NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Yana gama fad’a ya kashe wayar ya aje kan kujera, bai kula da Hajia ba duk da tana tsaye nesa dashi ya fice daga gidan. Ita ma daga b’angarenta kukan ta ci gaba da yi har aunty Bieba taji ba dad’i ta dinga rarrashinta, karo na farko da Sarah ta zauna baki da baki ido da ido ta labarta labarinta ga wani tun daga farkon had’uwarsu har k’arshenta.

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Kinga wani al’ajabi, amma Sarah me yasa zaki hukunta shi da laifin matarshi da k’anwarshi? Suma naga yanzu kun fahimci juna, dan gaskiya na hango kuma naji k’amshin soyayya mai k’arfin gaske a cikin zuciyarshi, Sarah da baya sonki tun farko ma da bai rabaki da mahaifinki ba, domin ya ceceki ne ya gudu dake garinsu, Sarah ke ce silar fara kawo sab’ani alak’ar dake tsakaninshi da mahaifinki, da baya sonki kuma baya so ki zama matarshi da bai tafi dake k’auyensu ba, duk da yasan mutanen da tsegumi da kafiya ga al’adu, haka bai hanashi tafiya dake ba ya shirya amsa duk wasu tambayoyinsu, Saratu da baya sonki da bai mayar dake matar aurenshi ba, ki sani da mutumin banza ne da zai iya nufa dake wani wurin da ba gidansu ba kuma ba gidan mahaifinki ba, da yanda kike tunaninshi ne da tun a hanyarku ta zuwa ya miki fyad’e kuma zai iya jefar dake a kan titi, Sarah da baya sonki da bai tashi hankalinshi sanda yake rik’e dake ba da kina gargarar mutuwa, amma ya saka rayuwarshi had’ari wajen ceto taki rayuwar, dan nasan ke ma kinsan ba cikin sauk’i ya sameki a garin Tha茂lande ba sanda aka sace ki, yanzu kuma gashi daga ganinki akan rakumi ya garzayo ya biyo ba tare da sanin mahaifiya ko matarshi ba.”

Girgiza kai tayi ta rik’o hannayenta tace “Wace irin soyayya kike so ya miki bayan wannan? Me kike so ya nuna miki kuma daya wuce wanda yake nuna miki? Sarah ki farka daga baccin nan haka, abinda ya kamata ki mayar da hankalinshi kanki ki kuma tambayi kanki yanzu shine, shin kema kina son shi? Ko kuma dai shine ke haukan son ki?”

Tsatsareta tayi da idon da suke ci gaba da mata ambaliyar ruwa, jinjina mata kai tayi tace “In har gaskiya zan fad’a miki mai sunan Hajia sai nace miki ke ma kika son sa, ba dan komai ba sai dan ajiyewa da kuma kula da kike bawa cikin shi, sannan lokacin da kika same shi kina da damar da zaki iya yin burus ko ma ki cire shi, amma da hanzari kika b’ata kud’i da lokaci kika same shi har k’asarshi kika fad’a masa, sannan in tambayeki tsakaninki da Allah?”

Ita dai da ido kawai take binta, d’orawa tayi da cewa “Sanda kukayi nisa dashi ba kya yawan tunaninshi ko tuna duk wani abu daya shafe shi?”

Rarraba ido ta fara yi alamar tana tunani, kallonta tayi tana tsuke baki tace “Duk abinda ya faru a zamana dasu gidansu yakan tayani hira yayin da nayi shiru, kuma nafi yawan tuna lokutan da muka kasance ni da shi ne kawai.”

Jinjina mata kai tayi tace “Kin gani, kuma gabanki na fad’uwa ko da sunansa kika ji ko?”

Da sauri ta d’aga kai alamar eh tare da fad’in “Gaskiya kam, indai yana kusa dani bana samun sukuni daga tanan b’angaren.” Ta fad’a tana nuna k’irjinta, dariya ta mata tana fad’in “Saratu na ke ma kina son bawan Allahn nan, wallahi karki yarda aurenku ya rabu, yanzu ba kince zaki je bikin k’anwarshi ba?”

D’aga kai tayi alamar eh sannan ta d’ora da cewa “Yawwa, yanzu ki shirya ma tafiya kuje lafiya ku dawo lafiya, Hajia zamu kula dake har ki haihu sai a miki gyaran jiki, a d’an wannan lokacin ina tabbatar miki zai fad’a miki abinda kunnuwanki suke son ji.”

Girgiza kai tayi tana dariya haka ita ma aunty Bieba, haka suka ci gaba da tattaunawa har yamma Sarah bata koma gida ba tana nan zamanta ana bata tana ci tana k’oshi.

Bata yarda tayi magriba anan ba ta koma gida a taxi, ko da taje Hajia ta so mata fad’a amma kuma saita kasa saboda tuna marainiya ce kuma duka yaushe ma suka saba? K’yaleta kawai tayi sai abinci data sa ta ci ta sake k’oshi ta kwanta.

