NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Duk mutanen sai suka koma kallonshi suna maganganu k’asa k’asa, Sandra ma ganin mijinta ya shiga sai ita ma tace “Nima zan shiga tare da kai.”

Da farin ciki ta rumgumesu dukansu tana ma Allah godiya, saida ta sallami ma’aikatan ta nemi da s茅curit茅 d’in daya kira mata malam ya rakata wajenshi tare da su Joseph, tare suka tafi a mota ya kaisu suka gurfana wajenshi a cikin masallaci, bayan ta gabatar mishi da abinda ya kawosu yayi murna sosai, a take ya basu kalmar shahada tare da fad’a musu wasu abubuwa dake dole su fara sani yanzu, daga bisani ya sallamesu yace da safe su same shi sai su d’ora insha Allah. Ita ma anan ta nemi daya had’ata da wani wanda zata iya nema idan ta tafi Mekka, wani adreshi ya rubuta ya bata sannan suka tafi, gida suka dawo inda ta umarci Sandra data kwashe duka suturarta dake d’akinta ta rabar dasu, akwatina da kwalaye ta dinga fitowa dasu ana sawa mota ana fita dasu daga gidan, ita kuma ta shirya cikin riga har k’asa mai hannaye ta yana wannan kallabin a kanta sannan tasa aka shirya mata jirgin mahaifinta, a mota tare da rakiyar su Sandra ta isa inda jiragen masu kud’i suke jibge, basu tsaya komai ba ta shiga suka d’aga zuwa k’asar mekka (inji bature).

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:16 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               3锔忊儯2锔忊儯

Tana sauka taxi ta kaita babban masauki dan hutawa kafin gari ya waye ta nemi malamin da waccen malamin ya had’ata dashi, cikin kulawa da girmama bak’i aka rakata zuwa d’akinta, bata nemi komai ba sai kaya data cire ta shiga tayi wanka ta fito, lallausan kayan bacci ta kwanta bayan ta sake yin addu’ar bacci kamar jiya.

Tunda Richard ya tabbatar masa da komai dake faruwa ya d’auki hanya ya koma, bayan zuwanshi gida Mama ta nuna mishi abinda ta bar musu, cikin rashin kulawa yace “Mama ki rik’e kawai ke ta ba.”

Da mamaki tace “Ban gane ni ta bawa ba bayan har da sunanka ta fad’a.”

A kasalance ya kalleta yace “Ni zan je na kwanta Mama na gaji.”

Wucewa yayi d’aki ta bishi da kallo, yana shiga Farha ta bi bayanshi, ya fara cire kayanshi zai kwanta ta durk’usa gabanshi cikin muryar rarrashi tace “Dan Allah yaya Salah kayi hak’uri da duk abinda ya faru ka yafe min, wallahi sharrin shaid’an ne da kuma son zuciya, amma na gane kuskure na insha Allahu ba zan k’ara ba.”

Murmushi yayi tare da kamota ta mik’e tsaye, rumgumeta yayi a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya, lumshe ido yayi bai ce komai ba har kusan minti biyu, a hankali ta sake cewa “Yaya baka ce komai ba, ko baka yafe min ba?”

D’agowa yayi daga jikinta ya tallabo fuskarta, a hankali ya sumbaci bakinta sai kuma ya tsaya ya d’an kawar da kanshi yana cije leb’enshi.

Kallon fuskarshi tayi sai taga kamar wani abu yake b’oyewa, a hankali tace “Yaya.”

Kallonta yayi sai kawai yayi k’unar bak’in wake ya sake durmiya da ita duniyar ma’aurata, zuciyarshi bata tare dashi a lokacin, tunanin halin da yar amana take ciki yake, yana so ya kasance kusa da ita ko kuma ita ta kasance kusa dashi dan yasan duk wani motsinta, sai dai ta k’i bashi damar hakan, gashi tun jiya duk ya rasa sukuninshi kamar wanda yayi shekara tare da ita, komai daya wakana a tsakaninsu na dad’i da akasinshi ne ke ta dawo masa akai.

Da dare sunyi nisa a bacci Farha na kwance gefenshi yaji wayarshi tayi k’ara alamar message, a hankali ya d’auki wayar tare da bud’ewa, sak’on Richard ne yana sanar dashi Sarah fa bata k’asar yanzu haka tana mekka, yayi mamaki sosai tare da son sanin me ya kaita can? Amma daya fad’a mishi bai sani ba shima saiya shiga tunanin ko lafiya? Sam bacci ne ya k’aurace masa har asuba.

