NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Hannunshi da yake daddab’awa ta rik’o ya matse a k’irjinta, hannun na kaiwa ya matse ido ya furzo wani iska, ita kanta tana jin hannun mutum ne tayi saurin bud’a ido, ko da suka had’a ido ta zabura ta mik’e zaune tana k’ara kallonshi, da sauri tace “Mr., what are u doing here? Where is mamie?”

Wata k’akk’arfar numfashi ya sake saukewa bai ce mata komai ba, har yanzu gabanshi fad’uwa yake ga wata wutar lanyarki da yaji ta taji daga sama ta bankashi k’asa, kofin dake hannunshi ya mik’o mata tasa hannu ta karb’a, saida ta kurb’a d’aya biyu ta kalleshi tace “Merci.”

Mik’ewa tayi tsaye ta bi ta gabanshi ta wuce ta zauna kan kujerar dake d’akin doguwa, a hankali ya mik’e zai fita saida ya kai k’ofa tace “Mr. wanka zanyi.”

Kallonta yayi yace “Na miki kenan?”

Saida ta matse kafad’unta wuri d’aya tace “Idan na samu haka ma zanji dad’i.”

Wani kallo ya mata ya fice daga d’akin, saida ta gama sha ta fito farfajiyar gidan babu kowa, ta manta da sai ta d’auki bokiti ta zuba ruwa sannan ta shiga bayin, ko da ta saka takalmi kawai ta nufi ban d’akin kanta tsaye, saida ta shiga ta ga babu ruwa ta fito ta d’auki bokiti kamar yanda taga sunayi.

Tarawa tayi bakin panpo har ya cika, hannu d’aya tasa ta d’aga bokiti sai taji har ga Allah yafi k’arfin d’aukarta cikin sauk’i, yana buk’atar saita saka k’arfi sosai, har zata saka hannu biyu taji motsin mutum, juyowa tayi ta ga Salahadeen ne ya fito tare da Farha a bayashi da alama zai fita, bata yarda ta had’a ido da Farha ba ta kalleshi tace “Yawwa mr. taimaka min da bokitin nan mana.”

Wani kallo ya mata na jin kawai raina shi ne tayi yace “Wannan bokitin ne ba zaki iya d’auka ba? Idan da Bugger ko pizza ce kin iya d’auka ki kai bakinki ba.”

Tsakaninta da Allah kuwa ta kyab’e fuska tana shirin yin kuka, tunawa da maganar mama na amana ce ta bar mishi yasa da sauri yace “Ba sai kinyi kukan ba zan d’auka.”

Zai wuce Farha ta rik’e hannunshi tace “Yaya me yasa zaka dinga biye mata? Duk abinda tace ka mata sai kayi ba zaka iya musa mata ba, ruwan ne ba zata iya kaiwa ba sai an kai mata?”

Kallon fuskarta yayi yace “Bari dan Allah na kai mata, kukan nan ne bana so wallahi.”

Sakinshi tayi cikin hushi ta juya ta koma d’aki, yana kai mata ya juyo zai fito suka ci karo, tsayawa sukayi kallon juna yanda sukayi kusa sosai, rab’ashi tayi zata wuce taji ya rik’o gefen rigarta, tsayawa tayi tana kallonshi shima ita yake kallo ya dawo da ita baya.

Gashinta ya nuna mata yace “Babu kyau shiga ban d’aki babu d’an kwali akai, tunda wanka zakiyi ki d’aure shi idan kika fito saiki sake shi, sannan ki dinga addu’a saboda neman tsari.”

Ba alamar damuwa tare da ita ta juya mishi baya tana fad’in “D’aure min, bansan yanda zanyi ba da kaina.”

Rarraba ido ya shiga yi yana kallon gashin, cikin rashin fahimta yace “To taya ni kuma zan iya inke baki iya ba?”

Juyowa tayi zata shige ban d’akin tana fad’in “To barni na wuce kawai.”

Da sauri ya sake rik’eta, saida ya harareta ta wutsiyar ido ya juya kanta baya, kusan kad’an ne ya fita tsayi, haka ya dandage yasa duka hannaye yana tattaro gashin mai shegen sulb’i ga kuma tsayi, ji yayi ya samu kanshi cikin nishad’i da son ci gaba da shafa kan har zuwa lokacin da zaiji ya gaji, haka ya dinga tattara shi yana matsewa a d’aya hannun yana kameshi amma ya k’i d’aure mata.

Gajiya da tayi yasa a k’ufule ta bubbuga k’afafunta tana fad’in “Mr. fitsari zanyi fa anan.”

Hankali kwance yace “Kiyi mana, waye za’a ce mai fitsari daga tsaye?”

Bushewa tayi da dariya tace “Yan uwanka sai su ce matarka mai fitsarin tsaye.”

