NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Marairaicewa tayi tace “Kayi hak’uri yaya Salahadeen, wallahi ba da niyya na turata ba.”

K’uri ya mata da ido yana ta k’ok’arin taushe wani abu da yaji yana taso mishi zuwa mak’oshi, had’ewa yayi kawai ya mata wani shegen murmushi da baida makama sai manufa, shafa gefen kumatunta yayi ya fice da sauri ya bar d’akin, daga tsaye ta bishi da kallo sai kawai ta sake fashewa da wani kukan.
D’akin Mama ya shiga ya samu tuburan km tana shirya kaya wai zata tafi, saida yayi wani b’oyayyan murmushi kafin ya k’arasa ya d’an sunkuya yace “Mama da gaske wai tafiya zakiyi?”

Wani kallo ta masa tace “Ka d’auka da wasa na fad’a?”

Murmushi ya sake yi yace “Mama kiyi hak’uri ni zanje na kula da ita.”

Juyowa tayi da kyau ta kalleshi tace “Saurare ni Salahadeen, bansan tsakaninka da matarka ba, amma magana ta gaskiya ba zan bari ina kallo kuna wulak’anta marainiyar Allah ba, yarinya abar tausayi dan kunga bata da kowa sai a dinga mata cin kashin da aka ga dama, to ba zai yiwu ba kaji na fad’a maka, tun farko da baka bawa Farhanatu fuska ba da bata isa tayi abinda take yi yanzu ba, amma saboda rashin kunya har ni zata dinga kallo tana fad’awa abinda ke ranta, amma kuma har yanzu banga wani b’acin ranka a game da hakan ba duk da dalilinta ne cikin baiwar Allah ya zube.”

Juyawa tayi ta ci gaba da had’a kayanta tana fad’in “Dan haka bana buk’ata ni zan kula da ita, daga yau ma ku d’auka baku da uwa kuma, watak’ila idan kun d’and’ana zafin maraici kun fahimci yanda wanda suka rasa iyayensu sukeyi.”

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta, bai iya cewa komai ba har saida ta juyo tana d’aukar gyalenya zata lullub’a yace “Mama kiyi hak’uri dan Allah ki saurare ni.”

Kallonshi tayi a hassale tace “Ina jinka.”

Wata ajiyar zuciya ya sake saukewa yace “Mama na miki alk’awarin zan kula da ita kamar kina tare da ita, fita k’asar waje ba kamar zuwa k’auyen dake kusa damu bane Mama, yanzu yi miki passeport ma da jiran visarki kad’ai zuwa lokacin ni kaina har na dawo, ba abu bane da zai yiwu yau ko gobe idan ba ta hanyar data sab’a k’a’ida ba, shiyasa nake so kuyi hak’uri Mama ki zauna, na miki alk’awarin zan dinga sanar dake halin da take ciki, sannan da zaran na tafi zan shirya miki tafiya can, tunda ita ma kamar ta sace ki ta gudu dake take ji, kinga idan kon tafi sai kiyi zamanki tare da ita sai dai muje ganinku kawai.”

Shiru tayi tana sauke numfashi da k’arfi k’arfi har ta fara saukewa a hankali alamar ta fara hucewa, mik’ewa yayi yana kallonta yace “Mama ki min addu’a ni zan tafi, Farha kuma zan barki da ita kafin na gyara mata komai ta same mu acan, Mama Farha tana ma Sarah abinda taga dama ne saboda bata san wacece ita ba, ina so taje taga irin rayuwar da take a daular masarautarta, ina so taga yanda take rayuwa cikin ‘yancin, ina so taga yanda Sarah ke bayar da doka da umarni cikin isa da iko, watak’ila hakan zai iya fara saka mata shakkunta da kuma tunani kafin ta tab’a ta.”

Jinjina kai tayi tana kumburo baki tace “Indai akan ladabtar da ita ne ba zan hanaka ba, amma kar kayi abinda zaka kauce hanya Salahadeen ko ka tauye hakk’in wata saboda wata, ka kula da kyau kaji sannan ka kula min da yar amanata.”

Jinjina kai yayi yace “Insha Allah Mama, nagode ni zan tafi saina kiraku.”

Saida ta dafa kanshi yace “Allah ya tsare ya kiyaye hanya.”

Da “Ameen.” Ya amsa ya fita ta bishi da kallo, tsuke baki tayi tana tunanin gwara ya ladabtar da Farhar nan tunda dai bata jin magana, gashi yanzu ta mata asarar gudan jikanta na farko duka kwana d’aya da sanin an same shi a duniya.

