NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Ganin baice komai ya tabbatar masa da gaskiya kenan, dan haka yace “What a wonderful plan! Great.”

Kallonshi yayi yace “Bari na turo maka ‘yarka ku tafi, ni dai na tsame kaina daga al’amarinku, sannan ina da hujjojin kare kaina.”

Har zai wuce ya rik’o hannunshi yana wani murmushin mugunta, saida suka sake kallon juna ya gyara tsayuwa da kyau yace “Salahadeen kana da basira sosai, shi yasa nake sonka sosai, ka harbo shiri na kuma hakan ba shi zaisa na fasa abinda nayi niyya ba, ka sani tun kafin na haifi Sarah nake rayuwar jin dad’i, ina sonta so mai tsanani saboda ni na haifeta, sai dai duk son da nake mata nafi son kud’ina akanta, kuma ita kanta na tabbata tafi son kud’i akan Abhinta, zata iya rayuwa babu ni amma rayuwa babu kud’i Sarah ba zata iya ba.”

Wata yar dariya yayi yace “To ina ma zata iya? Yarinyar da kud’in da take biyan mai wanke mata k’afa kad’ai sun isheka siyan motar da ranka ke so, Salahadeen! Rayuwar nan idan babu kud’i babu mai kulawa da kai har danginka ma bare a waje, dube ni yanzu, a k’asar da ba tawa ba ina iya fad’awa gwamnati kuma ta saurare ni, gwamnati kanta takan iya neman shawara ko kud’i dan gabatar da wani aiki a guri na, to ni kam me ye kud’i bai min ba a rayuwa?”

D’orawa yayi da “Ita kanta Sarah da zan bata zab’i zata zab’i ta mutu akan mu koma rayuwar talauci, ba zata jura ba ko kad’an dan bata saba ba, yarinyar da ko kukan yunwa bata sani ba bare kammninta, kaga ka manta da Sarah kawai, tunda babu komai tsakaninku na nesa ko na kusa.”

Jinjina kai yayi yace “Gaskiya ne, dama tun farko ba ita na ceta ba uba na so na ceto daga aikaya zunubin kisan ‘yarsa ta cikinsa, sai dai na gama fahimta yanzu cewa abotarka da shaid’an bata yau bace, amma kasan wani abu d’aya, kai musulmi ne kuma ka yarda zaka mutu, akwai hisabi tsakaninka da Sarah mai yawan gaske.”

Da yatsu ya shiga lissafa mishi yana fad’in “Na farko zata tuhumeka dalilin da yasa ka k’i d’orata kan addinka na gaskiya, bayan kuma Allah ya lamunce mana mu auri ahlul kitab ne saboda maza mune shuwagabani a cikin gidajenmu, amma saika barta sakaka babu madogara bare ak’ida, sannan zata tuhumeka dalilin da yasa ka ciyar da ita da haram ka girman da gabb’an jikinta da haram, a k’arshe kuma ta nemi dalilin da yasa ka kasheta.”

Wata dariya yayi yana fad’in “Salahadeen wai yaushe ka koma wa’azi ne? Ka manta ni da kai tare muke?”

Da sauri ya katse shi da cewa “Ba tare muke ba, zunubinka yafi nawa girma, ina aikata komai daka sakani ne saboda rudun duniya, amma yanzu na farka daga baccin daya dauke ni, zan nemi halak d’ina da k’arfin da Allah ya hore min, zan jajirce wajen ganin na cika yak’inin da mahaifina ke da a kaina.”

Zai wuce ya sake rineshi a hassale ya kubce hakan yasa shi cewa “Kwantar da hankalinka mana, kai yaro ne Salahadeen har yanzu baka san inda duniya tasa gaba ba, ba’a samun kudi cikin sauk’i sai ansha wahala, ni kuma a gurina zaka iya kashe rai ma dan ka samu kud’i, ka sani ba wai Sarah bace rai na farko da zan d’auka, sanda ka gudu da ita abu na farko da ya zo tunani na shine zaka rabani da ita kamar yanda mahaifiyarta tayi yunkuri yi, da kyma hakane ya faru da kaima ka bi mahaifiyarta inda nasa aka aikata.”