Wani duka yaji a cikin k’irjinshi sanda ta ambaci matarka, baisan me yasa yake yawan jin fad’uwar gaban ba haka kawai, a hankali ya shiga laulaye mata yana dunk’ule mata shi, yana idawa ya saki sai ya ga yana shirin warwarewa saboda sulb’i, da sauri ya rik’e ya sake mayse shi saiya laulaya ya mata kamar gammo akai ya sokeshi ya tsaya tsaf, wajen sokarwa saida ya kusa kaiwa k’asa saboda sosai ya soka shi da zafi.

Da sauri ta shige ban d’akin inda yace “Addua’r fa?”

Daga ciki har ta duk’a yin fitsarin tace “Idan na fito ka koya min sai nayi gobe.”

Wucewa yayi sai dai har ya kai k’ofa ya tuna da mama tace amana fa, kuma akwai abincin karinta bai ma nuna mata ba, dawowa yayi ya koma d’akin mama ya zauna kan kujerar yana jiran ta fito.

Bata wani jima ba dan sabulun kad’ai ta iya d’an gogawa a jikinta ta fito, ganin ba kowa gidan kawai yasa ta sako pant d’inta rigar kuma ta yafota a k’irji ta fito, tana shiga d’akin bata kula dashi ba dan takalmi ma k’afa ciki ne kuma ya shiga dasu dan ya ga mama bata nan.

Cire rigar tayi ta jefa kan katifa ta duk’a inda taga Mamuh na ajiye mai ta d’auko, cikin sauri take shafawa k’afafunta man ko fuska bata shafawa ba ta rufe ta aje. Salahadeen na zauna ya kasa katab’us, yana so yayi ko da gyaran murya dan ta gane da mutum amma yaji kamar ya cika bakinshi da tuwo ya kasa, yanayin daya tsinci kansa da zai fad’i gaskiya to matuk’ar sha’awa ce ta bijiro masa.

Mazaunanta dake cikin farin pant masu fad’in gaske, d’an tudun ba wani sosai ba, a rayuwar da yayi can ya ga d’uwawu iri daban daban, hatta na matarshi ma Farha sunfi wannan sau uku, amma me ye a tattare da nata da yaji sun d’auki hankalinshi tare da firgita mishi nutsuwa a nan take.

K’ugunta daga sama zuwa cikinta a bud’e yake ga kuma fad’i sosai, dogon bayanta wanda ke rufe rabinshi ke rufe da gashin kanta da dogayen k’afafunta, idonsa yake so ya d’an kawar ko yaya dan karta juyo ta kama shi yana kallonta, amma wallahi ya kasa sai lumshe su da yake a hankali yana sake bud’esu kanta.

Ledar kayan daya siyo mata ta bud’a ta shiga fito dasu, pant da bras d’in saida ta fito da dukansu kafin ta d’auki wasu bak’ak’e zata saka, mik’ewa tayi daga durk’ushen da tayi ta saita hannunta kan k’ugunta ta fara zame wandon daya rage mata.

Wata irin numfashi ya shiga saukewa da nufin taji sautin ta juyo, amma sam bai fahimci numfashin ya kasa fitowa ba, lumshe ido yayi dan hakan ne kad’ai mafita a gareshi, tunda ko k’amshin turarenshi ya k’i sanar da ita cewa da mutum a d’akin.

Saida ta kai shi sama ta k’arasa sawa kawai yayi kip alamar ko da ya shigeta ma zai matseta, k’ara ja tayi amma taji ba zai saketa yanda zata wala ba ko ta takura shi ta saka, cikin jin haushi ta juyo tana zage pant d’in tana fad’in “Taya ma zai siyo min wannan abun? Me ya d’auki to? Yariny…aaaaaaaa”

Bata k’arasa maganar ba ta ganshi zaune ido rufe, hakanne yasa ta sakin k’ara tare da fad’awa kan katifar dan pant d’in bai fita ba hakan yasa ya rik’e mata k’afafu. K’arar da tayi ce ta fargar dashi ya bud’a ido da sauri tare da tashi da gudu dan ya rufe mata baki baya so Farha taji har tasan me ke faruwa, da niyyar rumgumota ya tafi sai dai kuma ta fad’a kan katifar, hakan ya tilasta mishi fad’awa katifar shima bai shirya ba.

Da saurin bala’i ya mik’e zaune ya fizgota jikinshi, a tsorace ta kalleshi ba tare da wani yunk’uri na kare jikinta ba, dan b’oye halin daya riga ya tsunduma yasa bai had’a ido da ita ba, sauke idonshi yayi kan wuyanta da nufin magana, amma sai yaji sun rinjayeshi zuwa k’irjinta, da wani irin amo da cunkushewar numfashi ya furta “Allah na.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button