NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Mik’ewa a hankali ya tunkaresu kanshi k’asa yana murza hannunshi yace “To ni ne mijinta, ita d’in matata ce kuka sace.”

D’aga kai yayi ya kallesu yace “Uwar jaririna ce, cikina take d’auke dashi, amma tsabar rashin mutumci kuka saceta, yanzu ya kuke so nayi kenan idan wani abu ya sameta da kuma abinda ke cikinta? Na d’aukeku na kaiku yawon bud’a ido? Ko kuma na kaiku wajen hutawar da yafi kowane kyau da tsada a babban birnin america? Ko kuma dai…”

Bai k’arasa fad’a ba da k’arfi ya dunk’ule hannu ya gabzawa d’ayan, wuntsilawa yayi daga kan kujerar take bakinshi ya fashe sai jini, d’ayan na ganin haka ya shiga kiciniya kamar yana son ja baya yana fad’in “Kayi hak’uri Salah, mun rantse maka bamu san ita matarka bace, karka kashe mu kaji zamu fad’a maka komai da muka sani.”

A hankali ya juya ya sake komawa kan kujerar yana murza hannunshi da yayi zafi ya kalleshi yace “Ina kuka kaita?”

Cikin sauri yace “Wani gidan madara ne aka umarcemu mu kaita.”

D’auke idonshi yayi daga kanshi yace “Waya umarce ku?”

A raunane yace “Ka yarda dani Salah na rantse maka bamu san ko waye ba, ta waya kawai ya kiramu ya bamu aiki, tun kafin mu saceta ma ya biyamu kud’inmu.”

Kallonshi yayi yana shafar sumar kanshi yace “Sauran yaran da kukayi aiki tare dasu su waye?”

Girgiza kai yayi yace “Bamu san su ba, a lokacin daya bamu aiki ya turo mana su su hud’u, daga lokacin ma bamu sake magana dashi ba ta waya sai d’aya daga ciki ne yake tura mishi duk wata masaniya ta hanyar sak’on MMS.”

Mik’ewa yayi ya kalli wani daga ciki yace “Ku karb’i adresse d’in ku tura min ta SMS.”

Kallon Richard yayi yace “Ka biyo ni muje.”

Wannan matashin na farko ya kalla yace “Kai ma biyo ni.”

Mik’ewa yayi yana tsalle tsalle harda tsallaka kujerar da Salahadeen d’in ya tashi ya bi bayansu yana fad’in “Takardata ta fito.”

Fita suka tare suka shiga mota, suna tura mishi adresse d’in ya bi kwataccen daidai suka isa kampanin.


Tana bud’a idonta ta sauke su akan jar fitilar dake saman d’akin wacce haskenta ya gauraye ko ina, a hankali ta shiga sadda kanta k’asa har ta samu damar k’arewa d’akin kallo, banda jan yadi dake rufe da duka bangon sai k’warya a tsakiyar d’akin da kuma wani abu sak k’ok’on kan mutum, cikin lumshe ido ta furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, ina ne nan kuma? Me ya kawo ni nan?”

Motsawa tayi sai taji k’afafunta sun mata wani abu haka kuma ta kasa dawo da hannayenta zuwa gabanta, da sauri ta shiga dubawa ashe ita ce a d’aure, an d’aure k’afafunta a tank’washe haka ma hannayenta ta baya, mitsitsikawa tayi amma jim yaji su,
d’aga kai tayi zata sake kallon rufin d’akin sai kuma taji an bud’e k’ofa, dubawa tayi ta b’angaren da taji k’arar amma kuma babu alamar k’ofa bare ta ga mai shigowa. Ganinshi kawai tayi ya shigo kuma abinda ya k’ara tsorata ta shine rufe k’ofar da taji an sake yi, ajiyar zuciya ta sauke cikin jin dad’i tace “Alhamdulillah Allah nagode maka, uncle ina ne nan? Dama tare muke da kai? Me ya kawo ni nan?”

K’ala bai ce mata ba ya wuce gaban k’waryar nan ya tsaya, rufe idonshi yayi ya rumgume hannaye kamar wanda ya shiga sallah, kamar a almara sai gani tayi kayan jikinshi sun canza daga suit d’in daya shigo dasu zuwa doguwar riga ja, firgita tayi sosai taja baya tana k’ara zaro ido tana kallonshi, ya jima haka bai motsa ba sai jinjina kai da yake yi kamar yana magana da wani, ganin abun bana kai sake bane yasa ta fara karanta addu’a daga nan takure tana k’ara kallonshi. A harzuk’e ya bud’a ido sunyi zajur dasu ya tunkarota a matuk’ar hassale, yana zuwa daf da ita bai tsaya komai ba yasa k’arfi ya kwad’a mata wani gigitaccen mari, wata k’ara ta saki mai kayar da gaban mai sauraro, abu ga jar fata tuni yatsunshi suka fito kan kumatunta reras dasu, inda hancinta kuma da gefen bakinta jini duk suka sallamo mata lokaci d’aya.

