NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Dariya Mama tayi cikin ladabi tace “Hajia to duka nawa yar amanar take? Ita ma mai reno take buk’ata.”

Girgiza kai Hajia tayi ko ba komai taji dad’in yanda take k’aunar jikar ta ta, Zeid ta kira tasa shi ya nemo mata gasashen naman, sanda ya kawo mata suka gaisa take tambayarshi ina Tafa?Dariya suka dinga mata ita dai ko a jikinta sai ma namanta da take ci.

Saida ta idar har sukayi sallah la’asar Mama ta kama hannunta tace ta zo ta gani, fita sukayi suka zagaya ta bayan gidan ta shiga da ita ta wata k’ofa, suna shiga k’ofar nan ma wani falon ne mai zaman kanshi, d’aki ta nuna mata tace ta shiga, kallon Mama tayi ta mak’ale kafad’a tace “Um um Mama tsoro nake ji.”

“Tsoron me?” Ta fad’a tana tsareta da ido, a hankali tace “Bana so na had’u da Slahadeen Mamie, dukana zaiyi saboda yana hushi dani.”

Zaro ido tayi tace “Duka kuma yar amana? Tunda kuke ya tab’a dukanki ne?”

Shiru tayi dan ita dai sau d’aya ya tab’a zabga mata mari, bayan shi bai sake dukanta ba gaskiya, shafa kumatunta tayi tace “Karki damu kinji babu abinda zai faru, Sarah miji girma ne dashi, munyi waya dashi yace bai san ma zaku zo garin nan ba, shiyasa nake so kije ki gaisheshi saiki bashi hak’uri.”

Kallon Mama tayi kamar bata gamsu ba hakan yasa Mama cewa “Sarah ba dan yana d’ana ba nace kiyi haka, saboda ina son ganin kin dawwama cikin farin ciki ne, duk abinda zakiyi yanzu ba fad’uwa kikayi ba, zai k’ara miki girma da martaba ne a wajenshi, kinji ko?”

Jinjina kai tayi tace “Zan je Mamie, ki tayani addu’a Allah yasa kar ya min fad’a.”

Dariya kawai tayi tana jinjina mata kai, tana kallo ta nufi d’akin ta k’wank’wasa tare da yin sallama, fita Mama tayi inda ta samu Hajia ta shiga da ita d’akin da har yanzu Salahadeen ya kasa ce musu ga ma mallakinshi, saidai yasa Mamuh ko Iffa su shiga su share su goge a canza shinfid’a, amma da an tambayeshi sai yace kawai dai yayi shi ne, nuna mata tayi a matsayin d’akin Saratu, Hajia tayi ta murna dan gaskiya d’akin da kayanshi sun had’u sosai. Aba ma da suka gaisa ya bayar da kud’i masu yawa yace ayi wa amarya siyayya, Mama da kanta taje ta mishi godiya sannan ya tafi yace zai dawo y d’aukesu.

Ta d’an jima a tsaye ba’a amsa mata ba sai kawai ji tayi an bud’e k’ofar, da alama daga wanka ya fito dan towel ne a jikinshi, gaban madubi ya k’arasa yana shafa mai, jin bata shigo ba yasa shi fad’in “Idan ba zaki shigo ba zaki iya komawa, amma ina son ganin d’akina a rufe.”

A hankali ta k’arasa shiga ta mayar da k’ofar ta rufe…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:22 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 5锔忊儯8锔忊儯

Har ya gama abinda yake bai kalleta ba a zahiri sai dai yana hangenta ta madubi, ta mishi kyau sosai kuma k’ibarta ta birgeshi, saida ya gama abinda yake ya nufi k’ofar d’akin, ta d’auka kanta zaiyi hakan yasa ta ja baya ta manne a jikin bangon tana kallonshi a tsorace, harara ya b’alla mata yasa key ya rufe k’ofar, kusanta ya tsaya ya rufeta da gaba d’aya jikinshi ya d’aga hannu, kawar da kai tayi tana rintse ido sosai tana jiran jin saukar mari, girgiza kai kawai yayi yasa hannu ya kashe wutar d’akin, sauko da hannunshi yayi ya jawo k’ugunta ya had’a da nashi ya matse, bud’a ido tayi sai kuma ta kalleshi kamar zatayi kuka, turo baki tayi tace “Mamie na jirana a waj…”

Bai bari ta k’arasa ba yasa yatsa ya rufe mata baki, saida ya d’ora bakinshi a nata ya sumbata kafin yace “Zan fara horaki ne na duka laifukanki, daga bisani kuma saiki karb’i tuhumarki yanda ya dace.”

