NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Harshen daya mata magana dashi yasa ta fahimtar da ita yake, cikin sanyin murya tace “A’a, ko ruwa ban sha ba.”

A dak’ile ya amsa da “Me zaki ci?”

A hankali tace “Ka zab’a min.”

A hankali Farha ta kalleshi, jinjina kai tayi a ranta tana k’udurta “Lallai yau asiri zai tonu duk k’auyen nan su sani, wallahi saika saketa ko bata tashi barin garin nan ba.”

D’an dafe goshin da tayi yasa Mustafa kallonta yace “Ko kanki ke ciwo?”

Girgiza mishi kai tayi tare da fad’in “A’a, kawai dai saboda na saba shan koffee ne a irin wannan lokacin, amma yanzu har na fara sabawa kuma da rashin shi d’in.”

Cikin murmushi yace “Bari mu dawo ko saina had’a miki shi mai k’arfi biyu ma.”

Dariya tayi harta fito da hak’oranta tace “Ka iya ne dama? Kuma kaga dama mai k’arfi nake sha.”

Zeid ne yace “Idan kika sha kuwa sai kinyi ciwon ciki, babu abinda ya iya in fad’a miki gaskiya, ko ganinshi ma bai tab’a yi ba a zahiri.”

Dariya kawai tayi tare da kallon madubin dake fuskantarta, da sauri ta d’auke idonta saboda gabanta taji ya fad’i sanda suka had’a ido a bazata, k’asa tayi da kanta tana rarraba ido duk sai taji kamar ta takura da inda take zaune. Shima kuma sai yaji kamar ya daki sitiyarin saboda had’a ido da sukayi, ai sai taga kamar ita yake kallo tun d’azu, kuma gaskiya ne yana kallonta jefi jefi, musamman da suka fara hirar nan, sai yaji kamar ya samu koffee ya bata tasha, dan ire iren abun nan idan ka saba suna haddasa maka ciwon kai. Tsayawa yayi ya siyo mata sandwich kamar ranar tare da dafaffen kwai ya dawo, saida ya gama mik’awa kowa kafin ya tayar da motar, abun fad’a ne yake gudu shiyasa ya k’i siyo mata ita kad’ai, ko da taga k’wai ta mik’a mishi tare da fad’in “Bana cin k’wai mr.”

Bai juyo ba yace “Me yasa? Yana da anfani a jiki shiyasa na siyo miki.”

“Eh hakane, amma ni bana cin shi sai dai kaza.”

A hankali ya tsaya daga shirin tayar da motar ya juyo ya kalleta, lokaci d’aya kuma ya d’auke kanshi ya tayar da motar, mik’awa Mamuh tayi ta karb’a amma ta aje.

Tafiya suka dinga yi madakata kawai suke tsayawa ya nuna takardu su wuce, abun jin dad’i shine daf da su isa garin suka samu ana ta ruwa sai dai ba k’warai ba, su Zeid ne suka dinga tattaunawa ashe har anfara samun ruwa, shi dai bai tanka ba tafiya kawai yake, kamar wasa saiga su a k’auyen kwantagora, ba nisa ne dama ba ko matsalar hanya, dan danan ya sadasu da k’ofar gidan da suke kiran babban gida, gidan da aka haifi mahaifinsu kenan, kakansu nada mata hud’u kuma kowace da yayanta, yayan ne yanzu da jikoki a gidan tari guda, a hakan ma dan akwai mutuwa kuma wasu ba nan suke zaune ba.

Duk fita sukayi suka shiga ciki sai ita data tsaya tana kallon ko ina da kyau, har saida ya fito ya sameta tsaye bata gusa ba, a hankali yace “Muje.”

Kallonshi tayi da mamaki tace “Ina ne kuma ka kawoni nan?”

Saida ya shige yace “Gidan kakana.”

Tab’e baki tayi ta bi bayanshi suka shiga suna ta rabka sallama, babu soro sai filin gida da babbar bishiya a tsakiyar gidan, duk wani yaro mai wayo ya tafi makaranta sai k’anana da basu isa ba, matan duk suna farfajiyar gidan kowa da abinda yake, wasu na hura wutar d’ora girki domin tukunya d’aya suke d’orawa da rana, wasu kuma suna dakan furar da zasu kaiwa mazajensu gona, sai wasu na wanka wasu na tankad’en garin tuwo.

Gidan kamar gidan tarihi ya zamar ma Sarah, yanda take kallon komai zai ganar da kai haka, musamman da kowa ya shiga musu maraba da murnar ganinsu, wurin zama duk suka samar musu ana ta gaisawa. Sai dai kamar yanda take musu kallon mamaki da rashin sani haka suma suke binta da kallon nan, sai dai babu wanda yace komai har aka kawo musu ruwa da aka sirkasu da fura yayi tsululu, b’angare d’aya kuma kunu aka kawo musu d’aya daga cikin matan k’aramarsu tace “Bari na nemo musu glas (k’ank’ara) su saka a ciki kinsan yan birni.”

