NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Wani banzan kallo ya masa yace “Nine ma zan fad’a maka?”

D’auke kanshi yayi ya mayar kan wayar, da yake babu wani kwad’on tsaron k’ofa a sauk’ak’e ya shica kai tsaye cikin wayar, a daidai tana cikin manhajar sada zumunta ta yane馃榿 (WhatsApp) a kuma kan lambar Sajida, a hankali ya bi sak’on da kallo wanda ta tura mata cewa “Yanzu haka ina hanya zan je garinku na ga yan uwa na, yaushe zaki zo ke?”

Ta bata amsa da “Nima yau na samu hutu, yanzu haka ina shirin tafiya da zan nemi visar jibi ne, amma tunda zaki je bari na nemi ta gobe insha Allah.”

Ta fara rubuta “Ok sister, sai…” Bata k’arasa bane abun nan ya faru hankalinta duk ya watse bata tura ba, dafe kanshi yayi da hannu d’aya yana girgiza kai, juyowa yayi ya kalli Insp. d’in yace “Yanzu me ye abunyi?”

Saida ya dafe k’ugu d’aya da hannu yace “Abun baiyi kama da kidnapping na k’ananan yan ta’addan da muka sani ba, but koma miye nufinsu akanta nasan zasu kira waya su fad’i abinda suke buk’ata, dan a sanina da miss Sarah…”

Wani irin kallo Salahadeen ya mishi yace “Point of the correction, not miss Sarah, mrs Slahadeen Ibrahim Auta, understand?”

D’an dafe goshi yayi yana zaro ido yace “Oh sorry, a sanin dana wa mrs Slahadeen ba ma’abociyar yawo da kadarori masu tsada bane, ma’ana d’an kunnenta zuwa sark’a da agogo, da tana sakawa ne sai muce zasu rabata dasu ne su saketa, amma na tabbata zasu kira wani na ta dan su fad’i abinda suke so.”

Wani iska ya furzo yana kallonshi yace “Kenan kana so ka ce baku samu komai ba?”

Wani kallo Insp. d’in ya masa ya nuna shi da yatsa yace “Who are you?”

Kai tsaye yace mishi “Salahadeen, mijinta.”

D’aga gira yayi sama yana k’are masa kallo, saidai baiga wata makusa da zata zama mafakar da zata iya jawo masa raini ko k’ask’anci cikin zama mijin had’add’iyar yarinya kamar Sarah ba, shigarshi yanayinshi harshenshi duk a zahiri sun bayyana shi a matsayin bature ne kuma wayayye, haka ma suturarshi bata nuna talauci ba dan duk da k’ananan kaya ne jikinshi irin na gayun zamani, amma dai daka gani kasan ba wai masu farashi mai sauk’i bane, dan haka ya d’auke kai daga gareshi yace “Sorry yallab’ai, idan kana son sanin wata masaniya ka same mu a office.”

Zai juya dan barin wurin wata mace sanye da kayan police ta tsaya gabanshi tana nuna mishi wasu takardu da fad’in “Yallab’ai kamar yanda kace mun bincika a duka erea nan da kamarorin tsaron dage wajen, a cctv cam茅ra dake shagon mai coffee can muka samu ganin motar, wannan ita ce lambar da muka samu ta motar data fito mana da kyau.”

Salahadeen da duk yake jin me ya faru kallonsu yayi ya kuma juya ya kalli shagon mai coffeen da tace, juyawa yayi a sukwane ya tunkari shagon, yana zuwa kai tsaye cikin ya shiga, wanda ya gani ya tabbatar masa shine mai shagon, kai tsaye wurinshi ya nufa suka gaisa, ba b’ata lokaci yace “Ni d’aya ne daga cikin jami’an dake bincike akan b’atan mrs Slahadeen, abokan aikina yanzu sun duba cctv kamaranku, shin zan iya ganin n’aurar taku?”

Shi dai kallonshi yayi da d’an tunanin shi bai iya nuna katin shaida ko bajo bane na aiki ko me? Tab’e baki yayi ya bud’e mishi yar gajeruwar k’ofar yana fad’in “Shigo tanan yallab’ai.”

Bin bayanshi yayi suka shiga, zaune yayi akan kujerar inda ya sake nuna mishi abinda suma ya nuna musu, da sauri ya dafe goshi ya mik’e tsaye daga sunkuyawar da yayi yace “Jar bala’i, ku kuma.”

Cije leb’e yayi yana murmushi tare da yin k’wafa ciki ciki, da sauri ya juya ya fita yana lalubar wayarshi ko ta kan mai shagon bai bi ba, ya jima yana waya kafin ya isa gare su ya samu Insp. d’in suna shirin barin wurin, da sauri yace “Sir, ina da masaniya akan lambar motar nan.”

