NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Tara na safe har ta wuce sannan ta farka, dafe kanta tayi tana mamakin yanda yau tayi bacci mai nauyi haka, duk da lattin da tayi kuma saita kasa kazar kazar d’in shiryawa ta fita, da k’yar ta kammala shiri ta fita, haka duk ta wuni sukuku da ita a makarantar ma ba komai ta fahimta da kyau ba dan jikinta ne ma bata jin dad’in shi sosai.

Da rana tana zaune wajen da aka tanada dan cin abinci, ga abincin a gabanta ta d’ebo amma ta kasa ko kallonshi sai yamutsa fuska take, kujerar dake fuskantarta taji anja an zauna, d’aga kanta tayi ta kalli matashiyar budurwar kyakyawada ita, da k’yar ta k’ak’aro murmushi ta mata tana amsa gaisuwar da waccen d’in ta mata, cikin harshen turancin da ake musu anan tace “Ya ba kya cin abincin naki?”

Cikin kasala tace “Haka kawai, bana jin dad’i.”

Cike da kulawa tace “Ayya sannu, baki da lafiya kenan?”

Girgiza kai tayi tace “A’a lafiyata lau, kawai bana jin dad’i.”

Cikin kulawa ta sake cewa “Me zai hana kije asibitin makaranta to sai a dubaki? Watak’ila yanayin wurin ne bai dace dake ba.”

Wani murmushi tayi tace “Ba fa yau na zo ba, na kwana biyu ai.”

“Duk da haka dai kije a dubaki, in baki da lafiya taya zaki fahimci karatunki?”

Yanda tayi maganar yasa Sarah jinjina kai tace “Ok, bari na samu na ci wannan saina tafi.”

Ita ma aza farantinta tayi akan teburin suka fara cin abincin, kallonta Sarah tayi tace “Anan k’asar kike?”

Girgiza kai tayi tace “A’a zuwa nayi.”

Tana cin abincin tace “Daga wace k’asa kika zo?”

Da murmushi a fuskarta tace “Niger, ke fa?”

Kallonta tayi sosai tace “Yar niger ce ke? Yayi kyau, ni ma asalin mahaifina d’an niger ne, mahaifiyata kuma yar England amma ni an haifeni a Tha茂lande kuma anan na girma.”

Murmushi tayi tace “Kenan kina zuwa k’asarmu kema?”

Girgiza kai tayi tace “A’a, ban tab’a zuwa ba sai sau d’aya.”

Da mamaki ta kalleta tace “Baki tab’a zuwa ba? Kuma kince garin mahaifinki ne, me yasa baki zuwa?”

Kallonta kawai tayi tana murmushi ba tace komai ba, d’aga kafad’a tayi tace “Kinga ni kuma ina so naje Tha茂lande.”

Kallonta tayi tace “Kina da yan uwa acan ne?”

Cikin wulwula idonta tace “Eh to, akwai d’an uwan mahaifina acan.”

Murmushi kawai ta mata tare da yamutsa fuska, aje cokalinta tayi ta kalleta tace “Ina ga zan tafi, zaki zo muje ne?”

Tissue tasa tana goge baki tana fad’in “Eh idan kina so sai na zo.”

Murmushi ta mata ta mik’a mata hannunta, d’ora nata hannun tayi ta mik’e suka nufi asibitin, sanda suka je ta fad’i duk abinda ke damunta sai taga kamar malamar na neman kambama matsalar, har da wani d’aukar jininta da sata ta kawo fitsarinta, ita duk sai taji ranta ya b’ace ma, a waje tace su zauna su jira zata shiga d’akin gwaji, a nan ma hira suka d’an fara tab’awa har ta fito ta kallesu tace Sarah ta biyota, shiga tayi ta zauna a inda ta nuna mata, kallon data mata duk sai taji gabanta ya fara fad’uwa ba gaira ba dalili.

Ba tare data daina binta da wannan kallon ba tace “Sarah Shakoor?”

Jinjina mata kai tayi alamar eh, sake duba wasu takardun dake gabanta tayi tace “Sanda kika zo makarantar nan da kaina na miki test, kasancewar a waccen bayanin da kika bayar sanda za’a cike miki takardunki kin tabbatar baki da aure yasa ba’a miki awon ciki ba, amma kuma yanzu gwaji na nuna ciki ne a jikinki har na tsawon wata uku da kwanaki, ya akayi haka Sarah?”

Wani abu taji ya daki kanta da k’arfi har cikin zuciyarta, tsabar mamakin dake fuskarta kallo d’aya zaka mata kasan a firgice take, girgiza kai ta shiga yi tana fad’in “No! No! I am not! I am not pr茅gnant! Noooo.”

Da sauri ta rik’o hannayenta tana k’amk’amewa tace “Dan Allah ki sake dubani ki gani, wallahi bana da ciki ki taimaka min.”

