NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Cikin dariyar mugunta Hajia tace “Ke ce kuwa zaki haife abinki kuma ki bashi nono.”

Saida dai mama taga tabbas da gaske take sannan ta zauna tana nuna mata tayi hak’uri haka Allah ya tsara, kuma haihuwa rahama ce wasu nema suke ko da zasu rasa duk abinda suka mallaka, da haka ta kwantar mata da hankali, kiran wayar Salahadeen yayi yana d’auka cikin dariyar mugunta yace “Mai ciki, yaya?”

A tsammaninshi zata sa mishi kuka ne sai yaji tace “Ina ka tafi kuma baka ci abinci ba?”

Ba tare daya daina dariyar ba yace “Ni na yarda na ci abinda kika dafa, ai nasan tsaf zaki sa min guba na ci na mutu.”

Turo baki tayi tace “Daina wasa mana, ka zo ka ci abinci.”

Dakatawa yayi da dariyar yace “Me ya sameki? Na d’auka zakiyi ta kuka ne.”

Ajiyar zuciya ta sauke ta kalli mama sannan ta maida hankalinta kan wayar tace “Mr., akan me zanyi kuka saboda zan haihu da wanda nake so? Me zaisa na tashi hankalina saboda zan saka wanda nake so farin ciki yayin da yayi tozali da abinda ya fito daga ciki na? Ni fa mallakinka ce kuma gonarka wacce kake zuba takinka a duk sanda ka so, in har na yarda ni gonace a gareka kuma kana min ban ruwa a duk sanda nake buk’ata, ni kuwa me zai hana na fito maka da anfanin gonar a sanda ubangiji yace d’a ya kasance a cikin mahaifita? Kayi hak’uri kaji, wanda nayi a baya ma k’uruciya ce da kuma rayuwa a cikin mutanen da basa son haihuwar, amma yanzu ni na dawo daga rakiyarsu, wallahi na maka alk’awarin ko yau zan haihu indai kana so zan sake d’aukar wani cikin.”

Wata sassayar ajiyar zuciya ya sauke mata a kunne yace “Saratu Allah ya miki albarka, kin tabbatar na sameki akan gadona, dan dole na nuna miki farin cikina akan maganganun nan naki.”

Murmushi ta saki ta mik’e tana fad’in “An gama ranka shi dad’e, dole na amsa kiran sarkina ko kuma a k’wamushe ni ban shirya ba.”

Dariya mama tayi tana girgiza kai da fad’in “Allah ya shiryaki.”

Ficewa tayi dan cika umarnin shi, tana jin sakayau da ita tare da jin lallai zata kula da abinda ke cikinta, kuma sai taji wani dad’i da mama tace mata kinga sai kiyi sauri ki gama ki tsane abinki.

Haka rayuwar tasu ta ci gaba da tafiya har lokacin bikin Sajida ya mata izini ta tafi, tasha tsiya a wurin Sajida sosai data ganta da tsohon ciki, amma sam bata damu ba sai mayar mata da magana da take ma, haka akayi bikin aka gama amarya suka sake komawa k’asar mijinta, ita ma Sarah ta dawo ta ci gaba da rainon cikinta, ta wani b’angaren arzik’i na bunk’asa, dan har yanzu kampaninta ana kula dashi kuma Salahadeen na taimaka mata wajen kula da kampanin, shima kuma yanzu harkokin sake bud’ewa kawai suke yi ana ta shiga da fice, sai fatan yin k’arshe mai kyau kawai.

Alhamdulillah

  *Alhamdulillah*

        *Alhamdulillah*

Allah ka yafe min kurakurai na, Allah kasa muyi tarayya a cikin abinda na rubuta daidai, sai mun had’e a ci gaban Allura insha Allah.

*Masoyan Salahadeen fans, wannan book naku ne, hak’ik’a kun min hallaci kun nuna min k’auna, kun tabbatar min zaku iya biyan kud’inku dan karanta littafi na, kun nuna min ku masu biyata ne da kud’i ko babu kud’i, Allah ya barmu tare ya saka muku da alkairi.

馃グ馃グ馃グ馃グ馃グ

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button