Dariya kawai sukayi su dai suna kallonta, saida ta fita daga gidan babbar matar yayan mahaifinsu ta kalli Sarah da kyau ta kalli Salahadeen tace “Salaha wannan kuma wacece? Ban santa ba ko a dangin Amina.”

Ka rantse ba shi ta wa magana ba saboda ko kallonta baiyi ba, Farha da dama take jiran jin wannan tambayar da sauri tace “Matarshi ce ai, tare suka zo.”

Duk tsit gidan ya d’auka suka zuba ma Sarah ido da kuma Salahadeen, su kuma da suke tare da ita sai suka sakar mata ido suna kallonta, kallonshi tayi ta tab’e baki ta d’auke kanta.

Wacce tayi tambayar ce tace “Matarshi kuma? Jan kunne ka aura Salahadeen?”

D’aga kai yayi ya kalleta, sai kawai yaji haushin zuwanshi ma dan har yaji kanshi zai fara mishi ciwo saboda maganar da Farha ta jazo mishi, kamar mai ciwon baki yace “Eh Inna, matata ce.”

Kallon Sarah yayi daya ga tana lura da yanayin kowa ya nuna mata Inna yace “Ki gaisheta Mamana ce.”

Mik’ewa tayi tsaye ta mik’a mata hannu alamar su gaisa, bud’e baki tayi kamar zata saka wani abu a bakin tsabar mamaki, juyawa tayi ta kalli duk matan dake bayanta ta kuma kalli Salahadeen, da ido ya mata alamar bata kawai, har Sarah zata janye hannunta saboda k’osawa sai kuwa Inna Salamatu tayi ram da hannunta ta rik’e.

Bushewa tayi da dariya ta juya tana kallon matan dake baya tana fad’in “Ke kunji hannunta sai taushi, yo ba dole ba ba daka takeyi ba kamar mu.”

Juyowa tayi ta kalli Sarah suka yi ido biyu sosai, d’aya hannunta tasa ta shafi fuskarta cikin washe baki tace “Kyakyawa da ita ko, Allah ya tsareki yarinya.”

Sarah dake mamakin yanda taji hannun mace murmushi ta sakar mata, ta fahimci abinda ta fad’a dan haka ta zage hannunta daga rik’on data mata kawai ta d’an rumgumeta tana fad’in “Thank u Mom, thank u.”

Duk matan sai suka bushe da dariya wata na fad’in “To fa jan kunne yau Salamu kin shiga hannu.”

Suna raba jikinsu tayi dariya tace “Ke wallahi babu ruwanta, tana da nutsuwa.”

Dawowar wacce ta fita siyan glas yasa aka saki wannan zancen, suna had’a ido da Farha ta harareta tana jan tsaki, nan aka saka glas d’in kowa ya sha wanda zai iya sha, kunu da taga kowa yafi d’an kurb’awa yasa ita ma ta kafa kai.

Duk k’ok’arinta na son had’eshi ya fad’a cikinta abun ya gagara, abinda ta lura shine wannan abun ba zai tab’a shayuwa gareta ba, tunda Mamie ma ta tab’a bata shi ta amayeshi, ganin tunda ya riga ya shiga baki bari ta had’eshi yasa ta turashi da k’arfi ya wuce mak’oshi, ai ba shiri taji ya dawo zai bulbulo, da gudu ta aje tasar ta koma nesa dasu ta sunkuya ta amaye shi.

Duk gidan ne ya d’auka jan kunne na amai saboda tasha kunu, cikin matan ne wata tace “To me kuke bata a gidan naku Salaha?”

Saida ya lumshe ido saboda ya tsani sunan Salaha nan kafin ya bud’e ya kalleta, Mamuh ce tace “Wannan dai ne ina ga bai karb’eta ba.”

Wata ce ta bata ruwa ta kurkure baki ta dawo ta zauna, kallon fuskarta yayi musamman labb’anta da yaga har jan bakin ya goge, muryar Salamatu ce ta dawo dashi da take fad’in “Yawwa Rahamu idan kin kai saiki aika ko Abdu ne ya sanar dasu sunyi bak’i fa daga birni.”

Wacce ta d’auki hanyar fita da roba a saman kanta ta amsa da “To, in ma ban ganshi na wuce da kaina in sanar dasu.”

Sun so su tafi wasu gidajen gaishe da han uwa, sai Salamatu tace suyi hak’uri su jira baffannin nasu su dawo yanzu sai su tafi, haka kuwa suka zauna ana ta hira inda hankalinsu yafi komawa kan Sarah, komai nata kallo suke kamar su dakata da komai suyita kallonta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button