NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               7锔忊儯

“Shugaba an samu wata yar matsal…”

Da sauri shugaban ya tare shi da fad’in “Karka fara kira mana matsala anan wurin, bamu santa kuma bamu san mu santa, Shakoor karka ce zaka karya mana dokar k’ungiyarmu, ba’a tab’a yi ba kuma ba za’a fara a kan ka ba, ka cika mana alk’awarinmu indai kana so ka tsira da rayuwarka kaima.”

Da sauri ya kalleshi yace “Shugaba ka fahimce ni, gaskiya nake fad’a maka, wani yaro ne ya sace ta kuma n…”

Kabeer ne yace “Ya sace ta ko kasa ya saceta? Shakoor duk anan wa ya maka kama da wawa da zaka zauna ka raina masa hankali? Mu mahaukata ne kenan da muka d’auko iyalenmu muka kawosu a kowace shekara aka sha jininsu.”

Shigaban ne ya daka musu tsawa da cewa “Ya isa haka, duk inda take ma zamu ganota.”

Ko da ya fad’a ya kalli b’angaren hagu d’inshi dake rufe da jan k’yalle, cikin mintin da bai wuce d’aya ba Sarah ta bayyana a cikin yadin, ta kasa bacci tana zaune tsakiyar katifar sai fad’a take da french tana kallon mama na sallahr asuba.

Da k’arfi tasa hannayenta ta shiga tumurmusa gashin kanta cike da jin haushi tana kukan shagwab’a saboda zafin daya addabeta. Da sauri ya tashi tsaye yana kallonta yana fad’in “Sarah, ina ne nan? Ina ne ‘yata take?”

Kallonshi shugaban yayi yace “Kana da zab’i biyu Shakoor, ko dai ka kawo mana ita nan da hannunka, ko kuma mu shanye jininta daga inda take, ka zab’i d’aya daga ciki.”

Da sauri ya kalleshi yace “Zan kawota, zan kawota shugaba, a min afuwa karka tab’a ta yanzu.”

Kallon bangon yayi sai hoton nata ya b’ace yace “Kwana uku gare ka da zaka gabatar mana da ita, inba haka ba zamu sha jininta daga can, kai kuma zaka k’ask’ance ka lalace.”

Kl da ya gama fad’a ya b’ace a tsayen da yake, suma duk b’acewar sukayi inda aka bar Shakoor da zulumi, to me kenan Salahadeen yayi? bai rintsa ba yana tunanin ina ne ma yake, ya dai fad’a masa shima na Niger ne kuma maradi, amma a ina wace unguwa duk bai sani ba, alami kuma sun nuna yana niger ne tare da Sarah.

Ko da gari ya waye masaukin su Salahadeen ya kai ziyara, ko Richard bai samu ba bare Salahadeen, tuni abun duniya ya fara isarshi ga police da suka dame shi duk motsinshi suna tare dashi, bincike kawai suke da bin diddigi na son ganota, a garin binciken ne suka gano ta fita waje kuma da passeport d’inta, gari da taje da wanda suka fita tare duk saida aka basu bayanai.

A lokacin da aka fad’a ma Shakoor ya girgiza, ya tambayi kanshi me yasa Salahadeen zai mishi haka? Ya zai fita da yarinyar da bata tab’a giftawa ta africa ba? Wane hali take ciki yanzu sakamakon riskar kanta da tayi a sabuwar duniya? Kallon babban jami’in yayi sanda ya tambaye shi shin yasan wani abu game da wanda suka tafi taren? Saida ya saita nutsuwatshi yace “Saurayinta ne.”

Bai mishi gardama ba dan a hoton vid茅on s茅curit茅 camera ma da suka gani yana gaba tana biyarsa ne, amma sai yace “Me yasa suka tafi babu saninka? Kuma me yasa bata tafi da ko wayarta ba?”

Kallonshi yayi cikin nutsuwa yace “Kullum tana min k’orafi na kaita wajen dangi na, watak’ila ta tafi ne dan ta had’u dasu.”

Gira ya d’aga tare da cewa “Duk da haka, zamuyi magana da a had’a mu da jami’an dake can su kama mana su.”

Da sauri yace “A’a ku barshi, ku barshi ni zanje da kaina da dawo da ‘yata.”

Kallonshi yayi sosai kafin yace “Zaka iya tafiya, amma idonmu na kanka, zamu ci gaba da rik’e al’amarin a hannunmu har ka dawo da ita lafiya.”

Jinjina kai yayi ya mik’e ya fita, daga nan tare da dreba da masu tsaronshi dake wasu motocin airport suka wuce, bayan shekara goma yau ya shiga jirgin da zai kaishi k’asarshi wacce ba dan dalilin zuciyarsa dake nan ba shi da garin har abada.

