NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Farha na hangeta ta k’arasa da sauri suka rumgume juna, cikin farin cikin ganin juna Farha tace “Sarah babu abinda ya same ki? Hankalinmu ya tashi sosai wallahi.”

D’agowa tayi daga jikinta tana kallon fuskarta tace “Karki damu kinji, ina lafiya ba komai daya same ni.”

Jinjin kai tayi tace “Alhamdulillah, Allah ya k’ara kiyayewa.”

Da kai ta mata alama da “Ameen.” Kafin suka bi bayan Salahadeen daya shiga ciki, saida aka basu izini bayan sun gabatar da passeport d’insu kafin suka samu izini, da rakiyar Richard har suka isa inda aka iyakance masu rakiya da su tsaya, rumgume juna sukayi shi da Richard kafin ya d’ago ya kalleshi yace “Ku saki Daniel ya tafi yanzu bai da wani anfani, zan Richard sai dai bansan ranar dawowa ba, dan wacce nake tunanin zata sake dawo dani garin nan naji tace ita da nan har abada, kaga kuwa nima babu ranar dawowa.”

Dukanshi yayi a damtse yana fad’in “Baka da mutumci fa guy nan, dubi yanda ka tayar mana da hankali akan yarinyar nan, amma dubi yanzu sai wani cin magani kake.”

Sake had’e fuska yayi ya d’an saci kallonsu har suna daf da shiga jirgi yace “Baka ga duk taron yara bane, so kake su raina ni ne idan na sakar musu fuska.”

Nuna.shi yayi da yatsa yana fad’in “Amma dai kai ka ci uban raina ni, to kayita had’e fuskar mana a k’arshe saika kora da ruwa ka shanyeta.”

Dafa kafad’arshi yayi yace “Ni zan tafi bros, watak’ila idan aurenka ya tashi na zo muja shisha.”

Da sauri ya rik’o rigarshi yana fad’in “Ka ce fa watak’ila? Ai dole ma ka zo Salah, ai na tashi aure baka zo ba to fasawa zanyi.”

Ba alamar wasa yace “Saina saceka na kaika k’asarmu na had’aka da bahaushiya.”

Dariya yayi yace “Yi hak’uri dan Allah, dan nasan tsaf zakayi dan nan kafi k’warewa, sace mutum a wurinka ba komai bane kamar sace sweet ne.”

Murmushi kawai ya masa yana shirin ficewa ya sake rik’e hannunshi, tsayawa yayi yana kallonshi shi kuma yace “Baka fad’a min yaushe ka fara magic ba Salah?”

D’an zaro ido yayi cike da mamaki yace “Magic kuma? Kamar ya?”

Saida ya gyara tsayuwa yace “D’azu mana naga ko da ka fara prayer aka mana girgizar kasa d’akin nan ya bayyana sai kuma aka samu Sarah a ciki, abun ya bani mamaki sosai.”

Yar k’aramar ajiyar zuciya ya sauke yana dafa kafad’arshi yace “Richard ba magic bane, k’udirar Allah kenan, ubangijin da babu wani abu dake faruwa ba tare da yana da sani akan wannan abun ba, Kabeer da k’ungiyarshi ba abakin komai suke ba, basu da wani k’arfi sai wanda ubangiji ya ara musu na d’an lokaci, duk abinda ya faru da ikonsa ne ya faru kuma haka ya so ya faru, shiyasa ma kaga hakan ya faru, na rok’eshi ne a lokacin da yayi alk’awarin amsa mana, dama kuma ya fad’a mana mu rok’eshi kuma muyi imani.”

Jinjina kai Richard yayi yace “A gaskiya ubangijinku yana sonku tunda har yana iya amsa buk’atarku anan take, sai naji ina sha’awar zama d’aya daga cikin mabiyanshi da zuciya d’aya.”

Wani irin dad’i ne ya kama shi wanda har ya bayyanar da farin cikinshi a take, sake matsawa yayi kusanshi yace “Ya kake kwatanta soyayyar uwa da d’anta?”

A take yace mishi “Soyayya ce marar misaltuwa da fatun baki.”

Jinjina kai yayi yace “To ubangijina yana son bayinsa fiye da yanda uwa ke son d’anta.”

Gyara tsayuwa yayi shima yace “Richard zanyi farin ciki sosai idan ka karb’i addina na, hakan zai tabbatar min da banyi asarar zama daku ba, kuma tun farko dana mu’amulance ku yanda ya kamata kamar yanda addina na ya koyar, ina da yak’inin da izuwa yanzu ba kai kad’ai zanyi sanadiyar shigarshi addini na ba, amma a hakan ma ina godiya ga Allah.”