Bayan kwana hud’u kasancewar tun jiya suka kwana Zinder yasa yanzu sukayi sammako suka shirya tsaf suka kama hanya tare da Hajia Aba da Sabira, shiru take duk bata jin katsashi, ta damu sosai a kwanakin nan daya shareta bai kirata ba, tasan hushi ne yayi, amma a ganinta in yana sonta kamar yanfa aunty ta fad’a me zaisa yayi hushi da ita? Duk hirar dasu Aba keyi bata saka baki har saida Aba yace “Hajia lafiya naji kinyi shiru?”

Cikin sanyin murya ta amsa da “Lafiya lau Abhi, kawai bacci ne nake ji.”

Juyowa Hajia tayi ta harareta tana fad’in “Kaji ja’ira, wato yanzu kwana har ya zamar miki jiki ko?”

Mirmushi kawai tayi tana d’auke idonta daga kan Hajiar ta mayar a titi, awa hud’u ta k’araso dasu cikin garin dan ba gudu sukeyi sosai ba saboda Hajia, kai tsaye Aba gidan wani abokinshi ya wuce dasu wanda dama yasan da zuwansu, tarba suka samu ta musamman a wurin iyalinshi, d’akin bak’i aka sauke su sai Aba dake tare da mai gidan Alhaji Nasir, wanka sukayi suka ci suka k’oshi, saida Hajia ta rabawa matan gidan tsarabar data taho da ita sannan Aba yasa Sarah ta kira Farha ta tambayeta kwatancen gidan? Yanda ta fad’a mata haka ta fad’awa Aba hakan yasa shi cewa “Babu ma wuyar gane wurin ai.”

Kallonshi Sarah tayi tace “Aba kasan garin nan sosai?”

Dariya kawai ya mata suka d’auki hanya, kamar ba daga tafiya suke ba saboda yanda sukayi tass dasu har mota an wanketa. Tunda Aba ya tsaya a k’ofar gidan ta kalli gidan ta gane shi, a hankali suka fita suka tunkari shiga ciki sai gabanta dake ta fad’uwa kamar zata had’u da mugun abu, Aba ne ya tsaya k’ofar gidan tare da mai gadi suna gaisawa, suna shiga mutane ne dayawa na ta kai da kawo ana ta hidima musamman mutanen k’auye, hakan ya tabbatar musu da lallai gobe ake bikin, cikin rad’a Hajia tace ma Sarah “Ke ashe mijinki mai kud’i ne? Wannan gida haka mai kyau da girma.”

Kallonta Sarah tayi kawai tayi murmushi, to ina abun yake? Da taga inda ta rayu fa ya za tace? Ko da yake kam dole su suga kyawun gidan, Iffatu ce ta fito da wasu kwanuka a hannunta, tana ganin Sarah ta daka ihu ta saki kwanukan ta taho da gudu ta rumgumeta tana fad’in “Aunty Sarah, ke ce?”

Mamaki ne yasa Sarah kasa motsawa sai kallon ikon Allah, wai yarinyar da babu irin cin mutumcin da bata mata ba, ita ce yau ke mata wannan? Tab’e baki tayi ta k’ak’aro murmushi ta d’agota daga jikinta tace “Iffa, ya kike?”

Da murna ta amsa da “Lafiya lau, ya hanya?”

Da murmushi ta amsa da “Lafiya lau, ya hidima?”

Saida ta kama hannunta zasu shiga ciki tana fad’in “Muje ciki ki ga Mama.”

Kallonsu Hajia tayi tace “Ina kwana Hajia.”

Amsa mata Hajia tayi da sakin fuska sai Sabira da suka kalli juna suka gaisa da sannu, su Salamatu da Rakkiya suna ganin Sarah suka gane baturiyar k’auyensu ce, ai suma da murna sukayi kanta suna musu sannu da zuwa, ita ma dake ta gane su har rumgume Salamatu tayi suka gaisa suna mata dariyar wai yanzu tana jin hausa ba kamar da ba.

Haka da suka shiga ciki kowa dai a zahirance farin ciki ne akan fuskarshi, babu wanda yasan bad’ini kuma, musamman ma ganin ciki jikinta dan duk manya masu hankali suna ganinta suka fahimtar haka, d’akin Mama suka sauka aka shigo lodo musu abinci da lemu mai d’auke da tambarin sunan Sla, hatta ruwan da aka kawo musu a jikin robar wannan sunan ne, ita dai tana son sunan kayan nan tana jin dad’in nanata sunan duk sanda taga abun. Har Mamuh amarya saida ta shigo suka gaisa kafin ta koma d’akinsu inda take da k’awayenta, ruwa kawai suka iya sha da d’an lemun, sai Sarah data dinga yi wa Mama tab’ara tana fad’in ita fa irin naman nan take so ta ci wanda suka tab’a ci, ganin yanda Mama ke ta rumgumarta kamar jaririya yasa Hajia kama baki tace “Kice duk ke kika lalata ta haka, irin wannan shegantaka kamar haihuwar yau.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button