NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Mama da bata fahimceta ba saita karb’i robar ta kifa kai tasha saita koma ta mik’a mata tana fad’in “Kinga ko babu abinda na saka miki.”

Kallon robar ta sake yi tana kallon abin cikinta, duk da hasken asuba ne amma bata gane ko miye a ciki ba, cikin tsoro da fargaba ta d’an tsoma bakinta a robar, ta had’a na d’aya dana biyu har zuwa na uku, ta kurb’i na hud’u bata kai shi ciki ba kuma ya wuce mak’orgwaronta kawai wanda tasha ma ya dawo, bata samu damar d’auke robar daga bakinta ba aman ya taho mata, hakan yasa ta sakin robar kunun ya watse har ya fallatsar musu.

Sunkuyawa tayi tana aman yana fita babu kakari kamar ba daga gareta yake fita ba, kallonshi mama tayi tace “Salahadeen ko bata shan irin wannan?”

A dame yace “Mama abinda nayi k’ok’arin fahimtar dake kenan, idan ma tasan hatsi to anfaninshi a gurinta shine barasa.”

Da sauri tace “Barasa? Giya fa kenan? Tana shan giya dama?”

To shima dai bai tabbatar ba, dan haka yace “Ban sani ba mama, abinda tasan za’a iya yinshi da hatsi ne, ita ma barasar kafin wayewar kaine nake miki wannan maganar.”

Za tayi magana Sarah ta juya tana ma mama wani kallo tana nufa kanta kamar zata mareta tana fad’in “Are trying to kill me? U want to kill me?”

Kallon Salahadeen tayi ta nuna mishi mama tana fad’in “Wacece wannan matar? Me yasa take so ta kashe ni.”

Zai mata magana kuma Farhana ta fito daga d’akin wacce wannan hayaniyar ce tasa ta sallame sallarta, k’arasawa tayi tana kallon Sarah da ko kula da ita batayi ba, Salahadeen ta kalla da mamaki tace “Yah Salah, yaushe ka dawo?”

Kallonta yayi da annuri yace “Ban jima ba, ya kike?”

Bata iya bashi amsa ba sai kallon Sarah da take tana tunanin wannan fa? Dan kaf a zuri’arsu babu mai kama da ita ma, kallonshi tayi tace “Yah Salah wannan fa? Wacece ita?”

Kallon mama yayi ya kalli Sarah da har yanzu bata kalli Farah ba sannan ya kalleta yace “…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 03:58 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa ta Orange money(ba chap chap ba yan uwa, orange money dan karka tura ta chap chap amma zaku iya tura kati) akan wannan lambar 91-71-28-22 ko kuma wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               8锔忊儯

“Yar mai gida na ce, tare muka zo?”

Sake kallonta tayi tace “Tare kuka zo? Me yasa to?”

Sarah ce ta nuna shi da yatsa tana k’yasta mishi su tana fad’in “Hey mr., ina Abhi na yake? Wai yaushe zaka kaini na ganshi ba?”

Kallon Farha yayi yace “Dan Allah Farha taimake ni ki kai mata ruwan wanka, hayaniyar yarinyar nan ta fara hawar min kai.”

A yanda suka taso bai isa ya sata ta k’i yi ba dan haka ta wuce tana kallon Sarah, ita dai duk bata yarda da abinda ya fad’a ba, ruwa ta cika bokiti dashi dasu ta kai mata ban d’aki, kallonta yayi yace “Kije kiyi wankan sai ki fito na kaiki wajen Abhin.”

A harshen daya mata magana ita ma tace “Muje ka rakani da kanka, har yanzu ban yarda da kowa ba a gidan nan, na lura so kuke ku kashe ni.”

Wucewa yayi gaba tana binshi baya har suka isa bakin k’ofar ya tsaya ya mata iso, ko da ta zura k’afa d’aya ta juyo ta kalleshi tace “Ina ne nan?”

Kallonta yayi ya had’e yawu da k’yar yace “Idan ba kya son zuwa wajen Abhin to ki fito.”

Saida ta turo baki tace “To zanyi, amma dai nan ba toilet bane.”

Ya juya zai koma tace “Mr. tsaya, karka matsa ko ina har saina idar, na sani ko bom kuka saka da zata tashi dani, hey mr. kar kayi wasa dani.”