Da safe ya sake zama dasu mama kan sabon tsarin da yake so gidan guardin da gonarsu su kasance, dan haka mama tace to ya d’auki kud’in nan sai suyi abinda ya dace, amma ya murje ido yace wallahi sisi ba zai d’auka ba, kud’in da suka rage hannunshi yace zaiyi abinda ya dace, haushi da Mama taji ne yasa ta bawa Zeid da Mustafa wasu daga cikin kud’in tace su canza su ja jarin da suke buk’ata.

Haka kawai ya samu bak’i daga k’auye wai sun zo kan maganar baturiyar da aka ce matarshi ce, abun mamaki har da k’anwar mahaifiyar Farha ma tare dasu, kafin shigowarshi bala’i suke ta ma mama wai ta ci amanar d’an uwansu data yarda ya auri wata baturiya, tunda dai ba zaiyi aure ba ba tare da amincewarta ba, ga gajiya ga haushin tafiyarta da yake ji sai kawai ya kallesu dukansu yace “Dan Allah ku manta da maganar wata baturiya, ta koma inda ta fito dama kuma ba mai zama bace, shikenan yanzu kun ji dad’i?”

Fita ya sake yi daga gidan inda ya samu ya kunna sigari dan rage b’acin ranshi, hakan da yayi ma basu tsira ba dan sai suka ce tana kallo ya musu rashin kunya, haka dai suka tafiyarsu kowa rai a b’ace ita kuma daga nan da akayi ta watsar dasu bare abun ya dameta.

Mekka, cikin ikon Allah ta samu malamin data nema, wata babbar islamiyya ya sauketa wacce ake wuri karatu, ajujuwa bila adadin sai fannin da kake son karanta zaka zab’a, idan kana son ilimi akan hadisi ko Qur’ani ko fiqhu ko tauhidi da dai sauransu, bata zab’a da kanta ba face cewa da tayi a zab’a mata matsayinta na sabuwar shiga akan komai. Ta zab’i wuni nan ta dinga karatun Qur’ani da kuma hadisi, kafin idan ta fara kwari sai taje mataki na gaba, duk wani abun buk’ata na karatu da komai ta biya wa kanta, daga nan kasuwa ta wuce tayi siyayyar kayan sawa, kaf dogayen riguna ta siya kala kala masu kyau wanda suka karb’i jikinta, sai beby hijab wanda zasu dace da rigunan da kuma takalmi ballerine.

Tunda ta zo garin saiya daina ganin duk wani motsinta bare ya ganta a allon bangonshi, hankalinshi ya tashi akan haka dan haka ya sake zuwa gidan dan ganin ko har ta tafi Spain d’in ne, daga bakin tsirarun ma’aikatan da suka rage ya samu labarin bata k’asar tana mekka, sai lokacin ya fahimci dalilin da yasa yanzu zata shiga cikin kariyar data fi wacce ta fito a baya. A hankali ya kwatantawa shugaban k’ungiyar yanda ake ciki, tare da sake jadadda mishi alk’awarin lallai fa zai kawo mishi ita da hannunshi.

            *A gurguje*

Ta fara karatun da gaba d’aya zuciyarta kuma zuciya d’aya, ta aje komai gefe d’aya karatunta kawai ta bawa hankalinta, idan ta fita tun bakwai na safe sai tayi sallah isha’i a harami take komawa gida, wannan lokacin na hutu daya rage mata ma karatu take yi kafin ta d’an duba abinda zata iya a wayarta ta kwanta, sam maganar tsorata ta ko barazana ta kau, cikin aminci take bacci ta tashi cikin salama, harda harta fara zauna mata akai na karatu, malaman kansu suna mamakinta, sai dai ba abun mamaki bane duba da dama wanda ya shiga addini daga baya yafi kowa rik’eshi da mahimmanci, to hakane a wajen Sarah ma yanda take d’aukar al’amarin addinin nata yafi yanda take shak’ar numfashinta ma mahimmanci.

Saida Kabeer ya sake turo mata David anan, to amma Sarah ta baya data yanzu ba d’aya bane, duk hanyar da zaibi ma ya mata magana ya gagara, shigarta kad’ai ta yanzu firgitashi take, sau d’aya yayi nasarar yi mata magana da suka had’u ta fito ranar babu karatu, ta fito daga wani shago shi kuma yana ta biyarta, suna had’ewa bai ankara duk saiya rud’e ya shiga kame kame, murmushi ta mishi cikin tsari tace “Hi David, what are u doing here?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button