NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Wani nauyayyen numfashi ya sauke ya juya zai koma d’akin yana fad’in “Na karb’i tayinka da hannu bibbiyu.”

Shigewa yayi ya barshi nan ya koma inda yake zaune kan kujerar nan, kallonta yayi sai wani had’e fuska take tana turo baki, mayar da kallonshi yayi ga wayar daya ciro yana fad’in “Yanzun zaki kashe ni ko sai anjima?”

Juyawa tayi ta kalleshi sai ta sake kumburo baki ta juyar da kanta, ba tare daya kalleta ya sake cewa “Ke nan k’asarku da kike cewa na koma k’asata?”

Shiru ita dai bata ce mishi komai ba, tasowa yayi da wayarshi a hannu ya zo kusanta, zaune yayi bakin gadon yana fuskantarta da kyau yace “Ke kika fad’a masa kina da ciki? Me yasa baki da sirri?”

Da sauri ta d’ago idonta ta sauke cikin nashi, da sauri ya kawar da nashi idon saboda kasa jurar kallon nata idon da suke saurin kayar masa da gaba, ita kanta saurin d’auke nata idon tayi ta sadda su k’asa tana rarraba ido, jin ba shi take kallo ba yanzun yasa shi sake kallonta yace “Ina jinki, me yasa kika fad’a masa?”

Bata yarfa ta sake d’aga idonta ba a hankali ta shiga wasa da yatsunta tace “Ni ban fad’a masa komai ba.”

A tsanake ya kalleta yace “Ke kalli nan.”

Da sauri ta samu kanta da d’aga ido ta kalleshi, kakkafeta yayi da ido yace “Ni zaki ma k’arya? Ni abokin wasanki ne?”

Tuni taji gabanta ya fara fad’uwa idonta na neman kawo ruwa, girgiza kai tayi da sauri tace “Wallahi ban fad’a masa ba, daga makaranta ko da aka fad’a min kai tsaye naje na same ka.”

K’urawa fuskarta ido yayi yana jin wani hamshak’in dad’i da wata sarauta na mamayeshi ganin duk abinda take tak’ama dashi tana shakkarshi (humm kaji dad’i kenan? Ba farau ba dai ramau).

Kafin wani yace wani abu aka sake shigowa d’akin, Joseph ne da Sandra suka shigo da farin ciki suka k’araso, jimamin ganin halin da take ciki sukayi tare da mata sannu, daga yanda yaji suna mata addu’a da ambaton Allah yasa yaji da alama musulmai ne, daga kuma yanda take basu bayanin su samar mata sabbi masu aiki tana son komawa gida yasa ya fahimci masu aikinta ne, haka suka tafi suna mata addu’ar samun sauk’i suka tafi.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:18 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 4锔忊儯0锔忊儯

Wata ma’aikaciyar jinya ce ta shigo ta dubata ta kuma tambayeta idan da wani abu da take so ko take ji, ta fad’a mata babu abinda take so sai fitsari da take ji, fita tayi bayan tace ta jirata, ba jimawa ta dawo tana turo kujera ta zaman guragu, kamata tayi suka shiga kiciniyar sauko da ita daga gadon, ta kamata tana d’an taka d’aya k’afar tana d’yangyasawa zata zauna kujerar, wata surar karan mahaukaciya taji ya mata kawai ya nufi ban d’akin da ita ba tare daya d’ora kan kujerar ba, da sauri malamar jinyar ta juya ta bisu da kallo, shigewa sukayi ban d’aki sai kawai ta tab’e baki ta tura keken ta fita dashi.

Tunda taji yayi sama da ita ta rintse ido amma ba tayi yunk’urin hana shi ko cewa ya sauketa ba, ya gagara fahimta ne tun ranar da suka fara had’uwa ta fara jin tsoronshi, yanda ya mari abokinta Amit a cikin mutane, da kuma washe garin ranar data ganshi da bindiga bayan yanzu ta tabbatar ba d’an sanda ko wani jami’in da aka yarje ma rik’e bindiga bane saboda kare kanshi, sai kawai take tsoronshi ta kuma sa shi a sahun yan ta’adda, duk da zata iya cewa ba mugu bane a cikin yan ta’addan, amma dai ta yarda in ranshi ya b’ace zai iya yin komai, sannan yakan iya yin hukunci ma idan yafi k’arfin abu, shiyasa har ranar daya rabata da budurcinta bata iya tara mishi jama’a ba, tunda tace ya daina yace mata ba zai iya ba, a ganinta a wannan lokacin zai iya murd’e wuyanta ya kashe a banza a wofi.Yanzu ma bata ce mishi komai ba har taji ya sauketa, bud’a ido tayi tana ta neman tsayawa akan k’afarta guda amma bata samu nasarar haka ba saida tayi saurin rik’e kwalar rigarshi sannan ta tsaya cak, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalleshi tace “Nagode.”

