NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               3锔忊儯6锔忊儯

“Mr. ina so zan tafi ne, Mamie tace na zo na sanar da kai.”

Shiru bai ko motsa ba kamar ma bacci yake, yatsina baki tayi ta harari bayanshi ta tab’e baki ta juya tana fad’in “Shikenan ni na tafi.”

Saida yaji ta kama k’ofa zata fita ba tare daya juyo ya kalleta ba murya k’asa k’asa yace “Zo nan.”

Tsayawa tayi tana mai mamakin yanda bawan Allahn nan ke tuk’ata son ranshi, ta fahimci tun farko dukiyarta ko izzarta basu dameshi ba, hasalima banza yake yi da ita bare ya nuna yana shakka ko wani abu, dawowa tayi ta tsaya gaban gadon tace “Gani mr.”

Can mak’oshi ya sake cewa “Ni kike so na sameki anan ko me? Ba cewa nayi ki zo nan ba.”

Da yake da hausa yayi magana sai kawai ta kwarkwance ta nuna masa bata fahimci me yace ba tace “Mr. i don’t understand what to say.”

Tashi yayi zaune tare da juyowa yana kallonta, fuskarta ya tsura ma ido har taji ta tsargu da kallon, kasa kallonshi tayi saita shiga kalle kalle a d’akin, duk da d’akinta na da ya ci uwar wannan wajen kyau da had’uwa, amma tsari da rashin hayaniyar wannan d’in sai taga ya birgeta, ganin bata kallon inda yake ma yasa shi k’ara matsowa ya sauko k’afafunshi k’asa yana kallonta yace “Ba zaki tafi ba, ko ban fad’a miki haka ba?”

Gyara tsayuwa tayi tace “Ina karatu fa acan, me zaisa na zauna anan?”

Yanda ya sake tsura mata ido yasa tayi saurin cewa “Na maka alk’awarin ba zan sake mantawa da Mamie ba, zan karb’i lambarta yanzu zan dinga kiranta.”

Kallon da babu alamar wasa ya mata yace “Ke! Ni ba mahaukaci bane ko sakarai, ki zauna anan idan kin haife abinda yake cikinki kya tafi duk inda kike so.”

Kyab’e fuska tayi da baki da mamakin abinda ya fad’a, sai kuma tayi tunanin bari su rabu lafiya kawai tayi tafiyarta, juyawa tayi tace “To bari na koma na kwanta.”

Har ta kama k’ofa zata fita idonta ya sauka akan robar lemu da sunan irin lemun data siya, tsayawa tayi ta d’an matsa kusa dashi ta d’auki robar tana kallo ta juyo tace “Mr. wannan lemun me sunanshi ke nufi?”

Mik’ewa tayi tsaye ya fara takowa gabanta, a take taga hannayenta sun fara wata rawa rawa gabanta sai wata dokawa yayi, inda jikinta ya shiga fitar da wani dumammen sauti k’afafun na barazanar gagara d’aukarta, sunkuyar da kanta tayi saboda tunanin samun sauk’in abinda take ji, duk da bashi da tsayi sosai, amma k’irarshi ta karfafa ce ga kuma shafaffen cikinshi zuwa mara. Saida ya tsaya kanta daf da ita sosai yasa hannu ya karb’i robar, kallon robar yayi yace “Kin manta daga ina sunan nan ya fito?”

D’aga kai tayi amma sai bata kalli ko da fuskarshi ba bare idonshi tana k’yabta ido tace “Umm, na manta.”

Aje robar yayi a inda ta d’auka ya juya ya nufi gadon yana fad’in “Bari idan kika haife abinda ke cikin, kafin ki bayar da sunan mahaifinshi sai kiyi tunani.”

Da sauri cikin rashin fahimta tace “Kamar ya? Ka fad’a min yanzu mana.”

Zaune yayi bakin gadon kanshi k’asa cikin sauti mai nuna k’osawa yace “Me ye sunan uban d’anki?”

Da saurinta kuwa tace “Slah…” Sai kuma tayi cak, d’agowa yayi ya kalleta jin tashi shiru sai kawai ta bushe da dariya cike da kunya ta juya da gudu ta fita a d’akin dan ta harbo jirgin yanzu kam, shi kanshi murmushi yayi tare da fad’awa kan gadon yana lumshe idonshi.

Tana fita a lokacin ne Farha ta hawo sama suka had’e, kallon juna sukayi sai kowace taji wani abu a ranta, cikin rashin damuwa Sarah ta rab’ata zata wuce ba tare da tace mata k’ala ba, cikin jin haushi ta shak’o hijabinta wanda ya fita daga saman kanta tana fad’in “Ke! Me ya kaiki d’akin mijina?”

K’ok’arin k’watar hijab d’inta ta shiga yi saita sake rik’ewa sosai tana fad’in “Nace me ya kaiki d’akin mijina? Kenan karuwancin ne zakuyi min har gida? To wallahi baku isa ba bari kiga.”

