NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

               5锔忊儯

Ta jima tana jiran shigowar mahaifin nata dan suyi dinner amma shiru, tayi kiranshi kuma bai d’aga ba saita masa uzurin yana busy ne, d’akinta ta koma ta kwanta dan tasan ko tayi bacci ya dawo zai tashe ta, ya sabata bata iya yin break ko dinner ba tare dashi ba, tun tana kallo a matsakaiciyar tvn dake jikin gadonta tana d’an danna wayarta har bacci ya d’auketa.

Dare yayi sosai ya dawo gidan dan baya so ya had’a ido da ita, ko da ya zo aka fad’a mishi bata ci komai ba ya d’auki abinci a plate ya shiga d’akin, bai wani k’wank’wasa k’ofar ko neman izini ba ya shiga, wayarta na saman cikinta gashin kanta ya kusa rufe fuskarta, zanin rufar kuma da alama bata rufa da shi ba sai dogayen k’afafunta farare da suka fito fili, a hankali ya zauna bakin gadon yana kallon fuskarta, ‘yarsa Sarah da yake matuk’ar so ita ce yau yake mata kallon k’arshe, shi kam taya zai iya rayuwa babu ita? A hankali yasa hannunshi ya shafi gashin kanta, da sauri ta d’an zabura ta mik’e zaune, tana had’a ido dashi ta rumgume shi tana fad’in “Abhi.”

Shafa bayanta yayi yace “Na tasheki ko?”

Girgiza kai tayi cikin shagwab’a tace “Abhi me ya tsayar da kai? Kayi late yau.”

Yana ci gaba da shafa kanta yace “Sorry princess.”

Kallonshi tayi tace “Ka ci abinci?”

Da sauri ya d’auko plate d’in daya shigo dashi yana fad’in “Na ci, ke nake so ki ci yanzu an ce baki ci komai ba.”

A hankali ya shiga yanko loma da cokali mai yatsu yana kai wa bakinta, hankali kwance take karb’a inda ta kamo hannayenshi take cire mishi mashete d’in daya rik’e k’arshen hannun farar shemise d’inshi, tank’washe mishi hannayen ta shiga yi hankali kwance tana cin abincin, daga yanda ya ga ta tauna lomar daya saka mata yanzun ya bashi amsar ta k’oshi, yasan ta fiye da yanda yasan yunwar cikinsa, aje plate d’in yayi tare da bata farin ruwa ta kora dashi, ajewa yayi ya kalleta yace “Kwanta kiyi bacci, kina da sammakon tashi gobe.”

Jinjina kai kawai tayi ta bishi da kallo sanda ya mik’e da plate d’in a hannunshi zai fita, tana matuk’ar tausayin mahaifinta a maraicin da yake ciki, dan ya fad’a mata bai sake aure bane saboda ya kula da ita da kuma soyayyar mahaifiyarta, a hankali tana kallon bayanshi tace “Abhi please ina so na ga yan uwanka.”

Da sauri ya juyo ya kalleta da wani irin mamaki, d’an takowa yayi ya dawo baya yana kallonta yace “Why Sarah? Why?”

Da sauri ta sauko daga kan gadon tana rik’o hannunshi tana fad’in “Abhi ina so na had’u dasu, ko sau d’aya ne dan Allah ka kaini na gansu, Abhi kana buk’atar hutu kai ma, idan ka kaini zan iya zama na acan kai kuma sai kayi aure, please Abhi.”

Kallon rashin jin dad’i ya mata yace “Sarah ba zamu iya zuwa inda suke ba.”

Cike da damuwa tace “Why Abhi?”

Saida ya d’an kawar da kanshi yace “Parce que je suis un homme riche.”

Da wani mamaki ta kalleshi tace “Abhi…”

Da sauri yace “Stop Sarah, go to bed.”

Shagwab’e fuska tayi ta juya ta koma kan gadon, yana kallonta har ta ja zani ta rufa sannan ya juya, saida ya kashe mata wuta ya kalleta yace “I love u.”

Cikin turo baki na rashin jin dad’in k’in sadata da danginshi tace “I love u too.”

Rufe mata k’ofar yayi ya fita ya koma d’akinshi, yau ma baiyi bacci ba yana tunanin Sarah, yace Salahadeen ya d’aukota ne dan ya kawar da hankalin mutane, idan aka ce anyi kidnapping d’inta duk fad’in garin da kewayenshi zai d’auka, zai nuna masu k’wamushen sun nemi tsabar kud’i kuma ya kai musu, amma kuskuren da yayi na saka police cikin maganar yasa suka kasheta suka turo gawarta, a lokacin kuma an shanye jininta sai kawai ya bayyanar da gawarta, za’a tausaya masa tare da jajanta masa da kuma duk’ufa neman kidnappers d’in. Sai dai ba zai bar kowa yasan abinda yake shirin aikatawa ba har Salahadeen ma.

