NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Da sauri Farha tace “Ni baiwarta ko? To ba zanyi ba.”

Kallon Sarah ya sakeyi yace “Tashi ni zan daka miki.”

Girgiza mishi kai tayi tace “Zanyi.”

Ci gaba tayi da dakawa a hankali tana lura da inda take d’ora tab’aryar, nufa d’akinsu yayi dan gabatar da abinda ya dawo dashi, haka ya fito ya sake fita ya barta nan tana dakan.

Ita dai yi kawai take bata san yane zata gane yayi ba, jin kururuwar dakan ya isheta ne yasa ta kallonta da alama da hannu cikin jin haushi tace “Ya isa ke, daina hakanan.”

Tsayawa tayi ko tana kallonta ita kuma ta bita da harara tana fad’in “Haba.”

Ire iren aikin nan tayi ta saka Sarah ita kuma tana yi da rawar jiki, har saida su Mamuh suka dawo suka same su, bayan sunyi sallah azahar suka zauna cin abinci, suna idawa Mamuh ta fara had’a kwanuka dan wankewa Farha tace “Mamuh ki bari yau Sarah tayi mana.”

Kallonta tayi tace “Amma ita ta tab’a yi ne da zaki fad’i haka? Kuma ma ai naga n…”

Iffa ce ta katseta da cewa “To zabiya uwar Sarah, wanke wanken ne ba zata iya ba shima? Sai wani neman kike ki tare mata.”

Farha ce ta d’ora “To naga dai yanzu ita ma d’iyar Mama ce, kamar yanda aka raba mana aiki miye a ciki dan ita ma tayi, in ta iya ai dad’inta ne ba namu ba.”

Jinjina kai tayi tace “Hakane, Allah yasa da manufa mai kyau kika fad’i haka, Allah kuma ya bata basirar hardace duk abinda kuke son koya mata da sauri.”

Kallon juna sukayi tare da dariya harda tapa hannu, Iffa ce ta kalli Sarah da ita dai bata gajiya da kallonsu in suna abu, da hannu da kuma fad’a mata a baki ta mata alama tana fad’in “Tashi kiyi wanke wanke, wanke wanke kinji.”

Da murmushinta a fuska kuwa mai kyau ta jinjina kai alamar to ta mik’e, kasancewar ta kai komai a wajenshi yasa zaune kawai tayi kamar yanda taga sunayi, sai Mamuh ta dinga taimakata ta samu ta ida wanke kwanukan dama ba yawa ne dasu ba.

Ana kiran sallah la’asar duk suka gabatar da sallahrsu tare da shirin tafiya makaranta, suna fitowa Sarah ta kalli Mamuh tace “Zan iya tafiya tare daku?”

Da murmushi tace mata “Me zai hana, ki tashi muje, amma dai ba da kayan nan ba.”

Kallon kayan tayi tace “To ki bani wasu na canza.”

Juyawa tayi ta koma ciki ta bi bayanta, riga da siket ta baya ta saka, duk yanda suke ganin kayan ranar sun mata kyau, sai yau taga sunfi karb’arta fiye da waccen, musamman data d’ora mata hijabi kalar na islamiyyarsu bla mai haske, dogo ne har k’asa ko siket d’in ba’a gani gashi kuma da hannu da hularshi kamar kallabi, da kanta ta d’aure mata zariyar dake bayan hijab d’in a mazaunin kallabi, fitowa sukayi ta saka takalminta masu d’amara bak’ak’e.

Farha na sauke idonta akanta haka kawai taji gabanta ya fad’i, wani irin haushi taji ta bata kawai ta bita da harara da tsaki, saida suka fita kuma sai taji kamar tayi kuka ko tayi iju. Haka kawai ta tuna da kalmarshi ta jiya wai amma dai kinsan ina da mata, sannan maganar Mustafa ta amaryar yaya, idonta taji sun cika da k’walla ta yanda ba zata jura ba kawai.

Da fitarsu anjima kafin Mama ta shigo gidan da sallama da tunanin samun yar amanarta kuma rigimammiyarta, fuskar Farha ba yabo ba fallasa ta tarbi Maman, k’ofar d’akin ta zauna kan kujera tare da zube kayan hannunta nan, kallon Farha tayi data mata tsaye a kai tace “Farha taimaka min da ruwa nasha, na kwaso rana fa.”