Yuwanta ya shiga sumbata yana jawota har suka kai kan gadon ya kwantar da ita ya mata rumfa, kallon fuskarta yayi yace “Kin shirya? Kina da juriya? Kina da k’warin da zaki iya karb’ar hukuncinki?”

Girgiza mishi kai tayi tana sako da hawayenta cikin muryar kuka tace “Dan Allah mr. karka min komai kayi hak’uri, zan baka hak’uri kaji.”

Lak’ace mata hanci yayi yana fad’in “Oho! Kinsan baki da jarumtar kuma kika fara sa k’afar wando d’aya dani, zan matseki yanzu naga wanda ya isa ya k’waceki.”

Hannu yasa kan mamanta ya ciroshi daga cikin rigar, baki yasa ya lasa sai kuma ya kalleta yana murmushi yace “Kina kula masa dashi sosai.”

Ido tsaye ta kalleshi tace “Wanene?”

Saida ya kai bakinshi yana tsutsa yace “Baby Waleed mana.”

Girgiza kai tayi tana kawar da kanta tace “Ni fa ba zan shayar dashi da kaina ba.”

Ido kawai ya d’ago ya kalleta amma bai cire bakinshi ba bare yace wani abu, sarrafata ya shiga yi amma ta kasa hana shi sai nok’ewa da take yi kawai tana cewa bata so. Ita kanta sai yau ta tabbatar da tana da lafiya, dan tunda ya fara tab’ata ta fara amai a k’asanta tana so ta taimaka mishi amma kuma girman kai ya hanata, shi kam duk ya aje komai a gefe huce haushinshi yake hankali kwance, farin ciki marar misaltuwa ne ya mamaye zuciyarshi, yaji dad’in da bai tab’a ji ba ko da a waccen daren nasu ma, k’ibar da tayi ta k’ara ma kasantuwarsu armashi, haka ya dinga k’amk’ameta yana sumbatarta sai kiran sallah magrib ne ya dawo dasu nutsuwarsu daga baccin da yake barazanar d’aukarsu.

Da sauri ta zabura zata tashi ya rik’eta yana fad’in “Ina zaki je? Kinsan da yau babu mai rabani dake?”

Cike da sangarta tace “Um um! Ni wallahi gida zamu tafi, kuma saina fad’awa Mamie abinda ka min.”

Wani murmushi yayi yana tashi zaune yace “Na yarda ki fad’a mata, a ganinki bata san yanda akayi ciki ya shiga jikinki bane?”

K’ok’arin k’watar hannunta tayi tana fad’in “Sake ni nayi wanka nay sallah.”

Girgiza mata kai yayi alamar a’a tare da fad’in “Ki bari a gama sallaha sai kiyi, babu kyau bayyanar da tsiraici da magrib, ki jira kad’an.”

Ya fad’a yana jawota jikinshi, rik’e hannunta yayi yana kallon jan lallen akaifunta yace “Saratu amma ba zaki koma ba ko?”

Ba tare data kalleshi ba tace “Wai baka jin kunyar kiran sunana ne? Idan Abhi ya jika fa zaku b’ata dan sunar Hajiarshi ne.”

Cikin danne dariyarshi yace “To ni kuma Hajiar ba matata bace? Wa yace saina saya sunanta dole.”

Tureshi tayi tana fad’in “Amma ai sai ka min kara ko.” Bushewa yayi da dariya saboda yanda ta juya baki ita a dole tayi hushi, sake jawota yayi yana dariya yace “Shikenan to na daina, idan na ce Ummu Waleed yayi? Ko kuma princess?”

Turo baki tayi tasa hannunta ta shafo kumatunshi ta d’ora bakinta a kunnenshi ta rad’a mishi “Ina buk’atar kula da kaina fa, ba zan iya k’ara jiran minti d’aya ba.”

Rumgumeta yayi shima a cikin kunne ya rad’a mata “Zaki iya shiga yanzu mrs Slahadeen.”

Tintsirewa tayi da dariya ta sake shi ta mik’e, binta yayi da kallo yanda towel d’in ya tsaya iya cinyarta kawai, da zata sunkuya mazaunanta zasu iya fitowa waje, dama ya bata ta gasa jikinta da k’asanta da taji kamar yaune na farko kafin tayi wanka ta fito, shima shiga yayi da gaggawa hakan yasa ta mayar da kayanta ta kabbara sallah, shima a gaggauce ya shirya ya tafi masallaci bayan ya rufe k’ofar ta baya ba tare daya samu sallah ko d’aya ba. Ko da ya dawo ya sameta tana gyara kanta, kallonshi tayi ta mik’e tace “Mr. ina so na tafi, su Hajia zasu jirani fa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button