Sakin rigarshi tayi ta dafe d’an katakon dake jikin madubin dake ban d’akin, juyawa yayi ya fita ya tsaya bakin k’ofar, bata jima ba ta sake tasowa da cogal cogal ta fito, yana jin fitowarta bai bari ta gane yana nan tsaye ba ya sake yin sama da ita sai kan gadon ya direta, d’an katin nata dake lake da gadon ya duba kafin ya juya ya fita gaba d’aya. Wata nauyayyen ajiyar zuciya ta sauke ta girgiza kanta, gyara kwanciyarta tayi ta d’ora k’afarta inda aka rataya ta.

Wani likita ne ya shigo da fara’a yana tambayarta jiki, da fara’a ita ma ta amsa kafin ya fad’a mata yanda sukayi da Kabeer akan sallamarta, cike da tabbaci tace “Eh ni na buk’ata, bana jin komai yanzu zan so na koma gida.”

Jinjina kai yayi yace “Zaki tafi, amma zaki bari zuwa safe idan aka duba aikin yayi kyau saiki tafi, daga baya kya dinga zuwa ana dubaki.”

D’aga kai tayi alamar toh, kasancewarshi dattijo ne yasa shi dafa kanta yace “Good girl.” Wani murmushin ya mata ya sake ficewa daga d’akin.

Likitan na fita shi kuma ya shigo da d’an farantin dake nuna abinci ne, akan gadon ya aje mata ta bi farantin da kallo, ganye yafi yawa a ciki wanda ta tabbatar saboda k’afarta ne akayi haka, ba dan tana so ba ta d’an ci tasha duk yana satar kallonta, d’auke kayan yayi ya sake fita ita dai ido ne nata sai kyab’e fuska da take duk in ta kalleshi.

Tun tana jiran dawowarshi har dai ta cire rai da dawowar tashi da wuri, shi kuma ko da ya fita had’uwa sukayi da Richard ya d’auki kayanshi yaje yayi wanka, daga nan gari suka shiga har ya samu damar kiran Kasim ya fad’a masa tafiyar da Farha zatayi, cikin dacewa kam sai yace mishi yanzu haka shirye shiryen tafiya Niamey yake zai je d’aukar wasu kaya, cikin jin dad’i yace kawai yaje ya d’auketa su taho tare da Mustafa ya rakota.

A gida kuwa sunyi sallar asuba Mustafa ya dawo daga masallaci yake fad’awa Mama yanzu Kasim ya kirashi, da mamaki tace “Yanzu tafiyar zakayi kenan?”

Da damuwa yace “Zanyi Mama ko dai zamuyi? Ni rakata ne zanyi dan karta tafi ita kad’ai.”

Mik’ewa tayi tana fad’in “To bari na fad’a mata kaima shiga ka shirya kar ya zo ya tsaya jiranku.”

Yanda tace haka yayi inda ita kuma ta shiga d’akin Farha da sallama, ta same ta har ta sake komawa kwance, daga k’ofar d’akin tace “Abokin mijinki ya kira yanzu Salahadeen d’in yace ya tafi dake yanzu Niamey acan za’a miki komai, saiki tashi ki shirya Mustafa zai raka ki.”

Zunbur ta mik’e tana fad’in “Yanzu Mama? Amma..to kuma…yo Mama ni.” Duk sai ta rasa abunyi da abun fad’a ma, fita Mama tayi bayan ta sake jadadda mata da tayi sauri, har ta nufi hanyar d’akinta kamar daga sama ta hangi alamun waya a k’ark’ashin kujera, dawowa tayi ta sunkuya ta d’auko, ai kuwa wayar Sarah ce wanda ta tabbatar ta jefar da ita ne sanda ta fad’i. Juyawa tayi ta koma d’akin Farha da wata sallama, har ta cire kaya zata shiga ban d’aki sai kuma ta tsaya, wayar Mama ta mik’a mata tana fad’in “Farha rik’e wannan dan Allah wayar Saratu, idan Allah ya kaiki lafiya saiki bata ko.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button