NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Gyara musu yayi suka shigo sai kuma ya tsaya k’arewa k’ofofin kallo da mutane ke fitowa da gudu gudu wasu harda lema, kamar daga sararin samaniya sai kuwa ya hangi yar doguwa fara siririya a cikin farar doguwar riga tas da farin beby hijab. Kawar da kanshi yayi tare da sakin wani basaraken murmushi daya tabbatar daga zuciyarshi ne ya fito, danna hasken motar yayi hakan yasa shi haske mata gaba d’aya ido, hannu tasa ta kare fuskarta nan ne ya hangi jajayen yatsunta data rufe kusan kashi d’aya na kaso ukun su da lalle harda akaihunta.

Tayar da motar yayi ganin ta nufi k’ofar fita ba tare da ganin iskan nan da ake ba da kuma ruwa, odar daya mata ce tasa ta kauce mishi a hanya ba tare data juyowa ba, saida ya tsaya daf da ita ya sauke gilashin motar yace “Muje ko.”

Cikin rurrufe ido saboda iska da ake ta kalli inda taji maganar wacce ta haddasa mata fad’uwar gaba, bugun zuciyarta ne taji ya sake ninkuwa kamar zata fito mata saboda sauri, da sauri ta zagaya ta koma mazaunin mai zaman banza ta bud’a ta shiga, tana rufewa sai komai yayi shiru ganin hargowar iska da saukar ruwa kake ake ta madubi.

Banda numfashi babu abinda ke fita ka rantse kurame ne ko basu tab’a ganin masu kama da junansu ba, cikin wata dakakkiyar murya ta shan k’amshi ba tare daya kalli inda take ba yace “Me ya kawoki nan?”

Wani wawan kallo ta masa tace “Ya akayi kasan zan zo har ka zo d’aukata?”

Gyara zaman kanshi kawai yayi kamar baiji me tace ba bare ya bata amsa, cikin hassala tace “Bibiyata kake malam?”

Ba tare daya kalleta ba yace “Da bana bibiyarki da yanzu kina tsaye bakin titi.”

Da k’arfi tace “Sai me to? Zan rasa abun hawa ne?”

A dak’ile yace “Idan kin hau kice masa ya kaiki ina?”

Hararen gefen ido ta mishi dan ba tayi wannan tunanin ba ma ko kad’an, gyara zamanta tayi ta matse k’afafunta ta dafe kanta da hannaye biyu tana so tasan ta inda zata fara, saida ta sauke wasu manya manyan numfashi kafin ta kalleshi tace “Gurinka na zo muyi magana, zaka iya tsayawa anan?”

Shi kanshi yana son sanin meke faruwa dan haka bai mata musu ba, amma bai kalli inda take ba sai wani cije fuska da yake, wata ajiyar zuciyar ta sake saukewa ba tare data kalleshi ba tace “Yau a makaranta ne aka tabbatar min ina da ciki.”

Da sauri ya kalleta cikin wani irin yanayi da shi kanshi baisan ya kalleta dashi ba, ciki? Ciki ne da ita yanzu haka? Samun kanshi yayi da k’urawa cikin nata ido duk da a zaune take baya iya gane komai, nashi ne kenan? Shiyasa har tayi tattaki ta fad’a masa, hakan na nufi ta ci gaba da tsare kanta da mutumcinshi har zuwa yanzu, tunda shi shaida ne akan tabbacin nagartar budurcinta, shi ya fara bud’e wannan hanyar hakan ya k’ara damfarar mata da ita a cikin birnin zuciyarshi, ashe ta wannan abun daya faru har rabo ya shiga tsakani, hakan fa wani babban alamu da ubangiji ke nuna musu akwai wani babban al’amari da zai faru ke yake ma faruwa a tsakaninsu. Ta wani fanni kuma saiya samu kanshi da sakin murmushi, Sarah da ciki? Lallai za’a sha dambarwa da ita kafin wajen shiririta ta zubar mishi da kaya, Mama ma zatayi matuk’ar farin ciki idan taji yar amanarta na d’auke da cikinshi wanda hakan zai basu mamaki dan basu san ta inda akayi ba, sai dai ta b’angaren Farha kuma zai iya fuskantar matsala, zaiyi fatan Allah ya bata ita ma shikenan sai ayi 1/1.

Gam ya lik’e idonshi tare da had’e labb’an k’asa dana sama wuri d’aya, wani irin abu ne yaji yana kurd’awa ta zuciyarshi yana shiga, kallonta yayi sai kawai ya bud’a k’ofar ya fito daga motar, rufe k’ofar yayi ya d’ora hannayenshi saman rufin motar inda ba zata ganshi ba, rufe fuskarshi yayi da tafukan hannu ya fashe da dariya, bud’ewa yayi ya d’aga hannu sama yace “Alhamdulillah Allah nagode maka, Allah nagode maka abisa ni’imomin daka min kuma kake k’ara min.”

