NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Bai bari ta k’arasa ba ya figo kofin hannunta ya juye ruwan ciki a fuskar Sarah, bata zabura ba kamar yanda ba da k’arfi ta farfad’o ba, ajiyarzuciya duk suka sauke tare da k’ura mata ido.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:09 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               2锔忊儯1锔忊儯

Zaune ta tashi tana kallonsu duka, kallon Salahadeen tayi tace “Me yasa haka ke faruwa dani?”

Kafin ya bata amsa tayi k’asa da kanta tana kuka marar sauti tace “Ina so na mutu, ina so na mutu kamar mahaifina.”

Mamuh ce tayi saurin matsowa kusanta tana share mata jinin daya fito a hancinta tana fad’in “Ki daina fad’in haka aunty Sarah, kowane tsanani yana tare da sauk’i, insha Allahu komai zai wuce kamar ba ayi ba.”

Kallonta tayi tace “Ina jin kaina na min ciwo, duk bana jin dad’i.”

Mik’ewa yayi ya fita daga d’akin, Mamuh kuwa da ta ci gaba da shafa kanta bacci ne ya sauke d’auketa daga nan.

Saida safe ya shigo gidan da abun karin daya siyo mata wanda yasan zata iya ci, lokacin su Mamuh har sun tafi makaranta sai Farha dake d’akinta kwance, d’akin ya wuce inda ya zauna yana k’arewa kyakyawar fuskarta kallo, tausayinta yaji ya sake lullub’eshi daya tuna abinda malaminsa ya fad’a masa a game da ita, a hankali ya shiga tuna kalamanshi da yace doleya tashi tsaye ya dage da addu’a wajen ganin ya kare rayuwarta daga had’ari, shi daya fara dole shine zai k’arasa wasan, ajiyar zuciya ya sauke dan shi fa yau d’in nan yayi niyyar kaita Niamey ta koma garinsu, tun fitar da yayi jiya ya ciro ticket d’in, ya zaiyi kenan? Ya jima zaune wurin yana kallon yanda take sauke numfashi kafin ya fita daga d’akin.

Yana shiga Farha kuma da d’aurin k’irji tana shafa mai, ta bayanta ya rumgumeta yana lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya, kiciniyar raba kanta dashi ta shiga yi, sake matseta yayiya bud’a ido yana kallon fuskarta ta madubi yace “Menene?”

Turo baki tayi tare da fizge jikinta tayi baya, kallonta yayi ya sake cewa “Farha miye? Meye matsalarki?”

Juyowa tayi ta kalleshi tace “Meye matsalata? Humm.” Ta fad’a tana sake juyawa neman kayan da zata saka, cikin muryar da babu wasa yace “Farha kinfi kowa sanin ina son zama lafiya lau dake ko? To kar kiyi anfani da wasiyyar mahaifina ki ce zaki mayar dani shashasha.”

Juyowa tayi da k’arfi tace “Wai ni ce ma mai laifi yaya, ka manta me ya faru ne jiya? Tunda ka dawo tare da yarinyar can ka canza min kake nuna min banbanci, sannan jiya har kake fad’a min zaka je ka kwana tare da ita, shine ma har zaka nuna babu abinda ka min.”

Kallonta ya ci gaba dayi yana so yayi magana amma ya kasa, tsaki kawai yayi ya nufi wajen kayanshi ya cire ya saka na wanka ya fita, sake kumburowa tayi tace “Lallai, wato yanzu baka da lokaci na ma.”

Har yayi wanka ya shirya ya fita bai sake kulata ba, sai lokacin ne ma Sarah ta farka daga baccinta, kai tsaye wanke baki ta fara dashi da wanka ta fito, shiryawa tayi cikin riga da wando ta zauna karyawa, sosai taji dad’in sandwich d’in daya siyo mata, tana idawa ta gyara zamanta tana jiran tsammanin zuwanshi taji ya maganar tafiyar da kuma tsumayin Mamie.