Tsayawa yayi yana kallonshi yace “Me ka sani?”

Kai tsaye yace “In ban manta ba kamar lambar motar d’aya ne daga cikin motocin Great Garage.”

Da sauri ya ciro biro a gaban rigarshi da wani d’an k’aramin littafi yace “Bani address d’in.” Tsaf ya dage ya fad’a mishi komai kafin su tayar da motarsu, shima wata wayar ya sake yi tare da shiga motarshi ya bar wurin.

Kai tsaye wani tsohon gida ne ya wuce wanda ba zaka tab’a tunanin mutum zai iya shiga ciki ba, paka mota yayi ya shiga cikin takon k’asaita da isa, bugu biyu yayi aka bud’e k’ofar ya shiga, kalle kalle ya shiga yi yana neman wanda ya bud’e masa k’ofar, a saman kanshi ya hangeshi mak’ale da k’ofar, juya bayanshi yayi cikin k’warewa da sabo ya biyo bangon sululu ya diro k’asa, saurayi ne cikin bak’ak’en kaya da hular fuska amma ya d’ageta sama, dafa kafad’ar shi Salahadeen yayi yana murmushi dan yasan indai L茅onard ne yafi da haka, ko biri nan ya ganshi ya shafa mishi lafiya, kallonshi yayi yace “Ya ake ciki? Sun ce wani abu?”

Jinjina masa kai yayi yace “Kamar yanda ka ce haka akayi, sun tabbatar da sune suka aikata, amma sun ce basu san komai ba bayan umarnin da aka basu su kaita gidan madara.”

Murmushin gefen labb’a yayi yace “Maganar banza ce, za suyi magana ne yanzu.”

Suna ida shiga ciki smatasa ne a k’alla guda takwas wasu zaune wasu tsaye duk cikin bak’ak’en kaya, daka gansu kasan marasa jin magana ne, sai biyu dake zaune kan kujera an d’auresu tamau duk fuskarsu tayi jina-jina alamar sun sha duka sun fara fita a hayyacinsu, sai kuma Richard gefe d’aya zaune yana shan sigari. Ganin Salahadeen d’in k’arara ya bayyanar da mamakin matasan dan basu san yana garin nan ba, hakan yasa tsoro ya k’ara fitowa a fuskokinsu, duk da sun sa ba mugu bane dake iya cin zalin ba tare da hakk’i ba, sai dai sun san sun tsokano tsuliyar dodo tunda har suka ganshi gasu gashi, wanda ko zamanin da yake tak’adarin basu fiya had’uwa dashi ba sai dai ya umarce su ta waya, idan ma an had’u to sai dai wajen cin abinci ko wajen shak’atawa ko casu.

Tsaye yayi a kansu yana k’are musu kallo, wani murmushi ya shiga dokawa kamar wanda suka mishi albishir mai dad’i, saida ya d’anyi k’asa da kanshi ya shak’i numfashi mai kama da jan majina yace “Kunsan wani karin magana a yarena da ake fad’a wanda yayi daidai da abinda kuka aikata?”

Duk zuba mishi ido sukayi suna kallo, kallon fuskokinsu yayi yace “Cuta ce ta dawo cuta, ko kuma na ce sata ku kayi a gidan b’arawo, nasan kunsan dole zata zama bashi ce.”

Gyara tsayuwa yayi yace “Amma kunsan me ya bani mamaki?” Su dai ido kawai suka zuba mishi suna kallo, d’orawa yayi da “Yanda akayi kuka manta da horarwata, kun manta yanda na sanar daku tsarin aiki, kun manta na fad’a muku duk wanda zaku ma aiki ba ni ba to ku tabbatar kunsan waye shi kuma akan wa ya saku aikin, shin yanzu kunsan rashin bincikenku me ya jawo? Kunsan wa kuka sace d’azu?”

Dukansu ne suka girgiza kai sai d’ayan daya d’ora da cewa “Salah, karka cutar damu mun rok’eka, basu san komai ba ta waya kawai ake umartarmu.”

Kujerar dake bayanshi ya jawo ya zauna ya rumgume hannaye yana kallonsu sosai yace “Kunsan wa kuka sace yau?”

Cikin wofantar da lamarin d’aya yace “Sarah Shakoor, magajiyar trilliyoyin kud’i da kadarori.”

Wani murmushin shak’iyanci yayi ya kalli wanda yayi maganar yace “Hakane, Sarah ‘yar Shakoor ba, to amma kunsan waye mijinta?”

Kallon juna sukayi a tare sai kuma suka kalleshi d’aya yace “A cikin masaniyar da aka bamu kanta ba’a fad’a mana tana da aure ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button