NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Cikin jin dad’i ta dinga fad’in “Nagode, nagode sosai.”

Mik’ewa tayi ta nuna mishi suka fita, da Joseph ta had’ashi suka wanke gawar tsaf kamar yanda ya dace, a bayan gidan suka aje shi da taimakon almajiran malam d’in na masallaci aka sallaci gawar sai Alhaji Kabeer, ana idarwa suka d’aukeshi zuwa makabartar musulmi aka binne shi.

Bayan sun dawo gida ta sake zama da malam d’in take fad’a masa “Malam yanzu na shiga addinin nan, ina son sanin ilimin dake cikinshi, amma gaskiya kafin nayi haka ina so na bar k’asar nan na koma k’asar da zalla abinda zan dinga koya kenan, ka fad’a min wani wuri da zan iya zuwa wanfa yafi nan aminci.”

Murmushi ya mata yace “Akwai kuwa, ki koma saoudia ko kuma kije madina, insha Allahu zakiyi karatu hankali kwance, zaki kasance cikin aminci fiye da tunaninki ma.”

Da murmushi tace “Nagode sosai.” Farar enveloppe d’in hannunta ta mik’a mishi tace “Ga wannan, kyauta ce daga gareni.”

Girgiza kai yayi yace “Abinda na miki dan Allah nayi ba dan ki biyani ba, ki min addu’a kawai.”

Cikin kafeshi da ido ita ma tace “Nima ba biyanka bane nayi malam, kyautata min da kayi ne naga ya dace na kyautata maka, na gama fahimtar musulmi ba komai sukeyi dan a biyasu ba, shiyasa nake son na dinga kyautata musu dan na samu lada mai yawa a wajen Allah.”

Hannu yasa ya karb’a yace “Kin gama d’aureni da sark’ar da ba zan iya kub’uta ba.”

Dariya tayi ta raka shi har farfajiyar gidan tana ci gaba da mishi godiya.

Ta gama bucket d’in jirgin da zai kaita saoudia, jirgin mahaifinta ne mai kyau da girma amma kuma mutanen da yake d’auka basa wuce goma. Tsaye take ta d’ora gwiwoyin hannunta akan desk d’in gilashin dake zagaye da kwalaben lemu iri iri sha da kofin tangaran tana kurb’ar wani tsadadden lemu a hankali tana kallon tv na labarai kan tattaunawarta ta filin jirgi, d’aya daga cikin ma’aikatan gidan ce ta shigo da ladabi tace “Mma kina da bak’i.”

Furzar da isa tayi na rashin jin dad’i kafin tace “Ki ce su shigo.”

Sunkuyawa tayi ta juya tana fad’in “Ok mma.”

D’aukar kofin tayi cikin tafiyar kasala da jan k’afafunta dake sanye da takalmi slipas ta zauna kan kujerar alfarmar, wando ne jikinta mai sulb’i wanda ya saketa sosai kamar ya mata yawa, sai riga mai dogayen hannu kanta da hula ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya dan bata jin dad’in zaman daidai saboda zafi zafin da har yanzu take jin na ta’asar da mr. yayi jiya, a hakan ma dan ta samu tasha maganin rage rad’ad’i, sannan bayan tafiyar mutane ta samu ta sake wanka da ruwan d’umi harta zauna a ciki ta jima a ciki, tana cikin zaman jiran shigowarsu suka shigo kam.

Tana ganinsu ta saki fuska dan babu wanda bata sani ba a ciki, ma’aikatan banki ne daban daban da mahaifinta duk ke ajiya, mik’ewa tayi suka gaisa a mutunce kafin suka zazzauna.

Wasu irin mahaukatan kud’i suka shiga mata lissafi wanda suke son ta saka hannu a juye mata a account d’inta ko kuma in tana so a bud’e mata wani asusun sai aci gaba da mata ajiya, inda barristershi kuma ya shiga zayyana mata gidaje filaye da masana’antu shaguna wajajen cin abinci abun har sun fita hankali, duk saida suka gama kora mata jawabi inda a cikinsu wasu matasan ma su suna ganin komai ya daidaita zasu zagayo su kawo tayin soyayyarsu, idan Allah yasa ka dace sai kaji kayi wuf kayi sama. Bud’ar bakin Sarah shine “Zan zo ofishin naku gobe da safe, zanyi transf猫re d’in kud’in zuwa asusun mabuk’ata.”

