NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Tana zywa ta kai wannan takardar bayan ya bud’a ya kalla da kyau, kallonta yayi yace “Ya akayi haka Shakoor Aghali Sarah? Kince baki da aure, dama abinda kikeyi kenan a masaukin naki?”

Girgiza kai tayi tace “Zan maka bayani malam, zan fad’a maka komai daya faru idan ka bani izini.”

Cikin rashin jin dad’i ya girgiza kai ya kalleta yace “Ki tabbatar duk abinda zaki fad’a gaskiya ne zai fito daga bakinki.”

Jinjina kai tayi tace “Insha Allah.”

Nutsuwa tayi sosai ta fara fad’a mishi labarinta, duk da a d’an tak’aitacen lokaci ne amma bata tak’aita labarin ba, komai ta fad’a mishi daga zuwanta niger har d’aura aurensu mutuwar mahaifinta zuwansu k’auye da abinda ya faru. Ahiyar zuciya ya sauke ya kalleta yana cire gilashin fuskarshi yace “Sarah na yarda dake, kinsan me yasa?”

Girgiza kai tayi hakan yasa yace “Saboda banga alamar k’arya a abinda kika fad’a ba, sannan ba zaki yarda ki fad’i k’arya akan mahaifinki ba ta hanyar shafa mishi bak’in panti, hakan yasa zan miki wani taimako d’aya, insha Allahu zanyi magana da sauran shuwagabannin makarantar nan, zan fad’a musu komai na tabbatar zasu baki damar ci gaba da karatunki, amma yanzu shawarata gareki ita ce ki nemi uban yaronki ki sanar masa halin da kike ciki.”

A hankali tace “Nagode malam, nima abinda nake shirin yi yanzu kenan, zan je har can na same shi tunda ban da contact d’inshi.”

Jinjina kai yayi yace “Zaki iya tafiya ki same shi, zan nemeki a waya dan kiji yanda mukayi da malaman.”

Jinjina kai tayi ta mik’e da farin ciki ta fita tana godiya, ko da ta fita anan masaukinta ta koma ta d’auki passeports d’inta da kud’i ta fita, harka da kud’i ga kuma wanda ya saba a d’an k’ank’anin lokaci saiga ta a k’asar Niamey. Babbar sa’a da tayi ita ce sapun bus d’in da zata tashi k’arfe biyu na rana zuwa Zinder, bata tsaya komai ba ta shige kawai suka d’auki hanya, titi kawai take kallo yanda suke gifta bishiyoyi da gudu, gabanta fad’uwa yake duk in ta tuna ciki ne jikinta, bata san wane irin karb’a zai mata ba sai dai ta tabbatar Mamie ba zata kunyata ta ba, matarshi dai ce tasan ba zata yarda ba, ita kuma ba ita bace a gabanta, shi take so ya sani ya kusan yanda zaiyi da kayanshi.

馃槀 Ya fa zaiyi?

A k’alla ko da k’arfe bakwai tayi sun isa garin kowa ya fito, masu abun siyarwa ne duk suka rufesu hakan yasa ta siyan robar lemu dan ta jik’a mak’oshinta, data karb’a ko canji bata jira ba haka kuma ata damu data sha ba ta nemi inda zata samu motar da zata d’auketa daga nan zuwa maradi, saida ta tabbatar ta samu wata bus da zata tashi daga nan zuwa can hankalinta ya kwanta, cikin motar ta shiga ta zauna ta bud’a lemun ta fara sha, zallar magwaron ya mata dad’i, haka kawai ta samu kanta da dubawa ta ga miye sunanshi da kuma ingr茅dient d’in da aka sarrafashi dasu, sunan Sla ta gani a jikin lemun, sake karantawa tayi da kyau tace “Sla? Wannan kuma wane irin suna ne?”

D’aga kafad’a tayi alamar oho kawai ta ci gaba da kurb’a a hankali har k’arfe takwas tayi aka tashi motarsu.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:17 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               3锔忊儯4锔忊儯

Tun safe yake ta kiranshi amma matsalar sadarwa yasa bai samu ba sai yanzu da dare har ma ya kwanta shi saboda tashin dare da yake, saida ya fito falo dan kar ya tashi Farha sannan ya d’auki kiran, daga can b’angaren aka ce “Haba Salahadeen miye haka? Tun safe nake kiranka amma bana samu, kuma gashi ban ganka online ba.”

