NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Tinnnnn, k’arar da agogon falon tayi ce ta tabbatar k’arfe d’aya ce ta buga na dare, share hawayen tayi ta d’aura alwala ta murza key k’ofar ta bud’e, ido biyu sukayi saboda juyowar da yayi jin an bud’e k’ofar, da sauri ya mik’e yana tsareta da ido, hannu ya kai zai shafa fuskarta data kumbura ido suka k’ank’ance mata suka mata jajir, fuskar duk tayi ja da ita alamar kuka da ta ci, da sauri ta matsa gefe tana d’aga mishi hannu alamar karya tab’ata, ko kallonshi ba tayi ba ta wuce shi ta sake kallon gabas da nufin kabbara sallah dan taji sauk’in abinda ke ranta da zuciyarta. Kafin ta kabbara yasha gabanta cike da kulawa yace “Sarah lafiya? Me aka miki kike neman kashe kanki da kuka haka? Dubi yanda fus…”

Cikin sanyin murya sosai tace “Dan Allah babu ruwanka da matsalata, ina rok’onka ka fitar min a d’aki na ko kuma ni na bar maka d’akin, ka fita daga nan bana son ganinka, baka da had’i da matsalata kamar yanda babu abinda ya had’ani da kai.”

Saida ta d’auke idonta daga kallonshi kafin tace “Ka fice min a d’aki dan Allah.”

Matsowa ya sake yi kusanta dan ya rarrasheta ya ji miye matsalar, ja baya tayi tana fad’in “Nace ka fita ko, idan kuma ba zaka fita ba ni saina fita.”

Juyawa tayi zata fita kam yayi saurin tare gabanta, cikin fizgo numfashi da k’yar ya kalli fuskarta da yake jin kamar ya kaiwa bango naushi ya tambayi dalilin da yasa ta wahalar da kanta haka wajen kuka, waya tab’a ta? Me aka mata? Me yasa ta kuka haka? Me yasa zata nemi hukunta shi kan laifin da baisan anyi ba ko yayi? Girgiza kai yayi cikin jin haushi yace “Shikenan zan fita, amma dan Allah ki ce min ba zaki sake kukan nan ba.”

Kallonshi tayi kawai ta juya gabanta ta sake daidaita gabas ta kabbara sallah da “Allahu Akbar.” Jin haka yasa shi sauke nauyayyar ajiyar zuciya, k’eyarta ya kalla yana mamakin tashin hankalin daya shiga daga ganinta a wannan halin, me yake faruwa dashi a game da ita? Gaban goshinshi ya d’an shafa ya gyara tsayuwarsa yace “Dan Allah kada ki sake kukan nan, hakan na cutar dani ta b’angarori da dama, ki kiyaye haka ko dan lafiyarki data abinda ke cikinki.”

Region d’Agadez

Tana kashe wayar da sauri sosai ya rarumi makullin mota ya fito, da sassarfe ya sauka k’asan benen ya ratsa ta babban shagon kayan masarufin ya fita, gidan Hajia yaje tun k’ofar shiga yake k’wala kiran “Hajia, Hajiata, Hajia kina ina?”

Mai mata aiki ya ci karo da ita yace “Ke ina Hajia?”

Cikin mamakin yanda ya shigo a kid’ime ta nuna mishi tare da fad’in “Tana madafa.”

Da gudu gudu ya nufi madafar inda babbar rigarshi ke biye dashi a baya, ba sallama ya fad’a madafar yana fad’in “Hajia, Hajia albishirinki, kinsan me na gani yau?”

Tsohuwa ce mai k’iba sosai sai dai akwai alamar jin dad’i da hutu tare da ita, tsaye take tana kad’a miyar kuka da maburgi a hannunta, ko juyawa ba tayi ba bare ta kula shi, a tunaninta jiya sunyi fad’a shiryawa ne yake so suyi shiyasa ya zo mata da wannan rainin hankalin, tsayawa yayi gabanta yace “Hajia ina ta magana shiru.”

Ba tare data kalleshi ba tace “To me zan maka?”

Murmushi yayi yace “Allah ya huci ranki Hajiata, kinsan kuwa girman albishir d’in dana zo miki dashi?”

Tab’e baki tayi tace “Ba zai wuce kace ka samu matar aure bane.”

Da sauri yace “Bashi bane Hajia, wannan yafi waccen tsada da mahimmanci.”

Tab’e baki ta sake yi hakan yasa shi fito da wayarshi ya danna ya nuno mata hoton ya mik’a mata yana fad’in “Waye wannan Hajia?”

Karb’a tayi tana kallon hoton da kyau, da sauri ta kalleshi tace “Kamar autana ko? Shakoor ne wai?”