Da shiga da fita da hanya aka samu bawa jirginsu izinin tashi ya d’aukota bayan an tabbatar da bata da lafiya ne, dan haka har hukuma saida ta d’auki al’amarin da girma (kunsan dai turawa da su rasa rai d’aya nasu gwara su rasa dubu na black fata馃槑), cikin k’ank’anin lokaci jirginta ya iso filin jirgin dake cikin garin. Lokacin ya iso asibitin shima har d’akin ya yada zango, tsaye yayi gabanta ya mik’a mata hannu yace “Muje.”

Kallonshi tayi tace “I don’t go anywhere.”

Kallonta yayi shima yace “Kin fasa zuwa k’asarki ne?”

Kallonshi tayi da kokonto tace “Da gaske?”

Had’e fuskarshi yayi hakan yasa ta mik’a mishi hannun ya taimaka mata ta sauko, lik’e ido tayi saboda zafi da taji k’afarta, bud’a ido tayi daidai da shigowar wata malamar asibiti, da sauri ta k’araso tana fad’in “Madame har kin samu tafiyar ne?”

D’aga kafad’a tayi alamar eh tare da fad’in “Eh madame, nagode da taimakon da kuka min.”

Kallon k’afarta tayi tace “Madame anya ba zaki bari a duba k’afar nan taki ba kuwa? Dan kamar tana miki ciwo ko?”

Murmushin yak’e tayi tace “No karki damu, ba komai idan da wata matsala ma ina zuwa can zanje asibiti.”

Kallonta tayi tace “Kin tabbatar?”

Jinjina kai kawai tayi suka fara takawa ita dashi, ganin tafiyar ta ta zata tsayar dasu ga kuma halin da take ciki, sai kawai ya sunkuya yayi cak da ita ya d’auketa kamar yar baby, tunda suka fara saukowa ta matakalar duk kusan wanda ke wajen ya koma kallonsu, sun birgesu babu wanda ya gansu yaji wani abu na rashin jin dad’i, ita kam karon farko data ji kunya ta mamayeta saboda abu makamancin haka, duk sai taji dama dai ya sauketa ta k’arasa da k’afarta. Wanda kasan ya d’auko shaid’an a hannunshi haka ya had’e fuska kamar wani hadari, saida suka fita har k’ofar asibitin yayi dubarar bud’e gidan baya ya sauketa zaune, rufewa yayi ya koma mazauninshi ya zauna, babu wanda yace uffan sai sautin wa’azin dake tashi a motar kawai, wayarshi ya d’auka yana dannawa kamar wanda ya tura sak’o kafin ya aje, jefi jefi ya kan sarci kallonta ta madubi, amma abun mamaki bata kallonshi sai titi take kallo, duk da hakan na damunshi amma kuma saiya tab’e baki ya ci gaba da tuk’inshi. Suna isa sun samu jirgi su yake jira, kamar yanda ya sakata da kanshi yanzu ma da kanshi ya bud’e ya d’aukota, cikin izza da jin k’arfi ya shiga taka matakalar jirgin har ya shige, kan wata lafiyayyar kujera ya sauketa, jakar daya rataya kan kafad’arshi taga ya aje kan d’aya kujerar shi kuma ya zauna kujerar dake fuskantar ta ta, sunkuyar da kanta tayi tana tunanin ko wani abu zai ce kafin su tashi.

Kallon taga yayi daidai da zuwan Mustafa tare da wani akan moto, yana kallo ya d’auki motarshi ya juya da ita, k’ofar jirgin aka rufe inda matuk’in jirgin ya fara sanar dasu shirya zasu tashi su d’aura d’amararsu, da sauri ta kalleshi tana jawo d’amararta, ga mamakinta sai taga har ya rigata d’aura d’amarar.

Da mamaki cikin had’e fuska tace “Mr. lafiya? Me kake shirin yi haka? Jirgin fa zai tashi ne.”

Ba tare daya kalleta ba yace “Tare zamu tafi, zanyi jinyar ki ne.”

Da k’arfi tace “Me? Bana buk’ata kawai ka tafi.”

Kallonta yayi ya wani tab’e baki alamar ke ta shafa, cike da son ya yarda da ita tace “Wallahi da gaske nake, bana buk’ata zaka iya tafiya, nagode da nuna kulawarka kaina ma.”

Da mamaki sai gani tayi ya d’ora yatsa akan labb’anshi tare da fad’in “Shiiiiii.”

Ai kuwa ji tayi jirgi ya fara tafiya wanda ya tabbatar mata zai d’auki hanya, cikin tashin hankali ta k’ura masa ido, a hankali kamar a fuskarshi aka rubuta saita shiga tunano abinda ya faru tsakaninta da Dr. d’in nan bayan sunyi nasarar ceto rayuwarta ta farfad’o…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button