NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Duk yanda Mamuh ta so ta ci abincin ta k’i ci, haka ta rabu da ita tunda ba d’ura mata za tayi ba, su dai har suka koma d’aki suka kwanta bai dawo gidan ba, Farha ma tayi shirin baccinta ta kwanta ta rufe d’akin daga ciki, dan ranta a b’ace yake kuma ita lasisi ne gareta na yin duk abinda ranta ke so a gidan, dan a gaban idonta akan kunnuwanta kafin rasuwar mahaifinsu yace “In har ya b’ata mata rai ko ya cutar da ita to bai yafe masa ba.” Da wannan take tunk’aho tasan dole ya bita sannu in yana son zama lafiya.

Dare yayi sosai ya dawo gidan, d’akin ya fara shiga ya samu duk sunyi bacci sai ita dake k’urya tana bacci da shashek’ar kuka, fita yayi ya koma d’akin ya shiga bubbugawa, daga ciki ta tambaya “Waye?”

Tambayarta dariya ta bashi, girgiza kai yayi yana godewa Allah daya yo shi namiji ya kuma zagaya mata a kewayenshi, kowace da salon nata cajin da take masa, a hankali ya amsa mata da “Mijinki ne.”

Daga ciki ta tab’e baki tace “Mijina dai? Ko kuma mijinta? Kaga malam kaje wajen wacce kafi so, ni me zan maka da ka zo nan?”

Rik’e k’ugu yayi ya shiga kallon k’ofar d’akin, cikin taushin murya yace “Amma ai nan ne d’akina ko? Ki bud’e k’ofar sai muyi magana Farhanatu.”

Cike da tsiwa tace “Ba zan bud’e ba wallahi sai gobe idan mama ta zo ta fad’a min zaman da nake a gidan nan, yau kaje ka kwana tare da amaryarka tunda ita kake so dama bani ba.”

“Farhaaaa.” Ya fad’a cikin muryar gargad’i, tab’e baki tayi ta juya ta koma kan gado tace “Idan ka gaji zaka tashi anan.”

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon k’ofar d’akin, jinjina kai yayi ya sake matsawa jikin k’ofar yace “Farha ki bud’e k’ofar nan mana, kinsan dai babu inda zan iya kwana idan ba nan ba ko? Me yasa kike son wulak’anta ni ne?”

Cikin d’aga murya tace “Ni daka wulak’anta ban san ciwon kaina bane kenan? Kuma kasan dai nan d’akina ne ba naka ba ko? Albarkaci na dama kake ci kake kwana anan, kasan da haka ko na tuna maka?”

Cikin marairaicewa yace “Na sani Farha, d’akinki ne nan wanda Abba ya mallaka miki, kuma yace ko da babu aure tsakaninmu ni ne zan bar gidan nan amma bake ba, sannan yace bai yarda na sake ki ba ko bayan babu ranshi, amma ki tausaya min mana ki bud’e min na shiga.”

Daga ciki tace “Wallahi kaji na rantse ba zan bud’e ba, karka b’atawa kanka lokaci fa.”

Jinjina kai yayi cikin jin haushi da k’osawa yace “Haka kika ce?”

“Eh.” Ta fad’a daga can, cikin gatsali yace “Shikenan, amma kinsan da d’akuna a gidan ba wannan ne kad’ai ba? Sannan ina da wata matar ma, kin tuna hakan? Saida safe.”

Ai kuwa juyawa yayi ya tunkari d’akin Mama…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:08 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               2锔忊儯0锔忊儯

Har ya kai k’ofar d’akin ya tsaya ya tambayi kanshi “To me zaije yayi? Me ya had’ashi da ita kuma da zai shiga wurinta yanzu?”

Tsaki kawai yayi ya canza akalar ta hanyar nufa d’akinsu Tafa (inji Sarah ba), a hankali ya shiga k’wank’wasa k’ofar amma shiru, ci gaba yayi da bubbugawa amma babu ko motsi. Sarah a lokacin tana zaune sai faman gyangyad’i take da shashek’ar kuka taji bugun k’ofar, a hankali ta shiga dube dube har ta sauko daga kan gadon, falo ta fito a hankali cikin sand’a danta dubawa waye, a hankali ta d’an lek’o kai cikin tsoro, tana ganin mutum tsaye kuma ba maman da take tunani ba sai kuwa ta juya da k’arfin tsiya tana fasa ihu da fad’in “B’arawo, b’arawo ku tashi.”