Ita fa har ga Allah bata tunanin komai ko ta cutar da ita, turata kawai tayi cikin jin haushi ta nufi d’akin nashi, amma abunka ga shagwab’abb’iya sangartacciya da kuma tsautsayi wanda baya wuce rana, sai kawai Sarah ta fad’i akan benen ta shiga gangarawa tana ihu, jin ihunta yasa ita kanta Farha tsayawa cak ta juyo da sauri tana kallonta, shima da yake neman bacci ya d’aukeshi da wani irin gudu ya fito daga d’akin, bai lura da wata Farha dake tsaye ba ko ya ankara da ita, bai sani ba shi dai ya tsaya taka matakalar ko kuma shima gangarawar yayi, shi dai bai sani ba ganinshi kawai yayi k’asa kusanta ya tallabota.

Dakewa tayi sosai ta bud’a ido ta kalleshi duk da rad’ad’in da take ji a jikinta da kuma k’asan mararta, a hankali ta kalli hannunshi dake rik’e da nata hannun gam ya zuba mata ido da yanayin damuwa sosai da kulawa, cikin alhini da tausaya mata yace “Sannu Sarah, ya akayi kika fad’o?”

A hankali ta d’aga idonta ta kalli inda Farha ke tsaye a sama har yanzu, juyawa yayi ya bita da kallo shima sai lokacin ya kula da ita, lumshe ido tayi tare da cije leb’e, sai kuma ta bud’e ta shiga kiciniyar mik’ewa da k’afafunta, a daidai lokacin mama ta fito da sauri tana salallami da taji ihunta, k’arasawa tayi tana fad’in “Ita ce ta fad’o? Sarah wajen rawar kan naki ko? Na fad’a miki ki dinga kula fa.”

Saida ya taimaka mata tayi tsayen sai taji ba zata iya ba kuma, har zata rik’e hannun Mama sai kuma tayi saurin dafe mararta tana sake yatsina fuska, sake daurewa tayi ta d’ora k’afarta ta hagu zata takata ta tsaya, amma sai taji wani azababben zafi a k’afar kamar ta karye ko gocewa, da wani saurin bala’i ta damk’o hannunshi ta rirrik’e tana rintse ido, juyawa yayi ya kalli Farha dake saukowa daga matakalar yace “Ya akayi ta fad’o? Me kika mata?”

Cikin rashin gaskiya da son kare kanta tace “Ni fa babu abinda na mata, kawai tab’ata ne nayi kuma na saketa ban mata komai ba.”

Saida mama ta matsa kusan Sarah ta kamata ta kalli Farha tace “Farha baki tunanin ki ji mata ciwo? Ba fa ita kad’ai bace yanzu sai ana kulawa.”

Sarah dake cije baki sosai sai wani zafi had’e da gumi da taji yana karyo mata lokaci d’aya, cikin jin haushi ana son d’ora mata laifi tace “Nifa ba abinda na mata na fad’a muku, kawai dan nema na da sharri daga tab’ata saita durko ta fad’o k’asa, dan tasan dama ni ba k’aunata ake ba tunda ban da komai, tana so taga ta jaza min bala’i shiyasa ta fad’o da gangan.”

Duk kallonta sukayi amma da sauri Sarah ta sake damk’o Mama tace “Mamie, zafi, zafi…kaini na zauna.”

Sake rik’eta tayi da kyau suka juya a hankali tana takawa, sai dai abinda Salahadeen ya lura dashi a tafiyarta shine bata taka d’aya k’afarta, rintse ido yayi cikin takaici da azabar tausayin da zuciyarshi ke d’awainiya dashi, bin bayansu yayi sam ya manta da jikinshi babu riga, ya kuma manta da rabon da ya iya tsayawa gaban mama babu riga haka tun yana da k’uruciya sosai. Har mama ta zaunar da ita ta sake yin ram da rigar mama ta cukuikuye tana jan iska da bakinta alamar rad’ad’i, cikin kulawa Mama tace “Sarah ciwo kike ji?”

Da sauri ta shiga gyad’a mata kai alamar eh, d’orawa tayi da “A ina kike jin zafn?”

Sakin rigar Mama tayi ta kama kujerar data zauna akai ta rik’eta gam tana sulalewa k’asa, kamar tana son jure ciwon da take ji amma abun yafi k’arfin tunaninta, dan ciwo ne da babu wani ciwo data tab’a ji bare ta kwatantashi dashi, ko ciwon mara na lokacin watanta da takan sha azaba bata kai wanda take ji yanzu ba, bare kuma shi da taji yanzu ya d’an sassauta mata ma wata biyu da suka wuce. Cikin fara fita a hayyaci ta cire hijabin dake wuyanta ta jefar, har za tayi zaune sai kuma ta mik’e tsaye tana durk’ushewa, da azama ya sake matsowa yayi shirin sungumarta yana fad’in “Mama muje asibiti, mu kaita asibiti a duba ta.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button