Fizgar hannayenta tayi ta nuna mata sakamakon tare da cewa “Sakamako ba k’arya zai miki ba, ki zauna ki nutsu kisan a inda kika samo cikin nan Sarah, dan dokar makarantar nan ba zata d’aga miki k’afa ba.”

Fashewa tayi da kuka ta tashi da sauri ta zagaya kusanta ta durk’usa ta rik’e k’afarta tana fad’in “Kiyi hak’uri ki taimake ni dan Allah karki bari su sani, idan suka sani zasu koreni ne kiyi hak’uri.”

Tallabota tayi suka mik’e tsaye tana fad’in “Sarah ki fahimta mana, matsalar shine sanda kika zo kince baki da aure, sannan an miki tayin kwana a cikin d’akunan dake makarantar nan kika k’i amincewa kika ce kina da masauki, duk da makaranta tana saka ido a kanku kuma bana tunanin sun sameki da aikata wani laifi, amma abune mai wuya ki kare kanki a yanzu kam, dan kinga ba zaki fad’a musu kina da aure ba yanzu.”

Dafe kanta tayi da hannu tace “Mr. ka cuce ni, ka lalata min rayuwata da burina kai kuma kana can kana harkar gabanka.”

Wata enveloppe ta mik’a mata tace “Ki kaita ofishin principale.”

Girgiza kai tayi ta sake fashewa da kuka tana fad’in “Dan Allah na rok’eki ki rufa min asiri kar a koreni, wallahi nima bansan ina da ciki a jikina ba, ki taimaka min karku tsayar min da karatu na.”

D’aga kafad’a tayi tace “Kiyi hak’uri Sarah, idan ma na rufa miki asiri ai ciki fitowa yake, ko kin manta ne zai girma har ya fito a ganshi a jikinki?”

Dafa kafad’arta tayi tace “Kiyi hak’uri kinji, ko da sun koreki yanzu saboda k’aryar da kikayi ne, idan kika gyara kuskurenki a gaba zaki iya dawowa musamman idan kin samu mai tsaya miki.”

Kallon takardar hannunta tayi ta share hawayenta ta fita a office d’in, matashiyar nan na ganinta ta mik’e da sauri ta bi bayanta tana fad’in “Lafiya? Me ya faru ne a ciki?”

Tsayawa tayi ta juyo ta kalleta, saida ta sauke ajiyar zuciya tace “Ya sunanki?”

Cikin kulawa na ganin idonta alamun tayi kuka tace “Sunana Sajida Abdel Aziz Aghali, me ya sameki naga kamar kinyi kuka?”

Cikin son b’oye kukan dake taho mata tace “Sajida zaki iya fad’a min sunayen dake cikin k’asarku?”

Da mamaki a fuskarta tace “Me ya faru wai? Ki fad’a min mana.”

Rik’e hannunta tayi tace “Na rok’eki ki fad’a min karki b’ata min lokaci.”

Cikin mamakinta tace “Akwai Niamey, Dosso, Tillabery, Zinder Agadez, Maradi, Tah…”

Da sauri ta saketa tace “Maradi, nagode.”

Rab’ata tayi zata wuce ta rik’ota da sauri tace “Ko sunanki kin k’i fad’a min bare abinda ke faruwa, shin baki d’aukeni k’awa bane?”

Girgiza kai tayi tace “Kiyi hak’uri, ni sunana Sarah Shakoor Aghali, watak’ila zan rigaki isa k’asarki saboda wani abu na gaggawa daya taso min.”

Zata wuce Sajida ta sake rik’eta da mamaki sosai tace “Sarah Shakoor Aghali?”

Da sauri ta ciro wayarta a jaka ta mik’a mata tace “Dan Allah taimaka ki bani lambarki.”

Sarah ce ta fito da wayarta ta mik’a mata tace “Ke dai ki saka min lambarki zan nemeki.”

Karb’ar wayar tayi cikin shakku tace “Kin tabbatar zaki kirani?”

Jinjina kai tayi tace “Zan kiraki.”

Saka mata lambar tayi ta karb’a ta wuce, da kallo ta bita sai taji zuciyarta na raya mata kamar Sarah yer uwarta ce, duk da bata santa ba amma tasan yayan mahaifinta farin sani a hoto, duk da dangi na tsegumi akan dukiyarshi mahaifinta babu ruwanshi da wannan, kullum fatanshi bai wuce d’an uwan nashi ya zo ba, da jimawa kuma an fad’a musu yana da ‘ya mace wacce aka sakawa sunan kakarsu wacce ta haifi iyayen nasu Saratu, sai dai ita ko a hoto basu san kammaninta ba. Da wannan tunanin tayi saurin komawa aji dan lokacin cin abincin ya k’are.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button