NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

D’agowa tayi daga jikinshi tana kallonshi cikin fitar da kowace kalma a wahalce tace “Abhi, wani jaki na had’u dashi a wurin party, ni kawai ka kashe shi Abhi.”

D’an zaro ido yayi ya kalleta yace “Jaki? Waye shi to? Me ya had’aki dashi?”

Saida tayi kamar zata dafe kanta tace “Ni ni, i don’t know, kawai ka kashe min shi Abhi, ya saka min ciwon kai.”

Da daluwa ya kalleta yace “Kin gani ko? Shiyasa nake so ki dinga fita da s茅curit茅, amma ba kya so kin kasa fahimta ta.”

Lumshe ido tayi alamar gajiya da zancen tace “Abhi…”

Da sauri ya dafa kanta yace “Ok i’m quiet, get it inside to take bath, right?”

A kasalance ta wuce tana fad’in “Karka manta fa Abhi.”

Jinjina kai yayi yace “Don’t worry princess, let me handle thi’s.”

Bya bye ta masa tana fad’in “Luv u.”

“Luv u too.” Ya fad’a yana kallonta har ta shige ta wata k’ofar da zata sadata da nata falon zuwa d’akin baccinta.

Juyawa yayi zai d’auki wayarshi dan ya kira sai kuma yaga kiran wanda zai kira ya shigo, d’auka yayi yace “Ya akayi ka bar min ‘yata ta taho ita kad’ai? Ka manta da aikin dana baka ne ko me? SALAHADEEN ka manta da al’amarin yarinyata ne?”

Cike da kasala guy ya amsa da “Ban manta ba, ni na dawo da ita gida, bata fad’a maka ba?”

Wani murmushi ya saki yace “Oho! Kai ne jakin dama da take fad’a? Ta fad’a min ka saka mata ciwon kai, me yasa?”

Saida ya d’an zuk’i sigarin dake hannunshi kafin yace “Ban mata komai ba, ita ce dai ta saka min ciwon kan da masifa.”

D’an d’aga murya yayi yace ” ‘Yar ta wa? Salah SARAH ce kale cewa ta saka maka ciwon kai?”

A d’an saib’ance yace “Sorry sir.”

Ajiyar zuciya ya d’an sauke yace “Gobe ka zo ka same ni akwai aikin da zan saka ka.”

“Ok, see tomorrow.” Kashe wayar yayi ya k’arasa nashi masaukin.

Washe gari da safe ko da ta tashi wajen motsa jiki ta fara tafiya, har ta dawo ta ga motocin Abhi basu fita ba alamar yana nan, ko da ta shigo falon taga d’aya daga cikin wanda suke fita tare tace “Abhi?”

Da ladabi yace “Yana tare da bak’o.”

Kai tsaye ta nufin zai sadata da d’akin karatunshi, tana zuwa bud’a k’ofar tayi ta shiga, d’agowa duka sukayi suka kalleta, da sauri Shakoor ya kalli bindigar da Salahadeen ya aje akan teburin, lumshe ido yayi da tunanin abinda zai fad’a mata ta yarda dashi.

Da mamaki take takowa bata damu da wandon dake jikinta ba iya cinyarta na gudu da riga mai dogayen hannu, sai gashinta data d’aure tamau tana rik’e da yar robar ruwa da earpeas a kunnenta, saida ta tsaya kusa da Abhinta tana kallon bindigar tace “Abhi, waye wannan? Me ya had’aka dashi? Ka sanshi ne dama?”

Satar kallon Salahadeen yayi ya kalleta da murmushi yace “…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 03:54 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

              *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

SADAUKARWA GA

          _DUK_

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

Talla

        *Talla*

                    *Talla*

Ina kuke jigajigen masoya na? To ku garzayo ga sabo na dawo dashi, domin k’wamushe karatun wannan littafi zaku biyan mafi k’aranci kud’i ne, gareku yan k’asata Niger zaku iya tura 500 f cfa ta Orange money(ba chap chap ba yan uwa, orange money dan karka tura ta chap chap amma zaku iya tura kati) akan wannan lambar 91-71-28-22 ko kuma wannan lambar MOOV FLOOZ 84-55-55-56 (moov flooz ba chap chap ba amma zaku iya tura kati) . Ga yan uwa Nigeria kuma sai su tura naira 300 ta wannan account d’in 0004309211 Bank name Jaiz, ko kuma ku tura kati ta wannan lambar 806-559-0797, yau dai a yanzu zan ga adadin mabiya na wanda a shirye suke da kud’insu ma, (zan ci kaza fa).