Da safe ta shirya cikin riga da wando na cot farare k’al dasu sai dogayen takalmi bak’ak’e, ta tafi tare da dreba kamar kullum ya aje ta a campagni.

Wannan abu bai barshi baccin kirki ba yana tunanin me yasa? Dan haka ko da gari ya waye ya shirya ya fita, ya san Shakoor yana zuwa office d’inshi k’arfe 09:00 ne, dan haka tun takwas yaje masana’antar kai tsaye zuwa d’akin tsaro na wurin, ma’aikata biyu ne ya samu da alama su sukayi aikin kwana, dan d’ayan ma yana shirin shiga toilet, d’ayan kuma dake zaune yana yin break, saida ya ga shigewar waccen sannan ya shigo, da sauri mutumin ya kalleshi yana d’aukar bindigar da aka basu saboda tsaro, da sauri shima ya d’ago kanshi tare da cire hular da yasa dan kar a gane shi, da yake yana yawan zuwa sun gane shi sai ya aje bindigar a harshen turanci yace “Me kake yi anan?”

Shi a yaren da zai gane yace “Akwai hoton wani ne da yallab’ai Shakoor yace na zo na duba a nan.”

“Waye?” Ya fad’a yana kallonshi, matsawa yayi yana fad’in “Ka nemo min duk wata d’auka daga jiya k’arfe 09:40 zuwa da 45.”

Zaune yayi ya shiga bincika mishi, ba b’ata lokaci ya nuna mishi hoton, ko da ya hangin mutumen da yake son gani yace “Yawwa gashi nan.”

Tsayawa yayi ya mishi zoomenshi, wayarshi ya fito da ita ya d’auki hoton Alhaji Kabeer, kallonshi yayi yace “Thanks.”

Fita yayi da sauri yana turawa wani abokinshi shege ne kan n’aura, ko da ya tura mishi hoton a lokacin yana bacci dan ba aiki ne dashi ba, cikin jin haushi yace “Shiiit! Wek up Richard.”

Dole ya hak’ura ya shiga jiran lokacin da zai turo mishi da amsa, dan ko kira yayi ba zai d’auka ba in yana bacci, kusan awa biyu da tura masa hoton kafin ya tashi, ko da ya samu sak’on ya shiga binciken k’wak’waf, dan danan kuwa ya samu amsar abinda suke son sani ya turawa Salahadeen.

10:30 cif ta fito daga office d’in ta shiga lift zuwa caf茅t茅ria a k’asa, rashin girman kanta yasa ko da ta shiga kai tsaye wajen kayan abincin ta nufa, wani cake da jus kawai ta d’auko ta zauna d’aya daga cikin kujerun wurin, hankali kwance take cin abinta tana d’an kallon mutanen da suke shigowa suma cin abinda suke buk’ata, bata cinye duka ba ta mik’e da tissue a hannunta tana goge hannu, ta matakalar bene ta bi har ta sauka na d’aya dana biyu, a na uku ne ta kawo daidai lift wani dattijo a cikin ma’aikatan ya fito, kafin ta rufe bata san da mutum a bayanta ba kawai taji an fizgeta zuwa ciki tare da rufe mata baki da tissue wanda hakan ya haddasa mata yin baccin da babu niyya.

Saida suka sauka duka ya d’auketa cak ya nufi wajen ajiyar mota da ita, cikin motar ya sakata wacce ke sak da irinta Shakoor, bak’in gilashin dake ga motar yasa masu gadi basu b’ata lokaci wajen bud’e mishi ya shigo ba ko ya fita. Yana kan hanyarshi kiran Richard ya shigo mishi, ko da ya d’auka ya shiga zayyana mishi adreshin gidanshi da kuma masana’antarshi da ma irin tsaron dake gidan da masana’antar.

Da k’arfi ya juya akalar motar zuwa masana’antar, yayi sa’a yana daf da shiga mota zai bar wurin shi kuma ya k’araso, tsayar dashi yayi suka gaisa a sama sama kafin yace “Sai naga kamar na tab’a ganinka ko?”

“Eh yallab’ai, jiya mun had’u a renaux zaka fita ni kuma na shigo.”

Da murmushi yace “Hakane, to da me zan iya taimakonka?”

Gyar tsayuwa yayi yace “Akan maganar sace ‘yarsa ne, dan Allah ko kasan wani abu akai?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button