NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Da mamaki yace “‘Yarsa kuma? Saraf kake nufi? Yaushe aka sace ta?”

“A’a ba’a sace ta ba, amma dai ana shirin saceta, dan Allah ko kasan dalilin da yasa wani zaisa a sace ta?”

Da mamaki dai yace “Ban gane ba? Kana nufin wani ne zai sa a sace ta? Gaskiya bansan komai ba.”

Cikin rarrashi yace “Dan Allah ka daure ka fad’a min, a bayanan dana samu rayuwarta tana cikin had’ari, sannan a shirya yanda za’a sace ta.”

Girgiza kai yayi yace “A gaskiya ban sani ba.”

Gyara tsayuwa yayi yace “Misali idan na fad’a maka ni ne zan sace ta kuma mahaifinta ne ya saka ni, me zakayi tunani akai?”

Wani kallo ya masa yana murmushi yace “Sai nace zai tseratar da ‘yarsa daga sharrinsa ne, sai dai ba zai iya b’oyeta ba duk inda zai kaita a fad’in duniyar nan.”

Kallon tambaya ya masa yace “Sharrinsa, zai iya cutar da ita ne?”

Murmushin gefen labb’a yayi yace “Ya zaka ji nima idan na fad’a maka zai iya kashe ‘yarsa saboda son duniyarsa.”

Wani k’uri ya masa da ido yana kallo, kashe ta? Abinda yake shirin yi kenan? Ganin firgici a idon yaron yasa shi murmushi yace “Am jocking.”

Shigewa yayi mota dreba ya jashi suka wuce, k’arar motar ce ta dawo dashi hankalinshi, da gudu ya juya ya shiga motar ya tayar da tsiya ya d’auki hanya, kiran Richard yayi a waya ya tambaye shi yanda zaiyi ya bar k’asar da ita, dole ya tseratar da ita daga hannunshi, yasan tana da visa da passeport, ta n’aura ya duba mishi duk abinda kenan tare da musu buckin d’in jirgin da zai tashi awa d’aya, dan dama shima Salahadeen zai tafi a gobe, amma sai suka dawo da ranar a yau dan ya gaggauta barin k’asar.

A hanyarshi ta tafiya yake tunanin to wai taya zaiyi ya tafi da ita? Mahaifiyarshi ma bata san abinda yake yi ba a garin nan, haka ma matarshi bata san ma an kore shi daga makaranta ba, kawai yana raina musu hankali ne yana tura musu kud’i, a k’arshe yace musu ya samu aiki anan, ya zai koma da ita bayan yasan zai fuskanci k’alubale, ita kanta yarinyar ai zata bashi matsala ta ganta a wata k’asar da ba ta ta ba, amma kuma ceton rayuwarta shine mai mahimmanci a yanzu, duk da zai iya sa Richard ya b’atar da duk wata masaniya akan shi, amma kuma Shakoor shima shegen k’waro, yana da madatsa n’aura da manyan engineers, ko ba dad’e ko ba jima zai ganoshi. Kiran Richard kawai yayi yace su had’u a airoport ya taho mishi da kayanshi da sabuwar waya, bai b’ata lokaci ba tunda yaji abune na gaggawa, a filin jirgin suka had’u ya bashi sukayi sallama, saida ya dawo motar da wata yar kwalba kamar ruwa a ciki ya d’an zubasu a hanckiciep ya shak’awa Sarah a hanci, a hankali ta shiga bud’a ido tana d’an juya kanta, tana sauke ido a kanshi ta zabura tayi baya tana fashewa da k’ara, cikin azama ya rufe mata baki yana fad’in “Shiiii, saurare ni, nutsu ki saurare ni.”

Bige hannunshi tayi ta kama murfin k’ofar zata bud’e ya rik’e hannunta gam yana fad’in “Ki saurare ni nace, tare da mahaifinki nake.”

Tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi, ganin kallon da take masa yasa yace “Yana jiranki ne.”

D’an juyawa tayi tace “Ina Abhi na?”

Saida ya sunkuyar da kai yace “Ba kin ce kina son zuwa wajen danginshi ba?”

Cikin wani irin kallo tace “And so what?”

