki kwalin data bashi ya wuce d’akin ya samu Farha da wayarta a hannu, jefa mata kwalin yayi kan gado yana fad’in “Princess tace a baki ki sakata anjima zamu je dinner.”

Cire rigarshi ya shiga yi yana fad’in “Akwai wata mai aiki data sa aka d’auko saboda ke, zaki iya fad’a mata abinda kike sha’awar ci, sannan idan kina buk’atar wani abu ma zaki iya fad’a mata, misamman dan ke take zaune.”

Tunda ya fara maganar take kallonshi har ya kai k’arshe sannan tace “Saboda ni kawai?”

Sauda ya nufi k’ofar ban d’akin yace “Na fad’a miki ai sun iya karamma bak’o.”

Shigewa yayi ita kuma ta fito da kayan da ke cikin kwalin, zaro ido tayi ta bud’e baki tace “Wow!” Sauka tayi daga kan gadon ta shiga warware rigar tana kallonta, kalar ruwan gold ce mai walk’iya da d’aukar ido, kamar an mammana madubi a jikinta doguwa ce sosai, ajeta tayi ta d’auki takalmin bak’ak’e dogayen sosai, sai wasu k’ananan kwali guda biyu, d’auka tayi duka ta bud’e sai sark’a ta bayyana, wani tsaki taja mai k’ara sosai tace “Aikin banza, wannan har wata sark’a ce, nima ai ina da kalar da zata dace da rigar, ba zan saka wannan ba da wani shegen dutsi ne aka mak’ala kawai sai bak’i sai d’an kunnai. D’aya kwalin kuma agogo wacce da gani kasan zata saki hannunta idan ta saka, sai dai bata fata bace bare kuma ayi maganar roba, bata wani d’auki hankalinta ba dan haka kawai ta ajesu gefe tana sake kallon rigar dan ita ce ta birgeta.

Salahadeen na fitowa da sauri saboda yana son tafiya masallaci kar ya makara, cikin goge jiki ya kalli kayan lokaci d’aya kuma ya kalleta yace “Sai naji kamar kina tsaki kina fad’a, me ya faru?”

Cikin sanyi tace “Ba komai yaya, sark’an ce naga bata da girma kuma bata da kwalliya sosai, shine nace zan saka tawa dake gareni zata fi kyau da rigar.”

Wani murmushi yayi ya juya wajen kayanshi wanda Farha ta jera masa kamar nata ya bud’a ya d’auki wanda yake buk’ata, k’ala bai ce mata ba saida ya gama shirinshi tsaf duk tana binshi da kallo, saida ya d’auki agogo zai d’aura ya matso kusanta, mik’a mata yayi alamar ta d’aura masa, karb’a tayi ta shiga lak’a masa idonshi kuma na kan kayan dake saman gado, saida ta gama ya kalleta sosai yace “Farha ba wai a garinki ba, a garin nan idan kika saka sark’an nan zaki iya had’uwa da b’ata gari, idan kuma kika had’a da agogon nan to shakka babu za’a iya saceki dan an ga yar babban gida.”

Juyawa yayi da niyyar fita tayi saurin cewa “Kamar ya sacewa kuma? Me yasa za’a sace ni?”

Saida ya isa bakin k’ofar ya juyo ya kalleta yace “Ita sark’a da yan kunnan diamond ne, agogon kuma ba wai zinariya ko azurfa bace, tsagwaron narkakken gold ne, rigar kuma ta fito ne daga kampanin Bill James, k’wararren mai zanen da duk wasu super star da c茅l茅brities suke ji da kansu da kayan kampaninshi suke tutiya.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button