NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL


Nesa da kampanin suka tsaya suna hangen masu gadin k’ofar su biyu da uniforme iri d’aya, kallon L茅o yayi yace “Kaje ka bincika mana kaji me zasu ce.”

Murmushi yayi ya fita a motar ya nufi wajen, daga nan zaune suka dinga hangensu sai sakin murmushi suke ganin yanda L茅o har yake durk’usawa gabansu yana kukan k’arya yana rik’e k’afar d’aya daga cikin masu gadin, bushewa sukayi da dariya sanda ya mik’e ya juyo zai dawo ka rantse ba shi ne yake ta burususuwa a can ba, yana zuwa ya bud’a k’ofar ya shiga ya zauna, kai tsaye yace “Sun nuna basu san komai ba, a cewarsu ma yau ranar hutun ma’aikata ne babu wata mota data shiga ciki.”

Murmushi yayi shima, Richard ne ya kalleshi yace “Yanzu miye abunyi?”

Ba tare daya kallesu ba yace “Leo ka sa mana ido a kampanin nan, ina so na tabbatar da abinda suka fad’a, ka kula mana da duk wani shige da fice na wurin.”

Jinjina kai yayi ya kama murfin k’ofar zai fita yana fad’in “An gama.”

Fita yayi su kuma suka tayar da motar suka sake komawa wannan gidan…

Kuyi hak’uri masoya

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:21 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 5锔忊儯2锔忊儯

Police sun je garage d’in daya fad’a musu kuma haka abun yake, amma babu matasan biyu da suke nema, fuskokinsu kad’ai suka iya gani suka bar wurin dan sake zurfafa bincike har su gano su.


Ba laifi yayi aikin da aka saka shi yanda ya dace, dan lokaci zuwa lokaci ya kan turo musu da sak’on motar data shiga kampanin ko ta fita, a k’arshe sunyi nasarar sanin motar Malik data shiga kampanin kuma ya d’auki kusan awa d’aya kafin ya bar wurin, ta haka su fahimci kampanin ma na waye? Kabeer! Baiyi mamaki ba sai ma jin dad’in yanzu zai samu hujjar tagayyara shi, jinjina kai kawai yayi tare da cin burin saiya gano inda take nan ba da jimawa ba.

Tattaunawa kan lamarin yasa ya manta da Farha, sanda dare ya tsala kuma shaf ya manta wai tana garin ma sai kawai ya nufi gidan Richard, har yayi wanka ya fito d’aure da towel ta gorar ruwa yana sha sunan Farha ya zo mishi. Da k’arfi yace “Oh my God! Farha.”

Da sauri ya nufi kan gado ya d’auki wandonsa ya ciro wayarsa a aljihu ya shiga neman lambarta, kamar dama jira ake kam tana ringing d’aya ko na biyu ba tayi ba aka d’auka, cikin muryar kuka da tausayi tace “Yaya Salahadeen kana ina ne? Dan Allah ka zo na ganka ko naji sauk’i a raina, tunda ka fita da safe baka sake dawowa, ka barni cikin mutanen da ban san su ba basu sanni ba, gashi bamu san halin da Sarah take ciki ba kowa anan hankalinsa tashe yake.”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke cike da tausayinta, saida ya kwantar da murya sosai yace “Kiyi hak’uri Farhanatu, mun shiga tashin hankali ne sosai na b’atan Sarah, inda nake yanzu ba zan iya zuwa wajenki ba, dare yayi yanzu jami’an tsaro ne ta ko ina, kana fita zaka iya zama abun zarginsu da tuhuma, kiyi hak’uri kinji ki kwanta, na miki alk’awarin kafin ki bud’a idonki zan kasance a gefenki, kinji?”

A hankali ta sauke numfashi cikin samun nutsuwa tace “Shikenan yaya Salahadeen, ka kula da kanka.”

Saida ya jinjina kai kamar yana gabanta sannan yace “Insha Allah, ke ma ki kula min da kanki sosai kinji.”

Da haka sukayi sallama, zai ajiye wayar ya lura da wani kallon iskanci da Richard ke masa, had’e fuska yayi yace “Miye?”

Dariya yayi yana fad’in “Kana matashi da kai amma ka ajiye mata biyu, kaji dad’inka fa.”

Tab’e baki yayi yace “Kuma nasha azaba ba.”

