SALAHADEEN COMPLETE NOVEL
Yanzu kam Zeid da Mustafa a gaba suka zauna, sai matan a baya su hud’u babu matsi bare k’orafi, banda tsakin Farha dana Iffa babu abinda kake ji da maganarsu k’asa k’asa, babu wanda ya kulasu dai tafiya kawai ake har aka isa gidan.
Sab’anin yanda kowa yayi tunanin zata ruga ta shiga sai ta tsaya ita ce ma k’arshen shiga, sanda Mama ke ta farin cikin ganinsu ta shigo jiki a sanyaye, mama na ganinta ta bud’e mata hannaye tana fad’in “Iyeeh! Saratu na ta dawo, yarinyata tasha k’auye ko?”
Cikin matsanancin jin dad’i ta k’arasa da sauri ta rumgume Maman tana kwantar da kanta a kafad’ar Mama tana fad’in “Nayi kewarki sosai Mamie.”
Cikin dariya tace “Nima haka, to ya k’auyen?”
Turo baki tayi amma ba tace komai ba, kallon fuskarta tayi sai kuma ta d’ora hannu kan wani shati data gani kamar idan jinjiri ya yagi kanshi tace “Wannan fa miye? Miye ji miki a fuska?”
Zuciyarta ce ta zo wuya kawai ta fashe da kuka ta ruga a guje ta shige d’aki, kallonsu Mama tayi kallona tuhuma tace “Me kuka mata? Me ya sata kuka?”
Gogon kam sai wani d’aga gira da yayi sama ya nufi nasu d’akin ya barsu, Iffa ma wucewa tayi d’akinsu sai Zeid ne yace “To ban sani ba dai, amma ki tambaye su.”
Shima nasu d’akin ya nufa tare da Tafa haka ma Mamuh, daga ita sai Farha ne suka rage wacce suke kallon juna, a hankali mama tace “Farhanatu me aka mata?”
Gyara tsayuwa tayi sosai tace “Mama, shin yaya Salah ba auren wucen gadi bane aka musu shi da yarinyar nan?”
Da mamakin tambayarta tace “Eh hakane, lafiya?”
Cike da son amayar da abinda ke ranta tace “To dan Allah Mama kisa ya saketa, dan ni aurenshi da ita a kowace fitowar rana sake shiga tashin hankali nake, na gagara samun nutsuwa bare farin ciki, na tsani yarinyar nan Mama saboda ina ji a jikina kamar zata iya k’wace min miji, dan Allah kisa ya saketa in kuma kinfi sonta a kaina kamar yanda kike nunawa sai ni kisa ya sake ni.”
Ko da ta gama fad’a ta wuce nasu d’akin ita ma tana jujjuya baki, duk abinda ya faru akan idonshi da kuma kunnenshi, dan haka tana shiga ya bita da wani kallo na mamaki da jin lallai ta kai mak’ura, k’ala bai ce mata ba sai kayanshi daya cire ya fito ya shiga wanka.
Mama na shiga d’aki ta same ta uwar d’aki kan gadonta da wani kwali a gabanta tana duba takardu, zaune tayi tana kallonta tace “Sarah ba zaki fad’a min me aka miki ba?”
A tsanake ta kalli Mama tace “Mamie tafiya zanyi? Zaki taho tare dani k’asata?”
Wata dariya tayi tace “Wasa kike ko?”
Girgiza kai tayi alamar a’a ta ci gaba da duba takardun, rik’e hannunta tayi tace “Ke wai da gaske kike?”
Jinjina mata kai tayi a harshen french tace “Tafiya zanyi Mamie, akwai abubuwa da dama dake jirana, zan tafi na barku cikin kwanciyar hankalin dana same ku.”
Bandir hud’u ta d’auko na d’aurin dolor amuruka ta damk’awa Mama ga hannu tana fad’in “Ki rik’e wannan Mamie, kyauta ce daga gareni, abisa kyautatawarki gareni bansan me zan iya baki ba, a yanzu dai wannan kawai nake da, amma na miki alk’awarin dawowa wata rana saboda ke.”
Sakar mata kud’in tayi tana fad’in “A’a bana so, Sarah me aka miki da zaisa ki tafi da gaggawa haka? Shin har komai ya daidaita ne da zaki tafi.”
Kalmar daidaitar al’amura da ta fahimta ne yasa ta d’aga mata kai tace “Eh mamie.”
Sake damka mata kud’in tayi tace “Na rok’eki ki rik’e wannan, idan ba haka ba zan ji ba dad’i sosai.”
Girgiza kai ta sake tana fad’in “Sarah ina zan kai kud’i haka masu yawa da bansan ko na ina bane? Duk abinda na miki na miki dan Allah ne ba dan ki biyani ba.”