Durk’usawa yayi gabanta ya finciki gashinta dake cikin hijab d’inta da k’arfi, wata k’arar ta kuma saki saboda masifar zafin da taji, idonta lik’e gam duk ta had’e sama da k’asa na fuskarta, cike da mugunta da k’eta ya sake jan gashin nata hakan yasa ta saurin mik’e k’afafunta da taji fitsari na son kubce mata, bud’a ido tayi cikin masifa ta fizgo kalamanta tace “Uncle please, da zafi fa, me nayi maka kake son cutar dani?”

Da k’arfi ya sake fizgar kanta ya juyo da kallonta kanshi cikin kakkausar murya yace “Karki sake yi min addu’a a wurin nan, idan ba haka ba zaki sa na kasheki lokacinki baiyi ba.”

A wahalce ta kalleshi tace “Kisa kuma uncle? Dama zaka iya kashe ni?”

Sakin gashin nata yayi tare da turata gefe ya mik’e tsaye yana fad’in “Uban daya haifeki ma ya so kasheki bare ni da ban had’a komai dake ba.”

Da k’arfi cikin d’aga murya tace “K’arya ne, Abhi bai so kashe ni ba, tseratar dani yayi, sai dai in kaine kake son kashe ni yanzu.”

Juyowa yayi yana murmushi ya sake durk’usawa yasa yatsanshi manuniya yana yawo dashi akan fuskarta yace “Tabbas kasheki zanyi, sai dai ba yanzu ba, lokacinki na nan zuwa.”

Nok’ewa ta fara yi tana duk’ar da kanta saboda sauko da yatsar da yayi kan wuyanta har kamar zai shigar dashi cikin rigarta, wani murmushin ya sake yi ya mik’e yana fad’in “Dole na kasheki tunda shi mahaifinki ya kasa, shin kin ma san dalilin da yasa na dauk’arwa shugabana alk’awarin kawo masa ke?”

Zuba masa ido kawai tayi tana kallo a matuk’ar tsorace gabanta na fad’uwa, d’orawa da cewa “A dalilinki ne aka karya min yaro aka masa raunin da ko lokacin k’uruciyarshi bai samu ba, shiyasa na ci alwashin d’aukar masa fansa akan hakan, zanyi farin ciki idan naga an salwantar da rayuwarki, sai dai kuma kafin faruwar haka dole sai nayi jiran kin haihu, duk da dai a lokacin zamu ci riba biyu ne, amma jiran zai wahalar dani.”

Lumshe idonta tayi ta furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un.”

Bud’a ido tayi ta kalleshi tace “Shi yasa dama kake bibiyata? Me yasa ba zaku kasheni yanzu ba?”

A hankali ya zauna k’asa ya tank’washe k’afafunshi yana kallonta yace “Haka dokar k’ungiyar take, shugaba yace ba za’a kasheki da ciki jikinki ba dole sai kin haife shi.”

Girgiza kai tayi cike da rauni tace “K’ungiya? Wace irin k’ungiya ce wannan mai shan jinin bil’adama? Wace k’ungiya ce wannan kuka saka kanku a cikinta wacce kuke ganin ta dace daku? A ganinku Allahn daya halliceku bai muku gata ba sai wani ne zai muku abinda kuke so? Duk k’ungiyar da babu Allah kuma bata koyar da sunnar annabi Muhammad (S.A.W) to tabbas babu alkairi a ciki, k’arshe zata ja k’afafunku ne izuwa cikin k’asan wuta, uncle kasa na fara zargi Abhina kuma na fara gazgata masu fad’a cewa yana tsafi.”

Wata irin dariya ya bushe da ita har da rik’e ciki kafin ya tsagaita ya kalleta yace “Sai yanzu ne kika fara wannan tunanin? Lallai Shakoor ya jima yana yaudararki, ai kamar yanda kika fara tunani ne ni da mahaifinki sabgarmu d’aya kuma k’ungiyarmu d’aya.”

Kallonshi kawai tayi tana sako da wasu hawaye masu zafin gaske na nadama, mik’ewa yayi yayi tako biyu zuwa uku kafin ya juyo ya kalleta yace “Zaki ci gaba da zama anan, amma ki sani babu abinda zai kub’utar dake daga rik’on da nayi miki.”

Yana fad’a sama ko k’asa ta rasa inda ya nufa sai waige waige data shiga yi, madadin ta fashe da kuka kawai sai taji wani k’arfin hali da k’arfin gwiwa sun ziyarce, gyara zamanta kawai tayi ta lumshe idonta ruf ta fara rera karatu murya k’asa k’asa, dan yunwar data kwana ta tashi da ita ga kuma bacci sun fara tasiri cikin gangar jikinta ta yanda suka fara karya mata duk wani sinadarin dake bayar da k’arfi a cikin gangar jikinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button