Cikin rik’e dariya Richard yace “Gata kuwa mu ma muna sha azabar.”

Tsaki yayi yana wurga masa harara, haka sukayi shirin bacci suna ci gaba da tattauna al’amarin da kuma yanda zasu b’ullowa abun. Lafiya lau suka kwanta bacci bayan yasha gwagwarmaya sosai kafin ya samu ya d’aukeshi, bai ga komai ba ko da abunda zai zama makama a gare shi, sautinta kawai yaji sauti mai k’arfin gaske, siririyar muryarta ta daki dodon kunnensa ta ratsa b’argon jikinsa har ta shiga duk wata mahuda gashin dake jikinsa, kamar a wurin dake amsakuwa ne hakan yasa muryarta fita sosai kamar a lasifika yayin da ta ambaci sunan ” Slahadeeeeeeeen!!!”

Fiegigit ya tashi zaune da k’arfi yana kakkafe da idonshi, waigawa yayi ya ga Richard akan kujera dan cewa yayi ba zai kwana da k’ato ba haka kawai bayan ya saba bacci da matanshi a gefenshi, duk tsigan jikinshi yaji ta tashi yayin da yake sake nanata abinda yaji a mafarkinsa, idan fa sun kasheta? Wannan tambayar da zuciyarshi ta amtayo mishi ce ta haddasa mishi wani mummunan fad’uwar gaba, da sauri ya dafe k’irjinshi yana sunkuyar da kai da fad’in “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un.”

A hankali ya sauka daga kan gadon ya sulale k’asa, zuciyarshi da yaji na ta bugawa da sauri kamar zata fito ya dafe gurin, bud’e bakinshi yayi dan ya samu shark’ar iskan da zai numfasa, hannu yasa ya dafe kanshi sosai da yaji ya fara sara mishi, take idonshi suka d’auki launin ja sosai, girgiza kai ya fara yi yana fad’in “A’a, bata mutu ba, ba zasu iya kasheta ba, wallahi bata mutu ba, na tabbata ma basu mata komai ba, zan gano su, zan ganosu insha…”

Dafashi da akayi ne yasa yayi saurin kallon Richard da maganarshi ta bata mutu ba ta tashe shi, cikin kulawa yace “Kana nufin kasheta sukayi?”

Da sauri ya girgiza masa kai yace “Bata mutu ba, zuciyata ce ke raya min sun kasheta, amma kuma tunani na yana fad’in min bata mutu ba, ba zata mutu yanzu ba Richard, zan samo ta da yardar Allah.”

Bubbuga kafad’arshi yayi yace “Ka mata addu’a to, zata kasance cikin k’oshin lafiya.”

Kallonshi yayi kamar yanzu ne ya fara ganinshi sai kawai ya mik’e da sauri ya shiga toilet, ba jimawa ya fito ya d’auro alwala, kayanshi ya saka ya kalli alk’ibla akan carpet d’in ya kabbara sallah. Tun Richard na kallonshi yana k’idayawa har bacci ya sure shi daga nan ya sure shi bai sani ba.

Bai rintsa ba a daren nan bai kuma gushe ba yana addu’a da neman tsarin Allah ya kareta daga sharrin duk wani mai sharri, har lokacin sallah asuba yayi raka’atanil fijri yayi sallah farilla, azkhar yayi tare da tasbihi tahlili da takbiri ya kuma d’ora da salatin annabi Muhammad (S.A.W), yana idawa ya tashi ya shirya cikin gaggawa, daddab’a Richard yayi ya farka, gyara zamanshi yayi yana danna wuyanshi daya mishi ciwo saboda kwancin da yayi yace “Yane?”

Saida ya d’auki makullin mota da wayarshi yace “Zan je na ga Farha, ka tabbatar na sameka can gidan kafin naje.”

Hararanshi yayi yana turo baki yace “Salah ka barni nayi bacci na more mana, zuwa anjima saina je can d’in.”

K’afa yasa ya harbeshi yana fad’in “Baccin k’aniyarka, malam tashi kafin ranka ya mugun b’ace.”

Juyawa yayi zai fita yana girgiza kai yana jin yanda yake dariya yana fad’in “Munafiki kawai, da kana sonta kake zazzare mata ido idan tana gabanka, yanzu kuma bata nan ka tashi hankalin kowa dake k’asar nan, idan muka ganta da kaina zan had’ata da lauya a matsa maka lamba saika saketa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button