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               3锔忊儯

“Kin san shi ne Sarah?”

Da sauri tace “Yeah, Abhi shine wanda nake fad’a maka jiya ya addabe ni, amma me yake yi wajenka?”

Kafin ya bata amsa kuma tayi tsal ta kalli bindigar tace “Abhi thi’s gun, ta waye a cikinku?”

Kallonta yayi da alamar rashin gaskiya yace “Tashi ce.”

Kallon salah tayi wanda idonshi ke kallon teburin shi ko a jikinshi tace “Abhi police ne?”

Da sauri yace mata “Eh, police ne, ai ya fad’a min ma jiya ya kawo ki gida.”

Kallonshi tayi sosai irin kallon son gano gaskiya, sai dai bata ga wani abu daya nuna hakan a kayan jikinshi ba, dan kaya ne irin na gayu a jikinshi, dama jiya ne da suka had’u saita yarda, dafa kafad’ar Abhi tayi tace “Abhi me ya had’aka dashi to? Me ya kawo shi nan?”

D’aga kai yayi ya kalleta irin kallon nan da ita tasan manufarshi, d’an turo baki tayi tace “Sorry.”

Takawa tayi zata fita tana kallon Salahadeen da har yanzu bai kalleta ba, tana fita suka kalli juna Shakoor ya d’auki bindigar ya mik’a mishi yace “Kana sakaci sosai Salah, ka sani bana so Sarah ta shiga shakku ko tunanin wani abu a game dani.”

D’an d’agowa yayi daga kan kujerar yace “Me yasa ka kira ni nan?”

Gyara zama shi ma yayi yace “Akwai wani tsohon campagnin tumatir dana gani kuma ina so, nayi magana da mammalakinshi amma sun ce ba zasu sayar ba, wai bashi zasu nema a wurin gwamnati dan su tayar da shi.”

Saida ya jingina kan kujerar yana d’an juyawa yace “Takardun masana’antar nake da sa hannunsu, ya rage naka kasan yanda za kayi.”

Wani murmushi yayi yace “That’s all?”

“Yeah.” Ya fad’a yana kallonshi, mik’ewa yayi yana saka bindigarshi bayan rigarshi ya d’auki makullin mota yace “Gobe warhaka zan kawo maka takardun.”

Murmushi yayi mai tsada yace “I know u, see u.”

Fita yayi ba tare da shakku ko d’ar na aikin daya saka shi ba, shekara shida kenan daya taimake shi sanda wasu rebel suka tare su a hanya, an bada wuta sosai tsakanin yan fashin da masu tsaronshi, a garin gudun tsira ne ya had’u da Salahadeen wanda lokacin makarantar da yake sun kore shi saboda rashin ji shi da abokanshi, ga rayuwar da tsada abinda zai ci ma ya fara bashi wahala, sai kawai suka jone ya d’ora kan mummunan tafarkin da yafi k’arfin rashin jin shi na baya, ya zama kamar karan farautarshi, duk wani mummunan aikin da zai kauce doka shi yake sawa akai, ya bud’e mishi bakin aljihunshi yana sakar masa kud’i sosai. Sai dai kuma akwai amana tsakaninsu da yarda, duk da baya yarda ya zo gidanshi ko su had’u cikin mutane, suna komai da taka tsantsan, baya da tsoro ko sarau, duk abinda ya saka shi yi yake komai had’arinshi, sai dai kisa ne shi kanshi yace ba zai tab’a kashe mutum ba da hannunshi, amma zai mishi ko menene.

Yanzu ma ya saka shi bibiyar Sarah ne saboda ta dage ita bata son fita da masu tsaro, shiyasa yasa shi bibiyarta ba tare data sani ba.

Ta shirya ta fito zata fita ta samu mahaifinta yana waya, har zata fice yayi saurin cewa “Sarah.”

Dawowa tayi ta tsaya tana kallonshi yace “Ki jira kad’an yanzu d’an abokina zai zo ku gaisa saiki tafi.”

Cikin shagwab’a tace “Abhi.”

Da kulawa yace “S’il te pla卯t.”

“Ok.” Ta fad’a tana aje jakarta ta fita farfajiyar gidan, bata fi minti biyu ba da fita mota ta sanyo kai gidan, saida masu tsaron k’ofa suka basu dama kafin suka k’araso, gabanta motar ta tsaya wani saurayi ya fito, kallon juna sukayi inda ya bata hannu yana fad’in “Sarah?”

Jinjina kai tayi tace “Yes.”

Sake jinjina hannayensu yayi yace “Nice to meet u.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button