Babu shi babu alamar shi har taji motsin Farha a farfajiyar gidan ta fara aiki, bata yi tunanin fita ba dan bata son had’uwa da ta, amma bata tsira ba dan saida Farha ta lek’o d’akin ta mata alama da hannu cewa ta zo, tashi tayi gabanta na tsananta fad’uwa ta fita, takalmi ta saka ta bi bayanta har ta zauna kan kujera, juyowa tayi ta kalleta ta nuna mata robar yakuwa da allayahun da take yankawa tace mata ta yanka mata.

Bata mata musu ba tunda taga babu kowa gidan, zaune tayi a kan kujera ita ma ta d’auki yakuwa da d’aya d’aya tana yankawa, kallonta tayi taja tsaki ganin tana yankansu da guda guda, ko da taga ta kammala a hakan saita mik’a mata tafarnuwa ta b’are mata, a yanda tasan ana b’arewa haka tayi amma saita dinga karyewa har tana shigewa akaifarta, sanda ta juyo ta tara mata hannu ta bata ne taga bata tara komai ba, wata tsawa ta mata da fad’in “Ke sakaryar ina ce? B’are tafarnuwar ne baki iya ba dan kina musaka? Koda yake ance yar gata ce ke ko baki iya wahala ba.”

Fiage sauran tafarnuwar tayi ta turo mata turmi gabanta ta zuba gishiri da barkono tace ta daka, cikin satar kallonta ta k’ara jawo turmin gabanta ta d’aga tab’arya ta aje da k’arfi hakan yasa turmin bayar da sauti marar dad’i.

Kallonta tayi ta nuna ta da yatsa tace “Allah saiki dakashi, banza mai suffar aljanu.”

K’arfi tasa sosai ta fara kaiwa turmin bugu ta ko ina, dandanan hannayenta sukayi sanyi ta gaji ta ji ba zata iya ba, haka ta dage tayi ta dakawa amma babu abinda yayi daga alamar rusuna.

Atshawa ta fara yi inda majina ta fara mata zuba saboda yaji, haka ta rufe hancinta da hannu ta ci gaba da dakanta da k’arfinta kam.

Mustafa ne ya shigo da sallama ya nufi d’akinsu, juyawa Sarah tayi tana kallonshi sai Farha data amsa mishi, da kallo ya bisu hakan yasa ya dawo wajensu yana fad’in “Amaryar yaya Salah daka ne haka?”

Wata muguwar harara Farha ta wurga masa tare da tsaki tana fad’in “Aikin banza.”

Had’e fuska yayi yace “Ke ina wasa dake ne?”

K’wafa kawai yayi tare da durk’usawa gaban Sarah ya karb’i tab’aryar yana dariya yana cewa “To ke mutuniyar wannan daka haka ai ko ni dake namiji na fiki iyawa.”

Ko da taga ya fara dakawa saita jingina a kujerar tana sauke ajiyar zuciya da yarfa hannayenta da take jin sun sage mata, duk sanda tab’aryar tayi sama da k’asa haka tale binta da kallo, murmushi tayi tare da saurin karb’ewa tana fad’in “Na gani zan iya.”

Dafe turmin tayi da hannu kamar yanda ta ga yayi da hannunshi d’aya, d’ayan kuma ta fara dakan dashi, tayi d’aya biyu ana uku ta d’ora tab’aryar kan yatsunta biyu da suka fi kusa, wata azababbiyar k’ara ta saki tare da sakin tab’aryar ta mik’e tsaye tana juayawa tana yarfa hannu, cikin kulawa Mustafa ya mik’e yana mata sannu sannu, d’ora hannun tayi saman kai tana jujjuyawa cikin azaba, suna had’a ido da Farha taga sai dariya take mata tana fad’in “Allah ya k’ara, banza kawai da bata iya komai ba.”

Dakewa tayi sosai tare da yin juriya ta kalli Mustafa da taga ya nuna mata damuwarshi sosai tayi murmushi, yatsun tasa cikin baki tana tsotsasu tare da yin k’una bak’in wake ta sake komawa ta zauna ta d’auki tab’aryar. Tsayar da ita yayi yace “Ko aje mana ki bar dakan zata ida.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button