Da wani d’an banzan mamaki ya kalleshi baki bud’e yace “Kana nufin kai ka kashe mahaifiyarta saboda son duniyarka? Duniyar da zaka barta?”

Girgiza kai yayi yana fad’in “Oh my God.”

Takawa yayi da niyyar shiga gidan sai kuma ya tsaya cak ganin Saraf a tsaye…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 03:58 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa ta Orange money(ba chap chap ba yan uwa, orange money dan karka tura ta chap chap amma zaku iya tura kati) akan wannan lambar 91-71-28-22 ko kuma wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               9锔忊儯

Da sauri ta tako ta tsaya gabanshi tana kallonshi, hawaye ne fal idonta suna k’ok’arin sauko mata tace “Abhi, what are u saying? What are u talking about it? My mother.”

Nuna kanta tayi tana fad’in “Abhi u kill my mother because of your selfishness? Abhi…”

Durk’ushewa tayi ta fashe da kuka iya k’arfinta, da sauri ya sunkuya yasa hannu zai kamata tayi sauri ja baya tana fad’in “Stop, dont tauch me again, i hate u Abhi.”

Durk’usawa yayi yana fad’in “Sarah ki saurare ni, bani na kashe mahaifiyarki ba, kar…”

Da k’arfi ta mik’e tsaye tace “Abhi bana son jin komai, kai ne ka kashe min mahaifiyata kuma kake son kashe ni, ashe dama kai mugu ne.”

Rik’e hannunta yayi gam da k’arfi ya jata yana fad’in “Muje gida zamuyi magana.”

Tirjewa tayi tace “Babu inda zanje Abhi, sake min hannu na ba zan bika ba, kashe ni zakayi.”

Sakin hannunta yayi ya kalleta kallon da bai tab’a kwatanta yi mata shi ba yace “Wuce mu tafi Sarah karki b’ata min lokaci.”

Baya taja tana fad’in “I dont go anywhere.”

Cike da tabbatar mata yace “Yes u can.”

Da k’arfi tace “I cant.”

Da mamaki ya kalleta ya nuna kanshi yace “Sarah ni kike d’agawa murya?”

Da wani k’arfin ta sake d’aga murya tace “Yes, yes Abhi, u are a monste…”

Bai bari ta gama fad’a ba yasa hannu ya d’auketa da mari, yanda marin ya daki fuskarta yasa ta durk’ushewa k’asa, a matuk’ar tsorace ta d’ago tana kallonshi duk gashinta ya rufe mata fuska, ko d’aga mata murya bai tab’a yi ba shine yau ya mareta. Cikin rashin jin dad’i ya sunkuya zai mata magana, da sauri ta fad’i zaune ta shiga jan k’ugu tana yin baya baya, cikin rashin sani ta kaiwa Salahadeen karo dake tsaye har yanzu, da sauri ta juya tana ganin shine ta mik’e da sauri ta lab’e bayanshi.

Yanda ta cumimiyeshi tana ta turmusar mishi riga ta d’ora hab’arta kan kafad’arshi tana fad’in “Ka d’auke ni daga nan, karka bari ya tafi dani please mr., bana so na tafi tare da shi kayi wani abu.”

Matsowa yayi ya tsaya gabansu yana kallonta ya tara mata hannu alamar ta taho, sake b’oye kanta tayi cikin bayanshi ta zuro hannunta a k’irjinshi tana murza mishi k’irji, juyawa yayi ya hangi su mama har da Farhana da suka fito ganin ya kama hannun Salahadeen ya fita dashi, duk tare da Sarah suka fito sai dai mama babu abinda take fahimta, su d’in ne ma idan suka ji wani abu suke d’an ganewa amma ba sosai ba, sai Mamuh ce kawai tafi gane duk yaren da sukayi a harshen french.

Sake kallon Shakoor yayi a hankali ya sa hannu ya shiga k’ok’arin b’amb’areta, gam ta rik’e rigarshi tana kuka da iya k’arfinta tana fad’in “Bana so, bana so na tafi dashi, karka bari ya tafi dani mr. na rok’eka, zan zauna tare da kai anan ba zan bishi ba, kashe ni zaiyi kamar yanda ya kashe mahaifiyata.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button