NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Fizge hijabinta tayi tana fad’in “Kana d’auke da bindiga ne kake tunanin bani kulawa? Leave me alone.”

Fita tayi ta same su tana tambayar me ya faru? A lokacin har mai tsaron k’ofa ma ya shigo kowa na ta fad’in banga komai ba, banga wani alama ba komai lafiya lau, Farha ce ta matso da mamakin ganin Sarah tace “Dama kina nan? Na shiga d’akin ban ganki ba.”

Kallonta tay tace “Eh, na kwanta anan k’asa ne.”

Sandra ce tace “Amma princess ya zaki ce kin kwanta a k’asa? Bai dace dake ba a halin da kike ciki.”

Da hannu ta mata alama tace “Dont worry about me, yanzu kowa yaje ya kwanta tunda babu komai.”

Juyawa tayi zata koma d’aki ta sauke ido akanshi, tsaf idonshi akanta suke ganin zata jiyo ne ya d’aukesu sai kace baisan ma tana wurin ba, takawa ta fara yi ba tare data taka digadiginta ba, cak ta tsaya kuma saboda tunawa da wani abu, zaro ido tayi ta shiga rarraba su, da sauri ta sake kallon inda yake da k’arfi sosai cikin d’aga sautin da yasa kowa tsayawa tace “Granny!”

Juyawa tayi da k’arfi tayi azamar b’allawa a guje tana sake cika gidan da sautin siririyar muryarta tana kiran “Granyyyyyyyy!”

Tako d’aya yayi ya isa gareta ya kuma rik’ota jikinshi, cike da kulawa yace “Please Sarah kar kiyi gudu, tafi a hankali, muje mu duba.”

Fincikewa tayi a hassale ta kalleshi tace “Waye kai da zaka fad’a min abinda zanyi?”

Da gudu kam ta wuce amma saida ya rintse idonshi yana rakata da addua’r Allah ya kaita lafiya, da sauri kowa ya nufi d’akin da Kakar take, Sarah na zuwa ta tura k’ofar d’akin da k’arfi tana sake kiran sunanta. Kwance ta hangeta amma idonta a bud’e suke a kakkafe suna kallon sama, zanin rufar da wanda ke kan gadon duk ya turmushe kamar an d’anyi kokawa, ga kuma jinin dake fita ta hancinta.

Wata ihu ta sake tartsawa cikin kiran sunanta ta tafi a guje ta haye kan gadon ta rumgumota tana jijjigawa da kiran sunan “Granny, please granny karki tafi ki barni kema, A’a dan Allah ki tashi kar ki min haka.”

Juyawa tayi ta kalli tarin mutanen dake tsaye tace “Ku kira motar asibiti mana.”

Wani daga ciki ne ya fita ita kuma ta shiga jijjiga Kaka, duka mutanen wurin sun sadak’ar bata raye, a hankali Sandra ta matso kusanta ta dafa kafad’arta, tana jin haka ta saki Kaka ta juya ta fad’a kan cikin Sandra ta fashe da kuka tana fad’in “Dan Allah Sandra karki bari ta tafi, ki ce ta tashi karta barni ita ma, me yasa zasu dinga barina d’aya bayan d’aya? Ki fad’a mata ta tashi karta sake mayar dani marainiya, ita kad’ai gare ni yanzu fa.”

Daddab’a ta shiga yi tana bata hak’uri duk jikin kowa ya mutu, d’ago kanta ta sake yi ta kuma kallon Kaka ta shiga shafa fuskarta tana sako da hawaye, babu wanda ya sake magana har suka ji jiniyar ambulance a cikin gidan, ba jimawa ma’aikatan suka shigo da gadon d’aukar marasa lafiya, sauka tayi daga kan gadon suka samu damar d’aukarta suka fita inda suka rufa musu baya.

Kowa ya fita a d’akin amma banda shi daya shiga dube dube yana tunanin al’amarin, girgiza kai kawai yayi ya fita shima yana cije leb’en k’asa, yana fitowa an sakata motar Sarah na kiciniyar shiga ita ma, Sandra ya ma alama data rik’eta karta barta ta tafi tare dasu, matsawa Sandra tayi ta rik’eta tana fad’in “Kiyi hak’uri princess su tafi sai kije a mota tare da driver.”

Cikin d’aga murya tace “To a kira drivern mana.”

“To.” Sandra ta fad’a tana ma cikin s茅curit茅 d’in alama da ido, motar ta bi da kallo sai sintiri take ta kasa tsayawa, mota na tsayawa gabanta tayi saurin bud’awa ta shiga tare da Sandra da Joseph a gaba suka d’auki hanya. Saida kowa ya watse daga wurin har Farha ta shiga ciki sannan ya shiga mota shima ya bi bayansu, asibitin da tafi kusa da nan aka kaita a gaggauce, da gudu ita ma ta shiga ciki, a tak’aice dai likitocin sun fad’a musu bata da rai, Salahadeen ne ya cike duk wasu takardu tare da cewa da safe zasu karb’i gawar.