Juyawa tayi ta samu mazubi mai kyau ta kawo mata tasha, kallonta ta sake yi tace “Ina Sarah take?”

Kallon mama tayi da mamakin yanda ko su Iffa bata tambaya ba sai wata Sarah, cikin gimtse fuska tace “Sun tafi islamiyya.”

Murmushi Mama tayi tace “Ai nasan suna islamiyya shiyasa ban tambayesu ba, Sarah nake nufi.”

Ba annuri tace “Eh Mama tare da ita Mamuh ta tafi.”

Da farin ciki sosai Mama tace “Kai dan Allah? A’ah masha Allah, gaskiya naji dad’i sosai.”

Kallonta tayi tace “Salahadeen bai shigo ba?”

“Tunda ya fita da safe bai shigo ba har yanzu.” Ta fad’a tana kumburo baki, jakarta ta d’auka ta duba lambarshi ta kira, yana d’auka a tak’aice tace “Ka zo ina nemanka.”

Da “Sai ka zo.” Ta amsa mishi ta kashe wayar, kallon gidan tayi tace “Yarana kenan, lallai ko bana tare daku zaku iya kula da gidan nan.”

K’ala ba tace ba sai ma zaune da tayi kan kujera ita ma duk jikinta a mace.

Ba’a d’auki lokaci mai tsayi ba ya shigo da sallama da kuma fara’a, a tare suka amsa sai dai Farha can k’asan mak’oshi ta amsa, kuma ta amsa ne dan yana sabo ne gareta, kusan mama ya zauna akan tabarmar dake shinfid’e k’asa yana fad’in “Mama yanzu kuka dawo?”

“Yanzu na shigo ban jima sosai ba.”

“An zo lafiya, ya su kawu da Inna Mama?”

Tab’e baki tayi tace “Hum, ai in fad’a maka dole ne ku shirya a k’arshen satin nan kuje ku gane su, kaji caccakar da aka mana na rashin zuwanka kuma ka dawo.”

Murmushi yayi a gefen labb’a bai ce komai ba, Mama ce tace “Ina su Zeid ne?”

Kallonta yayi yace “Na kirasu ne?”

“A’a bari har su shigo da magriba, kaima na kiraka ne dan naji ya amanata take? Farhanatu kuma ta fad’a min tun safe daka fita baka shigo ba.”

Saida ya d’an kalli Farha da kanta ke k’asa kamar marar lafiya kafin ya kalli Mama yace “Duka lafiya lau.”

Kallonshi mama tayi tana murmushi, bud’a baki tayi tace “An ce ma tare da ita suka tafi maka…”

Bata kai k’arshe ba Sarah cikin takon nutsuwa kamar d’awisu cikin sanyayyar murya tana fad’in “Slamlaikum.”

Duk da ba daidai tayi sallamar ba, amma muryarta da kuma sauti da dad’in yanda ta rairai abun yasa Salahadeen tsayawa cak daga danna wayar da yake yi, har zuciyarshi ya so ya juya amma saboda tsaro kawai ya share, a sama sama ya tsinkayo muryar Mama na fad’in “…

Alhamdulillah

Sorry fo the late
13/04/2021 脿 04:09 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               2锔忊儯2锔忊儯

“Yan makaranta har an dawo?”

Ganin Mama yasa Sarah dakawa a guje ta k’arasa wajenta, durk’ushewa tayi tare da rumgume Mama da farin ciki tana fad’in “Mamie kin dawo?”

Mama ma rumgumeta tayi cikin farin ciki tana fad’in “Saratu ashe makaranta kika tafi?”

D’agowa tayi daga jikin Mama ta tallabo fuskarta da hannu biyu ta daidaici kumatun Mama ta danna mata sumbata, saida mama tayi wani wuk’il wuk’il da ido ta kalli Salahadeen, shahararre kenan yanda ya wani matse fuska yana satar kallonta ka rantse wata abokiyar gabanshi ce, amma kuma sumbar nan da tayi saida zuciyarshi ta dara yayin da yaji dariya taso kubce mishi. Rirrik’e hannayen Mama tayi tana kallon fuskarta tace “Nayi farin cikin ganinki Mamie, me yasa kika tafi kika barni?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button