D’aga mata kai ya shiga yi yana dariya yana fad’in “Shine Hajia, Hajia yau nayi magana da ‘yarsa mai sunanki, Hajia ashe suna nan duniyar nan.”

Sakin maburgin tayi tana kallonshi da yanayin farin ciki mai d’auke da alhini tace “Dama Shakoor d’ina yana raye? Na d’auka wani abu ya same shi kwanan baya dana dinga mafarki akanshi ina yawan tunaninshi, ashe yana raye babu abinda ya same shi, dan Allah ka kira min shi naji muryarsa.”

Cikin son kwantar mata da hankali yace “Hajia kwantar da hankalinki, ai nayi magana da ‘yarta sa tace ma zata zo nan da kanta, kuma nasan tare zasu zo tunda ita bata san nan ba.”

Murmushi tayi tace “Da gaske tace zata zo? Ka ce takwarata ce? Sunana ya saka mata kenan?”

D’aga mata kai yayi yace “Eh Hajia, sunanki ya saka mata.”

Mik’a mishi wayar tayi tace “Kira min ita dan Allah, kira kace mata ni kakarta ce ni na haifi ubanta.”

Kiranta yayi ta WhatsApp (video call) amma baya samu saboda ta sauka ita, dan farin cikin Hajia haka ya zauna zaman dakon Sarah ta hau danya kirata, sunayi suna hira yana k’ara fad’a mata yanda akayi, har ya kira Sajida ma suka sake tattaunawa ita ma ta fad’a mishi abinda ta sani, a bakinta suka ji cewa tana da aure yanzun har da ciki ma, anan yayi sallah magriba da isha’i a gidan yana kallon
lambar Sarah dan ya had’ata da Hajia amma shiru.


Haka ta shirya da safe ta fito cikin suit d’inta farare kamar yanda ta saba, dogayen takalmi ne ta saka masu shegen tsini sosai, d’an beby hijab d’inta ta saka iya wuya kafin ta d’auko wayarta data Salahadeen daya bari nan ta fito, Kaka ta samu a falon suka gaisa, kallon k’afafunta tayi tace “Baby ya zakiyi tafiya da takalmin nan? Ciwon fa?”

Ba walwala tare da ita tace “Na warke granny, zaje shopping ne, akwai abubuwan da nake buk’ata.”

Da mamaki tace “Amma baby y…” Sumbatar kumatunta tayi kawai tace “Yanzu zan dawo granny.”

Da kallo ta bita har ta tsaya tana tambayar Linda data gani ko ta ga mai gidanta? Da girmamawa tace mata “Eh ai ya jima zaune waje, kamar yana cikin damuwa na..”

Kallon data mata irin tambayarki nayi? Yasa tayi shiru, wucewa kawai tayi ta fita, sanin zata fita yasa ta samu mota a k’ofar fitowar, wasu sabi mai bata kariya ne su biyu cikin bak’ak’en kaya sai driver, har sun bud’e mata k’ofar zata shiga sai kuma ta tsaya saboda ganin Salahadeen ya nufo su, tsayawa tayi har ya k’araso daidai da fitowar Farha ita ma cikin hijabinta, juyawa Sarah tayi ta kalleta sai taga ita ma idonta sunyi ja kamar ta kwana tana kuka, mayar da kallonta tayi kan Salahadeen ta mik’a mishi wayar tana fad’in “Wayarka daka manta.”

Karb’a yayi ba tare daya daina kallonta ba yana son tambayar ina zata je? Wannan shigar fa? Takalmin fa? Ciwon k’afarta fa? Shi d’an iska ne da zata fita a haka da kuma wannan takalmin salon taja mishi salalan tsiya ta zubar masa da d’an k’ok’arin nasa? Kai ba zai yiwu ba wallahi, amma kuma fuskarta a had’e take sosai yanda yaji ma shi ba zai iya tambayarta ba.

Ta kama murfin motar zata bud’e Farha taja tsaki cike da jin haushi, juyowa Sarah tayi da mamakin jin tsakin, dan yau bata jin zata iya k’yale matar nan dan a jimame take, kallon tuhumar data mata ne yasa Farha saukowa kan matakalar tana fad’in “Eh nayi tsaki sai me? Inba iskanci ba ai tunda ya fad’a min zai kwana d’akinki nasan me zai faru a d’akin, ba wai sai kin bashi waya a gabana saboda kina so ki ci zarafi na ba.”

Cikin sanyi sosai ta bita da wani kallo tace “Ke, idan kina haukanki ki daina saka ni a ciki, na d’auka zaki fahimta cikin sauk’i cewa ni d’in mai abunyi ce da bana da lokacin rigima, amma naga kin kasa fahimtar haka kamar yanda kika kasa fahimta yanzu a yanata kike.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button