Gaba d’aya sai yaji baya k’aunar ganinta a yanayin da take ciki yanzun, tunda aka fad’i mutuwar sai tayi sakai da ita kamar ba mutuwa aka fad’a mata ba, ta daina hawaye bare k’arajin kuka, yanzu haka tsaye take jingine a bango tana kallon Sandra da Joseph da sukayi lak’was kansu a k’asa, d’agowa tayi tana sauke ajiyar zuciya, wani murmushi ta sakar musu tace “Mu tafi ko, tunda ita ma ta tafi me zamu jira anan?”

Kama hanya tayi da sauri suka bi bayanta cike da tausayinta, su suka fi kowa saninta dan tun tana yarinya suke wa Abhi aiki, ta rasa uwa tun tana k’arama, ta tashi cikin gata da kulawa da soyayyar mahaifi, duk wata zirga zirga tashi ta aiki da kasuwanci tare da ita yake yinshi, tun yana d’aukarta a kafad’arshi har ya fara kama hannunta tana takawa da k’afafunta, a shekarunta madadin ta samu kanta cikin yara yan uwanta tana wasa saita samu kanta tare da mahaifinta, a makaranta kawai take samun walwala irin ta yara, tun tana shekara bakwai take iya saka baki a lamarin kasuwancin mahaifinta, k’wazonta yasa yafi karkatar da hankalinta kan kasuwanci ita ma, wanda daga baya ya samu d’aukaka da kuma ci gaba ta dalilinta, bata cin abinci ba tare dashi ba, shine abokinta k’awarta kuma uwa da uba a gareta, bata san kowa da komai ba sai Abhi, Abhi, amma shima a k’arshe haka ya tafi ya barta.

Duk sun shiga motar driver zai shiga Salahadeen ya dakatar dashi ya nuna mishi tashi motar, wucewa yayi shi kuma ya shiga nan ya jasu, tafiya suke babu mai magana kowa da abinda ke ranshi, ba tare data kalli Sandra da suke tare ba a baya tace “Ku sanar da Daniel (yaya ne ga Kaka) mutuwar yer uwarshi.”

Joseph ne ya amsa da to, ajiyar zuciya ta sauke ta jingina sosai ta rufe idonta, a hankali murya a matuk’ar tausashe tace “Dama sun haifeni ne dan na birne gawawwakinsu.”

Da sauri ya taka birki ya juyo zaiyi magana sai kuma Sandra ta rigashi fad’in “Haba princess, ki yarda da k’addara mana, kin mata kowane mumuni tare yake da jarabawarshi, duk wanda ya amsa sunan musulmi to dole ya fuskanci jarabawa daga wajen ubangijinshi, ita kanta jarabawar ma’auni ne na tantance imaninmu, idan kikayi hak’uri kika ci jarabawarki saiki samu lada mai yawa, amma dan Allah princess ki daina magana iri haka karki kwab’ar da ladanki da wannan maganganun, in baki manta ba dalilin halayenki ne har suka ja ra’ayinmu muka shiga addinin nan, idan kina fad’in haka a gabanmu ya kike so muyi?”

Kallonta tayi tana zubo da hawaye tace “Na daina daga yanzu, ba zan sake ba.”

Kamo hannunta tayi ta d’ora kan k’irjinta cikin raunin murya sosai tace “Sai dai kuma ina jin zafi sosai anan, ciwo nake ji Sandra a k’irji na, kamar an d’ora min dutse nake jina, wanda zan fad’awa abinda ke damuna nake so, ina ma zan ga Ummina a yanzu dana kwanta saman k’afarta na fad’a mata abinda nake ji.”

Jawo kanta Sandra tayi ta d’ora a k’irjinta tana daddab’ata, tunda yaji abinda tace yaji shima kamar an jefa mishi wani murgujejen dutsi a k’irji, wasu k’walla yaji ta cika mishi ido, yaji yana so ya rarrasheta amma ya lura cizgashi kawai take yau d’in. Haka ya ci gaba da tafiya da niyyar gobe saiya d’auketa sun je asibiti an duba lafiyarta da abinda ke cikinta ko bata so, suna isa gida d’akinta ta wuce ta kwanta kan gado, amma ba bacci tayi ba sai tunanin wannan mutuwa ta Kaka, lafiya lau suka rabu amma kawai…Dafe kanta tayi kawai tana sako siraren hawaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button