Murmushi Richard yayi yace “Karka b’ata min lokaci mana, kayi sauri ka kaini mana nima na samu rabona.”

Dariya yayi yana rik’e hannunshi yace “Zan baka kalmar shahada yanzu, idan na sauka zamuyi magana a waya na fad’a maka yanda zakayi a gaba.”

Kalmar shahada ya lak’aba mishi a baki kafin suka sake sallama ya tafi, yayi farin ciki sosai da musuluntar Richard a sanda baiyi tsammani ba, haka ya same su a jirgin a kujera suna kallon juna, kujerar dake d’aya b’aren ya zauna yana hangensu ta wutsiyar ido har suka tashi suna mai addu’ar Allah ya sauke su lafiya dan isarshi.


Ko da suka gama waya ta shiga d’akin babban yayansu da gudu tana fad’in “Yaya Salim yaya Salim, tashi tashi.”

Da sauri ya dirko daga kan gadon yana d’aukar rigarshi yana k’ok’arin zurawa yana fad’in “Ke haukan ne ya motsa ko? Ya zaki shigo min d’aki kai tsaye? Ban hana ki ba?”

Turo baki tayi tana bubbuga k’afafu tace “Yaya Salim tace gata nan tafe fa, kuma tace ma na dafa mata abu mai dad’i.”

“Wacece?” Ya fad’a sanda yake zuro wuyanshi ta cikin rigar, da sauri tace “Sarah mana.”

“Da gaske?” Ya sake fad’a yana gyara rigar, da murna tace “Allah kuwa, yanzu mukayi waya.”

Da sauri ya nufo k’ofar fitar yana fad’in “A’a to bari nayi sauri naje shago na kwaso mana kayan abinci saiki dafa mata.”

Da farin ciki ta rigashi fitowa tana fad’in “Yawwa yaya kuma ka had’o mana da naman talo talo.”

Hanyar fita kawai ya nufa yana fad’in “Shikenan naji.”

Da haka ya fita ta koma d’aki ta tashi k’anwarta Sabira daga bacci, da sauri suka shiga gyara gyaren gidan da sarrafa abinci har magrib tayi suka sha ruwa, zuwa lokacin sun gama komai sun shirya zuwan Sarah kawai suke.

Ana kiraye kirayen sallah ta kira Sajida da lambar Salahadeen shi dake da layin k’asar ta sanar da sun sauka, haba wa ai dukansu gidan suka runkuta suka tafi tarbenta a mota har uku.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:21 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 5锔忊儯5锔忊儯

Duk ido suka zuba suna hange su ga ta inda zata fito, duk da a hankali take tafiya hannunta cikin na Farha, tana hangen Sajida da sauran da duk ta gane su tun a hoto ta saki hannun Farha, da sauri ta k’arasa ita kuma Sajida da gudu ta nufeta, juna sukayi cike da bege da shauk’i da kuma tausayin kansu, suna cikin farin cikin nan muryar Aba ta dakesu yana fad’in “Sajida ki barni na ga ‘yata mana.”

Da sauri Sarah ta d’ago ta kalleshi, bata tsaya komai ba ta fad’a jikinshi tana rumgumeshi shima, duk da yaji abun banbarak’wai amma ganin ita a d’abi’arta haka ba komai bane saiya share kawai, d’an bubbuga bayanta yayi yana fad’in “Hajiata kin zo lafiya? Ya hanya?”

A hankali ta d’ago tana sauke idonta akan shi da suka mata taf da k’walla, shagwab’e fuska tayi ta kalli su Salim dake gefen Aba, murmushi ta sakar musu tare da zame jikinta daga na Aba ta tunkari Hamid, waro ido yayi daga inda yake tsaye, jin zuciyarshi zata iya bugawa da katob’arar da take shirin jawo mishi, da saurin tsiya cikin dubara ya cakumi Hamid ya rumgume yana rintse ido, duka kallonshi sukayi tare da fahimtar manufarshi akan abinda yayi, Sajida ce tace “Lallai mijin yer uwa kana kishinta dayawa.”

Duka Salim ya kai mata a baki yana fad’in “Sarkin iya-yi, waya tambayeki?”

D’agowa yayi daga jikinshi yana had’a wata yar banzar fuska kamar bashi ba, murmushi Hamid yayi yace “Sannu ko.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button