Gyara zamanshi yayi akan kujerar ya bank’are ya kwad’a mata k’arya kamar haka “Ya so ya baki mamaki ne ta yanda zaki bud’a ido ki ganki cikin yan uwanshi, amma ni ina tsoron matsalar da zan fuskanta a wajen s茅curity d’in wurin, shiyasa na tashe ki.”

Wani kallon rainin hankali ta masa tace “Amma me yasa Abhi bai turo min jirgi na ba? Ko a h茅licopt猫re na ai zai yarda na tafi.”

Ganin zata b’ata masa lokaci kuma bai da amsar bata sai kawai ya bud’e zai fita yana fad’in “Ki fito muje yace zamu had’u dashi a airport, lokaci na tafiya.”

Fitowa tayi da zungura zunguran takalminta ta tsaya har saida ya k’araso kusanta ta kalleshi da kyau tace “Ban sanka ba, jure moi que tous ce que tu ma dit c’est la v茅rit茅?”

Saida ya d’an daga hannunshi yace “Je le jure.”

Wuczwa tayi ya bita a baya yana kallon yanda take taka dogayen takalmin nan duk santsin wurin bata tsoron fad’uwa, d’an kawar da kanshi yayi a hankali yace “Mata.”

Dalilin Sarah sai ga Salahadeen ma yana samun gaisuwar girmamawa, tunda shahararriya ce da aka sani a tv da redio, dama jirgi na daf da tashi dan haka suka abka kawai aka shiga k’ok’arin tashi, a lokacin da ake sanarwar kowa ya kashe waya a lokacin kiran Shakoor ya shigo wayarshi, kashe wayar yayi gaba d’aya ya saka aljihu.

D’an kallonta yayi inda take kusa da taga tana kallo zasu tashi, zubin hallitarta zubin fuskarta, gashin nan sai d’aukar ido yake k’amshin turaruka da mayuka na tashi suna riskar hancinshi. D’an murmushi yaji ya saki sanda ya tuna lokacin daya d’aukota, babu nauyi cass kamar ya d’auki poupe, yanda gashinta ke lilo yana kallon k’asa haka dogon wuyanta yayi. Take kuma sai yaji tausayinta ya lullub’eshi, mahaifinta zai iya kasheta, duk da ba tabbas amma ba zaiyi wasa da lamarin rayuwarta ba, ba wai dan tana da mahimmanci gare shi ba, sai dan yana ganin bai kamata ta mutu ba ta hannun mahaifinta.

Sun sauka babban birnin Niamey inda ya samu abokinshi da zai tafi shima suka d’auki hanya tare…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 03:56 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa ta Orange money(ba chap chap ba yan uwa, orange money dan karka tura ta chap chap amma zaku iya tura kati) akan wannan lambar 91-71-28-22 ko kuma wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               4锔忊儯


             *Waiwaye*

Mutum ne mai matuk’ar hazak’a da k’warewa da k’ok’arin k’irk’ira a fannin Engineering, yana aiki a k’asar waje wanda ya lura basirarshi kawai suke anfanuwa da ita, amma a gaban idonshi ake nuna mishi banbancin launin fata da yare, a k’arshe ya yanke shawarar barin aikin ya dawo gida yayi wani abun, amma sai mahaifinshi yace bai yarda ba, ko ba komai yana samun na rufawa kansa asiri, sannan wajen aikin sun bashi masaukin da yake zaune, kasancewarshi mai dogon buri yasa ya hak’ura amma dama k’arama yake jira ya bar wurin.

Yana d’aya daga cikin wanda suke wakilci campagnin a wani taron k’arawa juna sani a England, a wannan tafiya ya had’u da Samanta wacce ya wa lak’abi da Sam, da fari soyayya ce dan Allah, amma bayan ta gabatar dashi gidansu mahaifinta kuma yana matuk’ar sonta dan ita kad’ai ya mallaka, hakan yasa shi sakin jiki dashi yana jawoshi jikinshi, a k’arshe aje aikin yayi ba tare da sanin iyayenshi ba ya koma gidansu Samanta, mahaifinta na shigar dashi duk wasu harkokinshi musamman daya ganshi yana da k’wazon nema. Ganin sun fahimci juna sai kawai suka yanke shawarar yin aure, bai yarda kowa ya sani daga b’angarenshi, dan yasan abu ne da ba zai yiwu ba, ba zasu yardar masa ya auri baturiya ba kuma wacce ba musulma ba, dan haka aka rufe akayi auren.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button