Duk yanda suka so fahimtarta bata basu dama ba sai ma sallama data musu, sai takardun kadarorin data karb’a a hannun lauyan tare da cewa zatayi nazari akansu sannan tana buk’atar original d’in, suna tafiya ta nemi babban s茅curit茅 d’in mahaifinta wanda take ganin babu abinda bai sani ba, bayan ya zo ta nuna mishi wurin ya zama, da k’yar ya d’an zauna yana kallon tace “Ina so ka duba duk takardun nan ka tabbatar min wanene a ciki Abhi ya siya ba tare daya cuci wanda sukayi hark’allar ba.”

Kallonta yayi sai kuma ya karb’a ya fara dubawa, cikin sanyi yake duba takardun har yayi nasarar fito da guda goma sha uku a ciki ya mik’a mata yace “Wannan daga cikinsu wasu ya karb’a ne da k’arfin ikonshi, wasu kuma barazana yayi aka bar mishi, sauran kuma siya yayi amma ba akan k’a’ida ba.”

Fax d’in dake kusa da ita ta d’auka ta d’ora a kunne ta danna wasu lambobi, ana d’auka daga can tace “Joseph ya same ni a falona.”

“Ok mma.” Shine abinda aka fad’a mata, bayan minti biyu ya shigo cikin jikin manyantaka, bashi takardun tayi tare da kallon s茅curit茅 d’in tace “Kuje yanzu duk ku mayar ma da kowa hakk’insa kuma ayi a rubuce, ina buk’atar ganin resalt d’in.”

Mik’ewa yayi yana fad’in “Mma akwai wanda ba anan garin bane.”

Ba tare data kalleshi ba tace “Kuyi wanda zaku iya yi yanzu, zuwa gobe da safe saiku ida sauran.”

Kallon Joseph yayi suka wuce a tare, d’aukar sauran takardun tayi ta shiga dasu ciki, tsohuwar wayarta ta samu a wani akwatin ajiyarta, fito da ita tayi ta shiga social media, taga al’ajabi da mamaki a ciki, musamman lambobin samari bila adadin da kuma k’awaye wanda ta tabbatar hakan ya samo asali ne daga rasuwar mahaifinta saboda kowa naso ya samu nashi rabon, haka dai ta kai tsawon dare tana duba sak’on kafin bacci ya d’auketa.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:16 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               3锔忊儯1锔忊儯

Cikin yanayi mai dad’in gaske marar gundira, yanayi ne da babu matsi a cikinshi ko takura, yanayin shinfid’ar da garin da kuma iskar dake dukan gangar jikinta, su kad’ai sun isa su bawa ruhi hutu, ga kuma mafarkin dake mata jagora zuwa ga sakin murmushi a fuskarta yayin da take baccinta, komai yana tafiya mata daidai har saida wani abu ya faru da sam bai mata dad’i ba a bacci.

Haka kawai taji duk yanayinta ya canza, jikinta yayi nauyin gaske kamar a zahiri, siraren hawaye masu zafi taji suna fita ta gefen idonta, a hankali ta bud’a ido ta sauke su saman rufin d’akin, hakan yasa ta k’ara tabbatarwa mafarki ne take, tashi tayi zaune tana mayar da gashinta baya, dafe goshi tayi a hankali ta furta “Why mr.? Why?”

Shiru tayi kamar mai tunani sai kuma ta d’aga hannayenta alamar addu’a saboda tunawa da maganganun mam, da k’yar ta iya tuno abinda ta koyar da ita ta shiga harhad’a kalmomin tana fad’in ” 亘爻賲賰… 丕賱賴賲 丕賲鬲賵… 賵 丕丨賷丕.”

Jinjina kai tayi tace “Eh hakane, ai dama Mamie tace zata koya min kad’an ce wacce zan fara yi a yanzu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button