A wajen Sarah kuma yanda ta ga rana haka ta ga dare, mama dake zaune kan sallaya saidai ta juya ta kalleta, ta mik’e tsaye akan katifar ta koma ta zauna tayi durk’ushe, ta rasa me ke mata dad’i a k’arshe ihu ta dinga zabgawa tana fad’in “Mr. ka zo ka mayar dani gidan, mr.”

Mik’ewa mama tayi taje kusa da ita ta sunkuya tana kallonta tace “Yarinya ba kuwa za kiyi ba, ki dinga fad’in inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un idan wani abun ne ya dame ki.”

Mik’ewa tayi ta nunata da yatsa a harshen french tana fad’in “Ke rabu dani, ke ce kika ce ya tafi ya barni anan ko, idan baki sashi ya dawo ya mayar dani ba sai na sa Abhi ya yanka min ke.”

Duk da dai ba fahimtarta take ba amma tasan babu ladabi a cikin abinda take fad’a mata, juyawa tayi ta koma kan tappi tana fad’in “Allah ya shiryaki, da yanzu fa kin zama matacciya, kina nan kina mana ihu na hauka.”

Da sauri Sarah ta sauko daga katifar ta tsaya gaban mama tana mata alama da hannu tana fad’in “Ki tashi ki kunna min ac na gaji da zafin nan, ba zan iya k’ara minti d’aya a wurin nan ba ki tashi ki fitar dani waje.”

D’aga kai mama tayi ta kalleta ita ma ta shiga kwatanta mata da hannu tana fad’in “Ki bari Salahadeen ya dawo sai ki fad’a masa abinda kike so.”

Yanau kam ta gane me tace dan haka ita ma tace “Ba zan jira shi ba, ni ki bani ruwa nayi wanka.”

K’ura mata ido mama tayi saita dinga nuna mata da hannu tana fad’in “Wanka, wanka nake so, ina zanyi?”

Da sauri mama ta mik’e tana fad’in “Kaga ja’ira, ke da kina jin hausar ma kike min wannan fitsarar.”

Nuna ta tayi da yatsa cikin turanci tana fad’in “Karki min hauka mana, na fad’a miki wanka nake so nayi ko naji sauk’in wannan zafin mutuwar.”

Salahadeen ne ya shigo da sauri yana fad’in “Ke uwar tawa kike nunawa da yatsa?”

Tana had’a ido dashi ta rik’e k’ugu tace “Mr. i’m hungry.”

Sorora ya kalleta dan ya mata da maganar abinci, zai iya cewa tun a jirgi data ci wani d’an musakin abinci bai k’ara ganin ko tuwa tasha ba, ganin bai bata amsa ba sai tace “Wanka fa nake so nayi mr., ka san yanda za kayi dani na gaji.”

Kafin yayi magana ta ci gaba da cewa “Ina so nayi wanka, zafi nake ji ina so nasha iska, na gaji na gaji ni mr.”

Kallon mama tayi tace “Wai me take fad’a ne haka take ta fad’a?”

Jiki a sanyaye yace “Wanka take so tayi mama, kuma wai zafi take ji kuma tana jin yunwa.”

Da sauri ta mik’e daga kan sallayar tana fad’in “Yo data fad’a ai da tuni an wuce wurin, wanka kawai dai naji d’azu ta ambata.”

Kallonshi tayi da kyau tace “Ce ta fito farfajiyar gida, wane yanayi ne yafi na asuba dad’i a gurin bawa? Yanzu bari naje na fara kawo mata kunu, saina sa Iffa ta d’ora mana d’umamen tuwo, idan ta gama sai tayi wankan.”

Bata jira me zaice ba ta fice, da kallo ya bi mama bakinshi ya kasa furta kalma ko d’aya, d’umame da kunu? Sarah Shakoor Aghali? Yar billionnaire ? Lallai mama.

Kallonta yayi yace “Taho muje.”

Binsa tayi a baya suka fita tsakar gidan, mama ta gani tana kwalho mata kunu a roba da ludayi, saida ta kawo mata ta motsa ta kalli Salahadeen tace “Ko na kawo mata sukari?”

Da mamaki ya bud’a baki yace “Mama wane sukari kuma, shi kanshi kun…”

Bata barshi ya k’arasa ba tace “Ai ko ta raba kanta da shan kunu da sukari, nima dai haka nake shan shi.”

Mik’a mata robar tayi tace “Shanye ki bani robar.”

Kallon robar tayi ta kalli mama ta kalleshi, d’auke idonshi yayi daga kallonta hakan yasa ta kalli mama ta nuna kanta tace “Ni? Me zanyi da wannan?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button