Taka k’afar Mamuh da tayi yasa ta tashi zunbur a tsorace tana murza k’afar, durk’usawa tayi kusan Mamuhn data d’aga kai tana kallonta ta shiga jijjiga kafad’arta tana nunamata k’ofa da fad’in “B’arawo a waje, me yasa baku rufe k’ofar ba?”

Kafin Mamuh tayi wani yunk’uri Salahadeen daya tuna rayuwarsa ta k’asar waje yayi wata surowa cikin d’akin, yana tozali da ita ya cakumi tsakiyar cikinta ta baya ya rumgumota a jikinshi, a lokaci d’aya yasa d’aya hannunshi ya rufe mata baki yayi uwar d’aki da ita.

Wutsil wutsil ta shiga yi da k’afafunta tana dukan hannunshi dake kan cikinta ya zagayeta, saida ya kaita kan gadon ya direta kad’ai, da wani irin sauri ta wuntsila ta k’arasa shigewa k’uryar gadon tana juyowa ta ga wanene, suna had’a ido ta gyara zamanta tare da furzo iska, cikin harare yace “Waye b’arawon?”

Saida ta harareshi ita ma tace “Kai mana, me yasa zaka tsaya kana bubbuga k’ofa yanzu a dare?”

Rik’e k’ugu yayi yace “Duk da na buga k’ofar kuma na zama b’arawo? Shi b’arawo dama yana bubbuga k’ofa ne?”

Had’e k’afafunta tayi ta tokaresu kan gadon tana turo baki kawai ba tace komai ba, juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya ya juyo yace “Ba bacci kike ba? Me ya tashe ki?”

Saida tayi kalar tausayi sosai cikin muryar kuka tace “Jana’izar Abhi na nake, ba kace ya mutu ba.”

Da k’arfi ya rintse ido dan sai yanzu ya tuna abinda ya faru d’azu, sam sai yaji ba dad’i daya gaya mata hakanen kai tsaye, bud’a ido yayi tare da d’an gutun tsaki na jin haushin kanshi. Tausayinta yaji sosai sai yaji fa duk shine mai alhakin wannan abun, a hankali ya matsa kusa da ita ya d’an muskuta ya zauna kan gadon, fuskantarta yayi sosai ya kalleta, yanda tayi kamar wata mage a lokacin sanyi yasa yaji gabanshi na wani irin dokawa da baisan dalili ba, duk sai yaji ya samu kanshi a yanayin da baya son ya dinga jin irinshi akan ‘ya mace.

Saida ya aro k’arfi da jarumta ya d’aga labb’ansa da k’yar yace “I am so sorry, i don’t mean to hut you, your father..i am so sorry.”

Yanda take kallonshi ne har ya gama maganar, kuka ne na gaske taji ya taho mata, sake had’e jikinta tayi kamar wacce ke jin sanyi ko tsoro ta had’a kanta da gwiwa ta shiga kuka da gaskiyarta. Kallonta ya shiga yi har ga Allah sai yake jin kamar tana katso zuciyarshi tana jefarwa, kamar tana ciccirata ne tana wofantar mishi da ita, sam baya jin dad’in kukan, kuma bai tab’a jin haka akan kowa ba sai yau d’in nan.

Cikin nutsuwa ya d’aga hannunshi ya d’ora saman kanta, a hankali ya shiga shafa yalwataccen gashinta kamar mai son saka ta bacci, da sauri ta d’ago kanta ta jaye tare da matsawa nesa dashi tana fad’in “Don’t tauch me, it is your fault i loose my father, my Abhi die because of u, i hate u mr. i hate.”

Duk da ya d’auke hannunshi daga kanta amma bai janyeshi daga saman kanta ba ya tsayar dashi k’yam, kallonta yake sosai yana sake bawa kowace kalmar data fad’a muhallinta, baisan dalilin da yasa yaji kalmar ta masa tsauri dayawa ba? Baisan dalilin da yasa yaji haushi da tsanar kansa sun kama shi ba? Ya rasa gane dalilin da yasa yake jin ba dad’i akan al’amuran da suka shafeta? Menene yasa yanzun nan yake jin kamar yayi ihu ko zai ji sauk’i? Kalmar tsanar nan ya jita ta daki k’irjinshi sosai, shi kanshi sai yaji ya tsani kalmar tsana ta har abadan abada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button