NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Kallon Mama yayi sai kuma ya juya kawai yana fad’in “Zan kaita na dawo.”

Ido Mama ta zaro tana fad’in “Ina? Niamey fa?”

Ko juyowa baiyi ba ya sa kai ya fita, d’aga ma mama hannu ta shiga yi harta fice ita ma da sauri, ajiyar zuciya ta sauke ta juya zata koma d’aki ta ga Iffa da Farha zaune, girgiza kai tayi “Kin gani ko? Ni banga abun k’i a jikin bak’on da kasan ba nan zai tabbata ba, gashi dai kamar yanda ta zo ta juya dan komawa inda ta fito, ba wannan ne bun jin ba dad’in ba kamar yanda tayi watsa dake bata kula da sabgarki ba, tana fad’in zatayi kewar kowa amma ke ko kallonki ma ba tayi ba, yanzu ta baki wuri saiki zuba ruwa a k’asa kisha ko?”

Sake girgiza kai tayi dan takaici tace “A matsayinku na musulmai me zaku ragu dashi idan da kun nuna mata soyayya? Ko ba komai da ita zata bayar da shaida akanmu a garinsu na kasancewarmu masu son jama’a, sai dai kash ban san me ya same ku ba, kuka rufe ido kunata sabga mata rashin mutumci, wanda tafiyarta ma yanzu nafi tunanin da saka hannunku a ciki, Allah ya kyauta.”

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:15 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa akan wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               2锔忊儯9锔忊儯

Ko da Mama ta shige ta barsu duk sai jikinsu yayi sanyi, tunani Iffa ta shiga yi to wai ita me yasa tayi haka? Me yasa ta tsaneta? Hakan da tayi ai bai dace ba duba da addininsu ma ya hanesu haka, yanzu me Sarah zata iya fad’a akansu kenan, ba zata tab’a kyautata musu zato da kalamai ba, idan da soyayya suka nuna mata me hakan ya ragesu dashi? Gashi har ta koma inda ta fito fa, da sun mu’amulance da kyau da sun rabu da farin ciki, ta bi ta zuciyarta tare da taya Farha yer uwarta wacce ta fita dalilin k’in Sarah duba da sun had’a miji, amma ita fa? Kai co da nadama marar anfani.

Ita kanta Farha abinda taji kenan, da ita ce a halin da Sarah ke ciki me zata ji? Gashi fa a gabansu ma komai ya faru sanda mahaifinta ya zo, amma saboda shafewar tunani suka hantareta ita kuma ta had’a da cin zarafin mijinta, yanzu gashi ta zubar da kimarta a wajenshi, ta zubar da mutumcinta a wajen bak’uwar da ko kwana goma ba tayi tare da su ba, sannan ba lallai har yanzu tana da wannan matsayin da take da a baya ba a wajenshi, domin kuwa ya fad’a mata ko da kare ya d’aure a ganinshi zasu kula dashi saboda kimar da yake da ba wai dan karen ya isa ba? Cikin rashin jin dad’i ta kalli Iffa tace “Wallahi sai naji kamar ta dawo na rok’eta ta yafe min, gaskiya bamuyi yaya Salah adalci ba da kuma addininmu, mu musulmai mune ya kamata mu zama shaidar kyakyawan d’abi’un da aka koyar da muyi mu’amula dasu, amma sai gashi son zuciya ya hanamu.”

Jiki a sanyaye ta kalleta tace “Abinda nake tunani kenan, abun takaicin sai gashi ita da ba musulma ba ta fimu kyakyawan halaye, dan hak’urin da tayi damu mune ya dace ace munyi da ita, ta kawar da kai daga duk abinda muka mata, sannan ta shanye matsala da damuwarta ba tare da kowa na fahimta ba.”

Cike da tausayin kanta tace “Allah yasa yaya Salah ya dawo da ita karya bari ta tafi.”

A take Iffa tace “Naga kamar ranshi a b’ace fa, zaiyi wuya ma ya mata magana kinsan shi da wannan shirun nashi.”

