NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Za muji me yayi a gaba.


Tunda suka fita ya sake hannunta suka ci gaba da tafiya a hankali, tunani ne fal zuciyarshi kan abubuwa da sama, haka ita ma tunanin take na rayuwarta da kuma yanayin data samu kanta a ciki, idonta na kan hanya tana kale kale amma sam hankalinta ba nan yake ba, duk yanda ta rinjayar da mutane zuwa ga kallonta sam bata kulasu ba.

Wata gona suka isa inda yaja ya tsaya a bakin wurin yana kallonta, ganin sai tafiya take yasa shi cewa “Mun zo gurin.”

Da sauri ta juyo tana kallonshi ta tsaya, dawowa tayi ta kalli gonar, an share an gyara da alama an saka taki saukan ruwa ake jira, sosai ta dage tana kallon gonannkin dake wurin, ba tare data kalleshi ba tace “Gonar nan da zasu samu kulawa da taimakon kayan aiki na zamani za’a samu anfani sosai.”

Kallonta yayi amma da yaga bashi take kallo ba saiya d’auke kanshi shima, da hannu ta dinga nuna mishi tana fad’in “Kaga idan da ni na samu wajen nan me zanyi dashi?”

Murmushi yayi tare da zuba hannayenshi aljihu yana fad’in “An saba juya dala ba dole har kin hango ribar da zaki iya irga a wurin ai.”

Dariya tayi ta kalleshi da kyau tace “Ba haka bane, tunda kaine mai gonar zan iya baka shawara to? Saboda bana so ka d’auka ina son wurin ne.”

A tak’aice ya kalleta da alamar ina jinki, tab’e baki tayi sannan ta juya tana nuna mishi daki daki tana cewa “Da fari zan fara duba a gurin nan wani yanayi yafi yawa, sanyi ko zafi? Rana ko inuwa? Iska ko rashin sa? Idan na samu amsar nan shine zai bani tabbacin abinda zanfi cin moriyarshi, misali idan shinkafa zata fi karb’ar wurin saina nomata, na kawo injina masu kyau da inganci da zanyi aikin shinkafata dasu, daga nan kuma saina gyara a madadin girman gonar saina bud’a k’aramin campganien da za’a dinga sarrafa shinkafar, kaga kenan daga gona sai kampanin taceta sai buhu sai kuma kasuwa, hakan zai bada kala fa.”

Tunda ta fara magana yake kallon fuskarta da bakinta, yanda take motsashi da yanda take da fuskarta da hannayenta ma wajen mishi kwatance kai kasan kwararrar yar kasuwa ce, da fari tunaninshi na siyar da gonar ne, amma yanzu a take sai yaji son gonar yake da kuma burin bunk’asata kamar yanda take so ko ta bashi shawara, duk da ba shi kad’ai bane mamallakin gonar, amma yasan ba zai samu matsala ba idan har yace ga abinda yake son yi.

Wani murmushin ya sake sakar mata tare da rab’ata ya wuce yana girgiza kai, sake tab’e baki tayi ita dai ta bi bayanshi. Wata tafiyar suka sake yi ba mai nisa ba sosai suka isa wata k’ofa da aka zagaye ta da waya ta k’arfe, wanda suka samu zaune a k’ofar wurin suka gaisa cikin girmamawa kafin ya bud’e mishi k’ofar da makulli, ciki suka shiga tana binshi a baya, jardin ce wacce suka samu shuke shuke a ciki kama daga tumatur kabewa kabeji yakuwa dasu alayyahu da albasa, taji dad’in zuwa wurin sosai dan har juyawa take tana kallon wurin tana taba komai da hannu tana shinshinawa, sanda suka samu tumatur saida ta cira mai kyau yayi jajir, ta bud’a baki zata kai yayi saurin rik’e hannunta, kallon juna sukayi sai kuma ya saketa yasa hannu d’aya ya amshi tumatur d’in, nuna mata shi yayi yace “A addininmu wannan da zaki ci ba tare da sanin mai shi ba haram zaki ci, idan har bai yafe miki ba sanadiyarshi zaki iya shiga wutar jahanna ma.”

Zaro ido tayi tace “Yanzu ba zaka yafe min ba idan na ci?”

Lumshe ido yayi kawai ya rab’ata ya wuce, kusa da rijiyar dake akwai yaje ya d’ibi ruwa ya wanke shi ya dawo ya mik’a mata, karb’a tayi tare da kallon fuskarshi tace “Zan iya sha?”

Da ido ya mata alamar eh, saita bakinta tayi ta gatsa masa hak’ora, lumshe idonshi yayi tare da tambayar kanshi “Jarabar ta mecece wai Salahadeen? Ka d’auke idonka mana daga kanta.”