Kafin yayi wani yunk’urin ta cire yar yaloluwar rigar dake jikinta, hakan kuma yasa k’irjin nan nata da ba wani girma ne dashi ba ya fito fili, da wani irin juyin bala’i ya juya ya bata baya yana salati.

Bata ma kula da tsiyarshi ba sai dubawa data shiga yi taga ina bahon wanka? Ina shower bare ayi maganar ruwan d’umi? Ina…ina d’in ma tayi yawa, bokitin gabanta ta kalla tare da cire dogon wandonta da kuma pant, bata yi wata wata ba ta tsunduma k’afa cikin ruwan ta kuma saka d’ayar, duk’awa tayi da nufin yin zaune sai dai ina kafin ta zauna bokitin ya wurgata ta baya ta baje, kanta ne ya rigata tab’a k’asa kafin ruwan ciki suka k’arasa zubewa kan jikinta suka malale, k’arar da tayi da kuma k’arar da yaji kamar an fad’i yasa shi juyawa ya shiga ban d’akin ya manta ma da wacece a ciki ko kuma ya zai same ta?

Da sauri ya kamo siririn hannunta ya d’agata cak kamar yar tsana ya ajiye ta gefen bokitin, saida ya tayar da bokitin zaune ya d’ago da niyyar mata magana, wani irin fad’uwa gabansa yayi hakan yasa shi fita bai shirya ba ba tare da yasan ina ya jefa k’afafunsa ba, mama ce tayi saurin cewa “Me ya sameta take k’ara?”

Kallonta yayi jikinshi duk a mace yace “Fad’uwa ne tayi.”

Da sauri ta nufi ban d’akin dan ganinta, d’akin mama ya shiga ya zauna kan doguwar kujerar dake akwai zaman mutum uku, cire takalminshi yayi k’afa ciki ya mik’e k’afafu kamar zaiyi bacci. Hoton tsiraicinta ne yasa shi bud’a ido da sauri yana fad’in “Hasbunallah wani’imal wakil.”

Wani iska ya furzar ya sake rufe ido, kamar daga sama yaji muryar Farha na fad’in “Salah wai me take yi anan? Me ya had’aka da ita to da har ka zo mana da ita?”

A hankali ya bud’a idonshi ya saukesu kan rufin d’akin, juyawa yayi ya kalleta kafin ya tashi zaune yace “Farha manta da batun yarinyar nan, bacci nake ji yanzun, zaki iya taimaka min?”

Jinjina kai tayi tace “Shikenan, bari na gyara maka d’aki saika kwanta ko?”

Jinjina kai shima yayi alamar to, fita tayi ta wuce d’akin da aka ware musu ya zama na su, mama ce ta shigo tare da Sarah ta rufeta ruf da babban mayafinta dake jikinta sai rawar d’ari take, suna shigowa d’akin ya k’ura musu ido yana kallo har ta zaunar da ita kan katifar k’asa.

Rawa kawai jikinta keyi gab gab gab kamar zata cira, cikin tashin hankali mama ta kalleshi tace “Salah yarinyar nan fa zazzab’i ne jikinta mai mugun zafi.”

Gwiwar hannunshi ya d’ora kan cinyoyinshi ya had’e tafukan hannayenshi yana kallonta, ya fahimta dai matsala zata bashi ma, iska ya furza da nufin magana sai ji sukayi Sarah ta daddage tayi atshawa da iya k’arfinta, a hankali ya furta “Mura.”

Da sauri ya mik’e ya tsaya kusansu yana kallonta yace “Me kike sha idan kina mura?”

Cikin wata irin muryar wahala tace “Ha..ha.atshim.”

Da sauri tasa gyalen mama ta goge majinar data fara mata zubar ruwa, kafin kace me tuni ta jeme ta fita a hayyacinta, mura da zazzab’i ga farar fatar da bata saba wahala ba, tuni hancinta yayi jawur tsabar goge majina, idonta ruwa kawai suke fitarwa na kuka da kuma wahala, idon dake d’auke da launin k’asa k’asa sun bayar da kalar ja da yalo, gashin kanta duk ya hargitse sai gyarashi take amma yana rufe mata fuska.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button