NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

A ladabce ta amsa mata da “Eh matar dai tana ciki, amma mijin nata dai…”

Katseta Sarah tayi da fad’in “She’s my husband too, ku girmama shi kamar yanda kuke girmamani, mijina ne kuma uban d’ana, kin fahimta?”

Ma’aikatan ukun dake ta gyara wajen cin abinci suka amsa mata da “Sorry ma’am.”

Mayar da hankalinta tayi kan wayar tana gyara zamanta tace “Ki ce su fito nan zamuyi lunch.”

D’aya daga ciki ne ta tafi a sukwane dan isar da sak’on, sanda take duba sak’on da Sajida ta turo mata cewa “Turo min hotonki yer uwa?” Tana karantawa ta shiga kiciniyar neman hoton da zata tura mata, kasancewarta bata cika son wannan d’aukar hoton ba, da k’yar ta samu hotonta inda ta d’auka a cikin aji sanda tana makaranta, tura mata tayi kafin ita ma ta tura mata sak’o kamar haka “Sister hoton dake kan profil d’inki familynki ne?”

Ba jimawa ta maido mata da cewa “Eh, familyna ne, amma mahaifiyarmu ta rasu shekara uku data wuce, yanzu muna tare da kakarmu ne wacce ta haifi Abbanmu.”

Cike da jimami tace “Ayya sannu, kinga kuwa Abbanki yana kama da Abhina sosai.”

Maido mata tayi da fad’in “A gaskiya nima na buk’aci hotonki ne dan na nunawa Abbana, tun ranar dana fara ganinki nake jin wani abu a tare dake, kina kama sosai da mahaifina da kuma k’anninshi.”

Cikin murmushi ta tura mata “Kina ganin kenan zamu iya zama yan uwa ne mu?”

“Me zai hana kuwa? Ke ina Abhinki?”

Cike da jimami tace “Abhina ya rasu wata biyar da suka wue.”

Sosai ta jajanta mata ta mishi addu’a da ita ma Allah ya bata hak’urin rashi, turo mata tayi “K’anin mahaifina ya jima da barin gida ya fara aiki a k’asar Tha茂lande, amma daga k’arshe ya koma can da zama ya daina zuwa nan gida, bansan asalin me ya faru ba amma dai kamar akwai wani abu dake faruwa ko ya faru wanda ya hana shi dawowar, idan ba damuwa sis zaki iya fad’a min wani abu game da Abhinki?”

Wani murmushi Sarah tayi sosai tana jin bugun zuciyarta na harbawa da sauri sosai, ta gyara zama tana mayar mata taji anyi sallama wurin. D’ago kai tayi ta kallesu, suma ita suke kallo tunda suka taho wajen har suka k’araso, zaune sukayi kan kujerun yana kallonta yace “Priness ya jikinki?”

Haka kawai ta tsinci kanta da sakin murmushi tace “Naji sauk’i ma Sla, ina cikin farin ciki yanzu haka.”

Da gangan ya matso da kujerarshi kusanta sosai ya d’ora hannunshi kan table d’in yana kallon fuskarta yace “Fad’a min me ya faru?”

Kallonshi tayi ita ma tana dariya tace “Ina ganin na kusa gano yan uwan Abhina.”

Da mamaki mai d’auke da farin ciki yace “Da gaske? Gaskiya naji dad’i sosai, suma acan Agadez suke ko kuma anan?”

Cikin sauke ajiyar zuciya tace “Agadez suke, amma akwai guda dake karatu a mekka ita ma, ina fatan abinda nake tunani ya zama gaskiya.”

Kaka ce ta amsa da “To kiyi magana da ita maan, ko ta had’aki da mahaifinta ita sai kiji komai.”

Kallonta tayi tace “Zanyi haka granny, yanzu ma muna kan magana da ita ne.”

Saida ya gyara zamanshi ya d’auki cokali mai yatsu yana kallonta yace “Ki tura min lambarta na gani.”

Kallonshi tayi ta tambayi kanta ina ta samu lambarshi? Da tana da ita ai da bata je garinshi ba har wannan matar ta kusa kasheta, shiru kawai tayi dan karta nuna musu bata da lambar, kallon Farha tayi dake kallon Salahadeen tayi zugum, gyara zama tayi ita ma ta d’auki cokali mai yatsu tana kallon Farha tace “Bismillah, ki ci abinci.”

Girgiza kai tayi alamar a’a, cikin hausarta mai dad’in ji a kunne tace “Me zaki iya ci sai a dafa miki?”

Girgiza kai ta sake yi hakan yasa Salahadeen kallonta yana tauna abincinshi yace “Ki fad’a mana abinda kike so, ai ba ita zata girka ba umarni zata bayar, kinsan fa su mugun girmama bak’o garesu, yanzu nan tana iya zubar da hawaye duk taji babu dad’i akan rashin fad’an abinda kike so.”