Murmushi tayi tana rik’e kud’in a hannunta tace “Shikenan zan rik’e a hannuna, amma zan fad’a miki wani abu dana tabbatar zaifi kud’in nan faranta miki rai.”
Kasancewar a harshe biyu tayi maganar yasa bata gane ba sai kallonta da tayi, a hankali cikin karkatattar hausarta tace “Ina so…zan..musulunta.”
Da farin ciki sosai ta jawota ta rumgume tana fad’in “Kai Alhamdulillah masha Allah, Allah abun godiya, wannan labari ne mai dad’i Saratu.”
D’agowa tayi suka kalli juna tace “Ya zanyi yanzu idan zan shiga?”
Da sauri tace “Abu mai sauk’i, yanzu zan fad’i wasu kalmomi ke ma saiki fad’i duk abinda na fad’a.”
Daki daki ta dinga fad’a mata kalmar tana nanatawa har suka gama, kabbara tayi bayan ta gama fad’a wanda ita ma saida ta sake fad’a, nan mama ta rik’e ta shiga mata jawabin abinda ya hau kanta dallah dallah.
Sanda ya same su a d’akin har yayi shirin fita, fad’a masa tayi amma babu alamar farin ciki ko jin dad’in al’amarin a tare dashi, sai dai fa a zuciyarshi yafi kowa murna da faruwar hakan, fita yayi ya barsu ba tare da idonsu sun sark’e wuri d’aya ba. Fitowa sukayi Mama ta shiga koya mata wankan daya zama wajibi ta fara yi yanzun kafin sauran abubuwa su biyu baya.
Tabbas taji wani haske mai haskakawa marar k’una da kuma nagarta ya shigo rayuwarya, taji ta k’ara son abun da gaba d’aya zuciyarta sanda Mama ta sake fayyace mata shi, ta kuma d’auri niyyar rik’onshi da hannu bibbiyu ko da zata rasa ranta, taji a shirye take data rasa komai inda akan addinin nata ne. Ta b’angare d’aya kuma ta wayarta da bata cika kallonta ba ta shiga manhajar dan siyan ticket d’in jirgi, abun bai bata wahala ba tunda dama komai a kammale yake, ta kuma samu jirgin da zai tashi k’arfe d’ayan daren yau, saida ta gama komai na shirin tafiya zuwa k’arfe biyu ya shigo ya ci abinci, d’aki ta shiga ta fito daga yar k’aramar poshet d’in hannunta sai wayarta, doguwar rigar daya siya mata ce jikinta bak’a sai bak’in kallabin Mamuh data yane kanta dashi sak balarabiya.
Tsaye tayi kusansu shi da mama tace “Zaka iya sauke ni filin jirgi?”
Wani kallo ya mata a ranshi ya furta “Jarabar Abhi ta motsa ko?”
A fili kuma d’auke kanshi yayi kamar bai ji ba, d’aga kafad’a tayi ita ma alamar matsalarshi ce ta kalli Mama, sake rumgume Mama tayi tana fad’in “Mamie zanyi kewarki sosai, amma ki sani zan dawo saboda ke.”
D’agowa tayi tana kallonta tace “Nagode sosai akan duk abinda kika min.”
Matsawa tayi inda Mamuh ke zaune tana karatu ta sunkuya ta rumgumeta tana fad’in “Zanyi kewarki sister, ke ta musamman ce kina da kirki.”
D’agowa tayi suka kalli juna tace “Zan dawo saboda ke wata rana, ki kula da kanki.”
Jinjina kai Mamuh tayi tace “Ke ma ki kula da kanki, amma ni banji dad’i ba da zaki tafi haka kwatsam.”
Murmushi ta mata tace “Sorry, i will come back insha Allah for u and Mamie.”
Murmushi ta mata ita ma ta bita da kallo tana nufa wajen da su Mama ke tsaye, kallonshi tayi tace “And u mr., thank u so much for evrything do this to me.”
Mayar da jakarta tayi a hannun hagu ta rik’e ta bashi hannun dama da nufin su gaisa, kallonta Mama tayi ta nunata da yatsa tace “Duk da mijinki ne shi amma dan ki kiyaye gaba zan fad’a miki haka, ki sani a matsayinki na mace haramun ne ki gaisa da namijin da ba muharraminki, ko d’an uwanki ne indai har ya balaga yana da kyau ki kiyaye saboda gujewa fad’awa tarkon shaid’an, ko kin koma k’asarki Sarah karki bari kiyi arhar da har zaki iya had’a hannunki da kowane jaki alade, kinji ko?”
Kaso sittin na maganganun Mama ta fahimce su dan haka ta jinjina mata kai tare da fad’in “Insha Allah Mamie.”
A hankali ta kalli Salahadeen tace “Ka saketa ne?”