Har yayi shirin juyawa zasu fita kawai yaji ta matso daf dashi ta daduma tumatur d’in a bakinshi tana fad’in “Ci kaji ya nuna sosai wallahi sai dad’i.”

Rintse ido yayi tare da gumtse bakinshi, baya iya shan tumatur a haka, da a sandwich ne aka saka shi d’anyan shi zai iya amma ba haka ba, girgiza mata kai yayi tare da ja baya, kallonshi tayi a tsorace ta kalli tumatur d’in, ai kuwa saita sake matsawa daf dashi ba zato tasa hannu d’aya ta mishi cakulkuli a ciki.

Da sauri ya zille yayi baya yana sakin dariyar dolen da bai shirya mata ba yana fad’in “Kkkkee.”

Cikin dariyar ita ma tare da tusa mishi tumatur d’ina baki tace “Dame kake tunani, nasha ni kad’ai na mutu a nan ka binne gawata ko? To ba zan mutu ni kad’ai ba.”

Yanda ta matse tumatur d’in ta saka mishi a baki yasa duk dubararshi ta ciroshi saida dai ya ci wani ya had’e wani. Ganin ya duk’ar da kanshi zai zubar yasa ta saurin tara hannayenta biyu duka ya zubo a hannunta, da sauri ya kalleta sai yaga ta rintse ido ta shiga shafa tumatur d’in a fuskarta, waro ido yayi yana kallonta kawai kamar bashi motsi, saida ta idar ta bud’a ido tana fad’in “Ko ina ya samu?”

Kawai wani shauk’inta yaji ya d’ebeshi ya matsa daf da ita, bai tab’a jin irin haka akan mace ba har wanda ya gani a tsirara, yanda ya k’ureta da ido ka sai taji ta rasa kuzarinta dole ta sadda kanta k’asa, cikin taushin murya kuma k’asa k’asa sosai yace “Ba kya k’yamk’yami na ne? Daga bakina ya fito fa.”

Ba tare data had’a ido dashi ba tace “Haka kawai ne ban ji k’yamk’yamin ba akan ka.”

Shiru yayi bai ce da ita komai ba sai numfashi daya shiga sauke mata a fuska, jin shirun yayi yawa sai kawai ta d’ago kanta dan ganin yana ina? Cikin idonshi ta saukar da nata idon, kafin ta zame idonta saboda ba zata iya kallonshi ba duk wata kunyarshi taji ta rufe ta kawai taga ya saka yatsanshi yana yawo dashi akan fuskarta.

K’asa ta k’arayi da kanta cikin jin kunya tana d’an motsa bakinta tana so tace ya bari amma ta kasa, saida taji ya daina ta bud’a ido ta kalleshi, gani tayi ya juya ya zauna bakin rijiya, bak’in gilashi ya fito dashi ya danne idonshi dashi sannan ya fito da sigari ya kunna ya shiga sha a nutse. A hanjali ya d’an matsa tana k’are mishi kallo, alamu sun nuna ba wai d’an dad’i yake sha ba ko dan sabo, tayiwu kawai abun na zuwa masa ne.

Yanda shima yake kallonta ta cikin glashin ne yasa shi mik’o mata sigarin da mata alama da kai alamun zata sha ne? Da sauri ta girgiza kai tare da tab’e baki, d’an gyara tsayuwarta tayi ta jingina jikin biyar mangaron da tayi luf tana ci gaba da kallonshi, duk da ya rufe idonshi sai yaji ba zai juri yanda take kallon nan nasa ba, d’an k’asa yayi da gilashin tare da motsa bakinshi da k’yar yace “Miye?”

D’aga kafad’u tayi tana sake tab’e alamar ba komai, saida ya wurga mata harara ya mayar da gilashin yana sake kifata a baki ya zuka, da sauri kamar wacce aka tsikara tace “Me yasa ban tab’a gani kasha a gida ba? Kana tsoron Mamie ne?”

Ta cikin gilashin ya wurga mata wani kallo amma sam bata gani ba bare ta fahimta, jin baice komai ba ta sake cewa “To amma me yasa kake sha tunda kasan ba zasu ji dad’i ba? Ka daina mana ko dan farin cikinsu.”

Cikin jin haushi ya yarda sigarin tare da saka k’afa ya mitsiketa ya mik’e ya nufi hanyar fita, da sauri ta bi bayanshi suka fice daga wajen bayan ya sake wa wanda suka samu a bakin k’ofar wurin, a hankali suke tafiya ya zuba duka hannayenshi cikin aljihu yana kallon gabanshi, ita ma rawa take da hannayenta tana kallon ko ina na k’auyen, a hankali ta kalleshi tace “Mr. me yasa ba zakazauna anan ba?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button