Cike da kasala yace “Kayi hak’uri Richard wallahi yau naje k’auye ne duba yanayin aiyukan da ake min, ya ake ciki ne yanzu?”

A take yace dashi “Akwai matsala fa.”

Gabanshi yaji ya fad’i a take kanshi ya sara da k’arfi yaji kamar jikinshi zai d’auki rawa rawa, da k’yar ya bud’a bakinshi da yaji har yayi nauyi yace “Me ya faru? Wace irin matsala? Me ya sameta?”

Daga b’angarenshi ya amsa da “Matsalar dai ita ce wanda nasa yake bibiyar lamarinta yau shima zai dawo nan gida Tha茂lande, ita kuma Sarah izuwa yanzu inaga tana daf da kai.”

Jin yace daf dashi yasa shi juyawa hagu da damanshi ya duba, sai kuma yaji ya ba kanshi dariya kafin yace “Kamar ya tana daf dani Richard?”

A hankali ya shiga fad’in “Daren jiya sun had’u da uncle d’inta Kabeer, ma’aikaciyar hotel d’in ta tabbatar min da taga fitarta, amma sam basu ga dawowarta ba bare shigarta, abun al’ajabin kuma shine d’aya daga cikin ma’aikatan wanda yake kan duty ya tabbatar daya sameta a d’akinta tana bacci sanda yaje kai mata ganyen shayin da take anfani dasu wanda shi baiyi tunanin tana nan ba saboda basu ga dawowarta.”

Cikin al’ajabi ya mik’e tsaye ya fara safa da marwa yace “Ta ina kenan ta shiga?”

Ajiyar zuciya ya sauke daga can yace “Babu wanda yasan haka, ba wannan ne zai baka mamaki ba Salahadeen sai kaji cewa ba da makulli ta bud’e d’akin ba, dan in zata fita tana barin makullin a r茅ception idan ta dawo ta karb’a, amma a daren jiyan bata karb’a ba kuma an sameta a d’akin, hasalima sanda ma’aikacin yaje kai mata ganyen saida yasa makulli ya bud’e k’ofar.”

Da mamaki da kuma d’aure kai yace “To me ya faru da ita kenan? Shiyasa fa tun farko na fad’a maka bana son ganin Kabeer d’in nan, duk yanda akayi akanshi ne alamomin tambayarmu zasu tsaya, to amma yanzu kace tana daf dani, ina take kenan?”

K’arasa mishi yayi da fad’in “Da rana ta fito daga makaranta ta koma masaukin, ta bayar da makullin d’akinta tace zatayi tafiya, da ya bi bayanta kuma saiya samu a茅roport ta nufa inda ta hau jirgin da zai kaita Niger, daga nan ne kuma bamu sake sanin me ke faruwa game da ita ba, shiyasa nace maka watak’ila tana daf da kai.”

Da sauri ya juya ya nufi d’aki yana fad’in “Shiit, duk yanda akayi akwai abinda ya faru, kuma na tabbatar nan zata zo, Richard zamuyi magana da kai.”

Da gudu ya k’arasa shiga d’akin ya d’auko makullin mota, sam ya manta da kayan dake jikinshi wando ne iya gwiwarshi da rigarshi sai slipas ya fita, duk da ba wani dare bane dan ko sha d’aya da rabi ba tayi ba, amma da yake ba mutumin cika dare a waje bane sai yake jinshi a daban yau. Gudu yake a mota inda zuciyarshi ta raya mishi gidan bus d’in dake kusa da filin jirgi zata shiga, dan haka kawai can ya nufa shima kai tsaye duk a rikice yake.

Kamar jiran isarshi ake a wurin sai kuwa hadari ya taso tare da iska da kuma ruwa sosai, bai fita a motar ba sai kallon wurin daya shiga yi yana son gano wace motar ta zo yanzu, ganin shiru yasa zuciyarshi fara raya mishi idan fa ba nan bane? Kenan tana can ta wani wurin yanzu, to wai ma ka tabbatar nan ta taho? Tsaki yayi sai yaji ma haushi ya kama shi daya kasa tsayawa yayi lissafi da kwakwalwa ko tunanin abinda zaiyiwu kawai tunanin ya ganta ya rufe mishi tunani. Wani tsakin ya sake yi ya daki sitiyari yayi wa motar key zaiyi ribas, odar bus d’in ce tasa shi wani fad’uwar gaba har saida yaji abun a tsakar kanshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button