NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Jinjina kai tayi tace “Allah ya kyauta, ina jiranki to sai kin zo.”

Da haka sukayi sallama ta fita, d’aki ta koma Sarah kuma ta fito daga wanka ta shiga ciki, cikin kayan daya siyo mata ta saka wata riga da siket, cornflakes d’in data gani da kuma madara ya tabbatar mata ita aka ajewa, zubawa tayi daidai shan ta ta ci ta k’oshi, tana idarwa ta d’auki wayarta ta fito farfajiyar gidan.

Daga d’akin ta fito da zanin shinfid’awa kan gado dana rufa zata wanke, ajewa tayi ta d’ebo ruwa duk ta aje har da sabulu, har gabanta ta zo ta tsaya kamar wacce ta haifeta tace “Malama tashi ki wanke min kayan can.”

Kallonta tayi da rashin fahimta hakan yasa ta nuna mata kayan da mata alama da hannayenta cikin jin haushi da k’aguwa, fahimtar abinda take nufi yasa Sarah kallon kayan ta nuna kanta, cikin d’aga murya tace “Ke mana, idan bake wa zaiyi wankin? Ke da zaki zauna ne muna miki bauta, sai dai a dafa a baki ki cinye bayan kinyi wanka.”

Cikin harshen french tace “Kiyi hak’uri, ban iya wanki ba.”

Cike da mugunta tace “Au! Haka kika ce? Bari ki gani.”

Kamar ‘yar data haifa sai kuwa ta daddage ta cakumi gashinta data d’aure taja ta, saida ta kaita wajen kayan ta zubar da ita kamar kayan wankin ita ma, cikin tsawa ta sake nuna mata kayan tana fad’in “Maza tashi malama ki wanke kayan nan.”

Da k’yar ta tashi tsaye tana kakkab’e jikinta tana kallon Farha, tabbas bata iya fad’a ba amma kuma ta yarda tafi k’arfin tsayawa tayi fad’a da Farha, alamu ya nuna za suyi daidai a shekaru, sai dai ba tsarar fad’anta bace ko kad’an, ba fa dan sauyin rayuwa ba da ko a mafarki ba zasu had’u ba, wayar dake hannunta ta saka aljihun wandonta na baya, kallon Farha tayi tace “Nuna min yanda zanyi to, ni ko pant ban tab’a wankewa ba bare wannan uban abun.”

Wata dariyar rainin hankali ta mata tace “Yau kuwa zakiyi yarinya, ba iya wankin nan ba ma har da girki, dan yau su Iffa hadda suke a makaranta sai k’arfe d’aya zasu dawo.”

Wani d’an juya ido tayi tare da furzo iska alamar zancen bai dameta ba, wani zane ta d’auka ta saka mata a roba ta d’auki k’waton sabulu ta nasa ta zuba mata omo a ciki, nuna mata tayi ta zauna tayi.

Zaune tayi kan kujerar data aje yar tsugono ta ware k’afafunta ta saka robar tsakiya, d’aukar sabulun tayi ta kamo zanin, ikon Allah sai taji duk sun kubce a hannunta, sabulun ya mata girman da hannunta ba zai iya rik’e shi ba, shi kanshi zanin babba ne ga yawa ba zata iya ba.

Sake k’ok’artawa tayi ta d’auki zata sake jarabawa, sallamar da Salahadeen yayi tasa ta sakin sabulun tana kallon mai shigowa, k’ura mata ido tayi tana kallo, ba wani dogo bane sosai amma zama a k’asar waje tasa har ya zama baturen dole shima, a tak’aice zaka kirashi da jan kunne shima, ga duguzar turawa da askin yan zamani daya shek’a a kanshi. Murmushi ta saki ba tare data d’auke kanta daga kallonshi ba, shi kuma murmushin da tayi ne yasa yaji ya tsargu tare da son sanin abinda yasa ta murmusawa bayan tana binsa da kallon k’waf.

Yana k’arasawa da mamakin kayan dake gabanta yace “Me kike wa dariya?”

Saida ta kalleshi da kyau tace “Dole matarka tayi kishinka, kyakyawa ne kai handsome guy.”

Basarwa yayi ya sake kallon kayan gabanta yace “Me za kiyi da wannan?”