Saida ya kimtsa kamar bashi ba ya had’e fuska sannan ya dawo motar ya zauna ba tare daya kalleta ba, kallonshi take ita ta kasa fahimtar ma me yake nufi da yanayinshi, bak’in ciki ne haka ko farin ciki? Sai dai tafi dangantashi da bak’in ciki da labari marar dad’in ji, juya kanta tayi tace “Ka fad’a mana mafita, idan kana so a zubar ne a gask…”

Bata k’arasa maganarta ba saboda bayan hannu da yasa ya bugar mata baki, duk da ba sosai bane amma taji zafi dan bata san me hakan ke nufi ba, kallonshi tayi tace “Me yake damunka ne? Kana hauka ne?”

D’aga mata kai yayi yace”Eh hauka nake, amma fa irin wanda kikeyi, mahaukaciya kawai.”

Tayar da motar yayi ya d’auki hanya ita kuma tana fad’in “Nice mahaukaciyar? Zaka ga mahaukata idan na haife abinda ke ciki, kaga mun zama mu biyu kenan, da ni da kai da abinda muka haifa mu uku kenan.”

Kallonta yayi yace “Ke.”

Kallonshi tayi tana turo baki har yace “An tab’a zubar miki da hak’ora?”

Da sauri taja baya tasa hannu ta rufe bakinta, zuwa lokacin shiru motar ta d’an d’auka kamar ba zasu sake magana ba, a hankali sai kuma ta fashe da kuka tace “Me yasa mr. ka cika son kanka da yawa? Me yasa baka tab’a nemana ba ko da sau d’aya ne? Yanzu gashi ina tare da cikinka ni kaina ban sani ba sai yau, mr. bana so na samu matsala a karatu na ko kad’an, bana so cikin nan ya kawo min cikas a cikin neman ilimi na, sai dai kuma na yarda da k’addara na kuma karb’eta, na tabbata akwai abinda Allah yake nufi dani shiyasa haka ta faru, ba zan iya zubar dashi ba ko da hakan zai sa na mutu, zan kula dashi har lokacin da zan haifeshi, ka sani ba na zo fad’a maka bane dan ina buk’atar wani taimako daga gareka ba, na zo na fad’a maka ne saboda ina so kasan da cewa nan gaba kad’an idan Allah ya nufa zaka zama uba, hakk’inka ne kasan haka shiyasa na zo na fad’a maka.”

Sanda ta gama fad’a yayi daidai da tsayawarshi k’ofar tank’amemen gidan, duk da tsayawar tashi tasa mai gadi fitowa ya bud’e k’ofar amma bai shiga ba sai yayi shiru, a hankali ya kalleta yasa hannunshi na dama ya rik’o hannunta, da sauri ta kalleshi tana jin bugun zuciyarta na k’ara harbawa, kallon fuskarta yayi cikin nutsuwa sosai yace “Nagode da kika sanar dani haka.”

Ta d’auka zai k’ara cewa wani abu sai kawai taga ya saki hannunta ya danna hancin motar ciki, cikin rashin jin dad’i ta wulwula idonta tana kallon gidan da suka shigo. Yana fita ya zagaya ta baya ya d’auki lema a cikin motar sannan ya bud’e mata ta fito, bud’e lemar yayi ya mata rumfa da ita, kallonshi tayi amma sam idonshi ma ba a kanta suke ba, rik’e hannunta yayi ya jata zuwa ciki, suna isa yar k’aramar verendar da babu rufi a samanta kawai ta fita daga cikin lemar ruwa suka fara sauka jikinta.

Ita kanta fa k’uru ce tayi dan bata san saukar ruwan sama a jikinta, suna saka ta zazzab’i mai tsanani idan suka daketa, yana ganin haka da sauri ya fizgo hannunta ya tura k’ofar falon suka shiga, wani irin kallo ya mata mai d’auke da gargad’in kiyi hankali fa da kanki, da hannu ya mata alamar ta biyoshi suje, a k’ofar d’akin Mama suka tsaya ya shiga k’wank’wasawa a hankali, kafin a bud’e k’ofar idonsu suka had’u sai yaga kallonshi take tana dariya, tsaki yayi tare da fad’in “Miye kuma?”

Cikin dariyar tace “Abunda ke faruwa yanzu sak irin wanda ya faru ne sanda ka satoni daga k’asata.”

Nuna mata yatsa yayi a hassale yace “Ke karki sake fad’in na satoki, ni ba satoki nayi ba taimakonki nayi, da banyi haka a waccen ranar ba da yanzu…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button