Tunda ya fara magana take kallonshi, har ga Allah ji take kamar ta fashe da kuka saboda wani nauyi da taji zuciyarta ta mata duk bata jin dad’in yanayin, kawar da kanta tayi hakan yasa Sarah kallon wata ma’aikaciyar dake tsaye gefe tace “Bani biro da takarda.”

Juyawa tayi da sauri ta koma ciki bayan wasu mintoci ta dawo ta aje mata gabanta, rubutu tayi wasu abubuwan buk’ata kafin ta mik’a mata tace “Ki kaiwa Sandra ta kula da komai.”

Karb’a tayi da ladabi ta juya ta tafi, ci gaba sukayi da cin abincinsu amma banda Farha data tabbatar ba zata iya ci ba ko da ta fara ma. Kaka ce ta fara mik’ewa tsaye ta kalleta tace “Zaki koma ciki ne ko na barki anan?”

Kallonta tayi tace “Kije granny zan shigo.” Juyawa tayi ta nufi ciki, ganin haka yasa shi kallonsu dukansu ya jingina a kujerar yace “Ku shirya anjima akwai dinner dana shirya mana.”

Aje cokalinta tayi tace “Akan me?” Ba tare daya kalleta ba yace “Ina farin ciki duka iyalina suna tare dani.”

Wata yar dariya tayi kawai ta shareshi ta d’auki wayarta, mik’ewa yayi zai bar wurin ta d’ago kanta tace “Wane kaya ka zab’awa fitar? Ko duk kalar da muka saka tayi?”

Juyowa yayi yace “Kin fini sanin kalar data dace da soyayya ai.”

Ita kam dariya ta sake bushewa da ita har da aje wauarta a harshen turanci tace “Sla, me yasa kake hakane? Ko dai matarka kake so ka tunzura?”

Kallon Farha yayi sai yaga hankalin na kan wasu flowers tana kallo alamar bata ji ba bare tasan anyi, murmushi yayi kawai ya juya ya tafiyarshi, ita ma kallon Farha tayi tana sale d’aukar wayarta tana ci gaba da dariya.

Ganin ya tafi ya barta saita kasa motsawa daga wurin, ita kuma Sarah ta koma kan hirarsu da Sajida ta bata amsar d’azu da cewa “Sister Abhina bai fad’a min komai dangane da familynshi ba, abu biyu yake fad’a min shine garinsu Agadez ne, sannan yan uwanshi sun juya mishi baya, dan haka yake fad’a min na manta dasu dan ba zasu tab’a so na ba zasu k’yamace, shine kawai abinda na sani.”

Maido mata tayi da cewa “Sai naji kamar ke yar kanin Abbana ce, amma inba damuwa zan iya had’aki da Abbana kuyi magana?”

Da farin ciki tace “Zanyi farin ciki sosai idan kika min haka, amma d’azu naji kince mahaifiyar Abbanku ko? Zaki iya turo min hotonta?”

Maido mata tayi da cewa “Ba damuwa, bari ki ganta kamarku d’aya.”

Dariya tayi da tunanin tsokanarta take hakan yasa tace mata “Da alama tana da rigima da shagwab’a ko? Dan su nafi k’warewa akansu.”

Dariya ta turo mata tace “Ai karma kiga salon nata rigimar, na tabbata ita kika biyo.”

Kafin ta sake cewa wani abuta turo mata hoton tsohuwar, kallonta ta shiga yi da wani tattausan murmushi a fuskarta, tabbas ba dan tsufa ba sai tace tsohuwar kamar tayi kakinta ta tofar, cikin sauri ta hango Abhinta a fuskar tsohuwar, saidai yanda taga yanayinta a hoton zai tabbatar maka lallai za ayi rigimammiya mafad’aciya, dariya tayi kawai ta tura mata da “Amma dai tana da masifa ko?”

Ajiyar zuciya ta sauke ta maido mata da “Ai karma ki tona ki gani, duk da bansan asalin me ya faru tsakanin dangi da Abhinki ba, amma dai kamar suna zargin dukiyarshi ne, kullum tsohuwar nan da kika gani saita tsinewa duka dangi tana fad’in su suka rabata da d’anta dan sunga yayi kud’i, tana ganin laifin mijinta marigayi da cewa shiya zugasu duk suka tsani d’anta yanzu gashi ya daina zuwa inda take.”

Maida mata tayi da cewa “Da alama tana son shi, ya zatayi idan taji rasuwarshi?”

Maido mata tayi da cewa “Gaskiya zata ji ba dad’i, kullum maganarta akan shi ne da k’orafin bata ga d’anshi ko ‘yarshi ba an rabata dashi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button