Dafe goshi kawai tayi ba tace komai ba, mama kuma na shiga d’aki a saman gado ta riski wannan kwalin Sarah ta bari, ta d’auka mantawa tayi da sauri ta fito falo ta samu Mamuh data shigo ta bata wayarta tace “Yi sauri kira min Salahadeen su dawo in basuyi nisa ba ta manta da kwalinta.”

Wayar ta d’auka tare da karb’an ta bud’a, takardar data rufe abinda ke ciki ta d’auka tana fad’in “Wannan ai kamar takardar da naga tayi rubutu a kai ne sanda ta karb’i alk’alami na.”

Sanda ta karanta abinda ke rubuce da sauri ta yanke kiran data aika mishi tana kallon mama tace “Mama ke da yaya Salah fa ta bar wa kud’in nan.”

Da sauri Mama ta dafe k’irji tana kallon kwalin dake cinyar Mamuh tace “Me? Ni kuma? Ni ina zani da wannan kud’in.”

D’aga kafad’a tayi tana fad’in “Gashi dai tace wai ke da yaya Salah kun mata karamci, ita kuma d’abi’arta ce saka alkairi da alkairi, tasan idan da hannu ta baku ba zaku karb’a ba shiyasa ta tafi ta barsu.”

Zaune Mama tayi ta buga tagumi tace “To wai yaushe ma ta samu kud’in nan? A ina ta same su?”

Alamar bata sani ba tayi tare da cewa “Idan yaya Salah ya zo sai muji.”

***Tunda suka d’auki hanya kamar yanda Iffa tace ne babu mai magana, ita tunaninta ya riga daya koma kan abinda zata tarar a can, shi kuma tunanin me yasa ta tsiro tafiyar lokaci d’aya haka? Lokaci lokaci ta kan d’an juya ta kalleshi, amma abun haushi ya k’i kallon inda take, yanda yake nunawa ma kamar baya tare da kowa a motar, dole daga k’arshe ta fita harkarshi ita ma ta ci gaba da kallon hanya.

Yanda ba gudu suke sosai ba ne yasa dare ya riskesu a hanya sosai kuma dama basu taso da wuri ba, kai tsaye filin jirgi suka nufa dan baifi minti ashirin ba zasu tashi, kafin su isa suka sake cinye sauran mintocin, dan haka suna isa duk wurin ya gauraye har an fara kiran sunayen mutanen da zasu hau jirgin nasu, shiru motar ta d’auka sanda kowa ke kallon gabanshi, a hankali ta kalleshi tana murmushi tace “Nagode da duk abinda ka min, ka kula da Mamie da Mamuh, ni zan tafi.”

Har ta bud’a murfin motar ko motsi baiyi ba bare tasa ran zai amsa, har ta zura k’afarta d’aya sai kuma ta tsaya ta juyo, harbawar da zuciyarta ke yi ne take so ta gano dalilin, har yanzu baya kallon inda take dan haka tace “Dan Allah ka min lamunin kiranka mijina sau d’aya tak.”

Duk da bai kalleta ba amma sai taga ya rufe ido, cikin jin haushi ya daki sitiyarin motar ya juyo ya bud’e idonshi a kanta, kamar mai koyon magana yace “Me yasa kike so ki tafi? Ba kya jin dad’in zama damu ne?”

Langab’e kai tayi kamar zatayi kuka tace “Mr…” Bata kai ga fad’a ba taji an kira sunanta a cikin filin wurin, juyawa tayi ta sake juyowa ta kalleshi, sosai take kallonshi kafin tace “Sorry mr., i have no choice, i shouldt to go.”

A hankali ta lumshe idonta ta fara matso da kanta zuwa fuskarshi, a duk kowane samun kusanci da suke k’ara wa bugun zuciyarsu ma tsananta yake, yana jin tana matsowa daf dashi amma bai iya kallonta ba bare ya fahimci me zatayi, a hankali ta sauke labb’ata akan kumcinshi ta mishi hot kiss, bud’a idonta tayi ta kalli fuskarshi shima ya lumshe ido, ba tare data matsa daga kusanshi ba tace “Take care of yourself Slahadeen.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button