Turo baki tayi gaba ta nuna d’akin Farha tana fad’in “Waccen jarababbiyar matar taka ce ta sani wanki, na fad’a mata ban tab’a yi ba amma bata yarda ba.”

K’urawa fuskarta ido yayi, yar caras da ita har yanzu bata da matsala ko d’aya, ko kuwa dai bata nunawa ne ko kuma dan bai zauna da ita ba bare ta fad’a, amma dai a jikinta bata nuna ba bare ka gani. D’auke kanshi yayi a hankali tare da cewa “Me yake damunta ita?”

Kyab’e baki tayi tare da d’aga kafad’a alamar bata sani ba, kallonta yayi yace “Kin ci abinci?”

Jinjina masa kai tayi alamar eh, wucewa yayi d’akin ya samu Farha zaune da waya tana dannawa, saida ya nufi inda ya aje kwalin jiya yace “Me yasa kika bata wanki Farha?”

Ba tare data d’ago ko ta damu ba cikin rashin kulawa da fito da zancen daga bakinta tace “Um saboda ya kamata ita ma ta fara aiki, ba wai ta zauna mu mu zama bayinta ba.”

Murmushin gefen labb’a yayi ya d’auko kwalin ya juyo ya kalleta yace “Kije ki wanke kayanki da kanki, ko zata shekara a wurin can ba zata wanke miki d’aya daga ciki ba.”

Saida ya tako ya zo gabanta yace “Ruwan wanka ma da take kaiwa kanta wallahi anan ne, Farha a inda Sarah ke rayuwa ke aljanna ce a wurinki, a b’angarenta kawai ba wai gaba d’aya gidan ba tana da ma’aikata masu mata hidima a k’alla guda takwas, karki rainata dan ko yanzu zata iya dawo da abinda kike ganin kamar ta rasa.”

Ficewa yayi bai jira me zata fad’a ba, ita kanta tab’e baki tayi tace “Ko ma yar sarki ce acan tunda ta baro masarautarta ta zo wata dole ta zama baiwa, matsayinta bai dame ni ba kai ya shafa.”

Ko da ya fito ya kalleta yace “Zo.”

Mik’ewa tayi da sauri ta bi bayanshi cike da jin dad’in ya fansheta a wankin, d’akin Mama ya shiga haka ita ma tabi bayanshi.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:04 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               1锔忊儯7锔忊儯

Yanda ta zauna daf dashi akan kujerar yasa shi dan muskutawa ya matsa, kwalin ya aje gabanta tare da bata wasik’ar, saida ta fara bud’awa tace “Na miye?”

Ba tare daya kalli fuskarta ba yace “Bud’a ki gani.”

Kwalin ta fara bud’ewa sai taga kud’in nan tari guda, kallonshi tayi a tsorace tace “Mr. ba dai sata kayi ba? Ina ka sa..”

Tsaf ta had’iye maganarta dan kallon daya mata ba k’aramin kayar mata da gaba yayi ba, bai ce komai ba ya sake d’auke kanshi, a hankali ta shiga warware takardar nan ta shiga karantawa. Tausayin mahaifinta taji ya kamata sosai, alamu sun nuna mata zata rasa shi shima, dan haka ta kalli Salahadeen tana zubo da hawaye tace “Mr. please ka kaini wajen Abhi, yana cikin matsala, bana so na rasa shi shima kamar yanda na rasa mahaifiyata, dan Allah ka kaini na yarda ya kashe ni indai zai rayu.”

Bai ko kalleta ba sai dai kowace kalmarta yana mata masauki na musamman ya shigar da ita k’walwarshi, gaba d’aya ta d’auki kwalin ta d’ora mishi kan cinya tana fad’in “Ka rik’e wannan duka na baka amma ka kaini wajen Abhi, please mr.”

A wani shek’e ya kalleta yace “Zan kaiki idan Mama ta dawo daga k’auye.”

Cikin share hawaye tace “K’auye kuma?”

Shiru ya mata sai k’ok’arin tashi da yayi, da sauri ita ma ta mik’e tsaye tana fad’in “Me Mamie zatayi a k’auye? Dama k’auye ta tafi ta barni ni kad’ai?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button