NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Dariyar da tayi ne tasa su kallonta duka, wani kallo ya shiga yi mata na tuhuma da son ganin da wa take magana haka? A hankali ta shiga mayar mata da “Nagode yer uwa, amma ya zakiyi maganar so? Taya zan yarda na fara son sa bayan bai damu dani ba? Ai ki ma daina wannan tunanin.”

Ma’aikata biyu ne suka shiga jera abubuwan da suka d’auko, daidai tana d’ago kai daidai Salahadeen ya kannewa d’aya daga cikin ma’aikatan ido tare da nuna masa da baki Sarah, hakan yasa ma’aikacin ya jinjina kai ya aje wani plate mai fad’i na silba a gabanta, bud’e k’aton murfin yayi hakan yasa ta kallon ciki, tuffa ne da mango da fraise, yankasu akayi aka musu kwalliya, saida ta nutsu ta aje hankalinta ta fahimta abinda kwalliyar ke nufi, a hankali furta kalaman a cikin zuciyarta ” Mom Waleed.”

Kallonshi tayi fuska a had’e ta tab’e baki tare da d’aga kafad’a, d’an ture farantin tayi cike da halin ko in kula.

Ga abincin an jibge musu wanda ko wani plate dalolin kud’i ne, amma duka matan babu wacce ta kalli plate d’in bare tayi sha’awar ci, duk sai yaji haushi na neman kashe shi kamar ya zabgesu da mari, ba ma kamar Farha data duk’e kai kamar tana kuka, a hankali ya juya ya kalli mutanen dake wurin, suma dai mutanen wasu na d’an satar kallonshi suna mamakin yanda ya zo da mata har biyu, alamun matan bai nuna rashin tarbiya da fitsara ba da sai suce wani uban daba ne shi na wata k’asar, ga kuma yanda matan sukayi halin ko in kula dashi suka fita sabgarshi. Lura da basu fara cin komai ba yasa wani ma’aikaci matsowa yana tambayar Salahadeen ko da wata matsala ne? Cike da jin haushi ya mik’e tsaye ya fito da kud’i ya sanya a cikin littafin abincin ya kallesu yace “Ku tashi mu tafi.”

Bai jirasu ba dukansu ya wuce a fusace ya fita, saida ya kira driver ya zo zuwa lokacin duk sun fito harda Sarah data jawo k’afarta da k’yar, gaban motar ya bud’a ya shiga su kuma suka zauna a baya, hankali kwance ta sake d’aukar wayarta tana latsawa, babu wanda yayi magana yanzu kam har suka isa gida, ko da driver ya tsaya duk suka fita suka shige ciki, ma’aikatan mamaki suka shiga yi ganin an fita da farin ciki an dawo kowa fuska a had’e babu annashuwa.

Suna shiga d’akinsu ya shiga cire kayanshi bai kulata ba har ya gama ya canza wasu, yana d’aukar wayarshi zai fita ya kalleta yace “Ki rufe d’akin idan na fita, z kwana tare da ita ne saboda larurar k’afarta.”

Da wani irin mamaki ta kalleshi kamar zatayi magana sai yayi saurin tsayawa ya juyo a zafafe yace “Miye? Da magana ne?”

Sunkuyar da kanta tayi ta girgiza kai alamar a’a, nuna kanshi yayi yace “Hankalinku baya kwanta ba da kuka wulak’anta ni kuka tozartani cikin mutane ba?”

K’wafa yayi ya juya ya fice yana fad’in “Zaku gani dani kuke zancen.”

Da kallo ta bishi yana fita ya turo mata k’ofar sai kawai ta fashe da kuka ta shiga cire kayan jikinta da k’arfi kamar zata yagasu.

Yana fita ya gaishe da Kaka daya gani zaune a falo ya wuce d’akin a matuk’ar hassale, ta b’ata mishi rai sosai yanda yake ganin ya wareta ya mata bajinta ya fad’a mata sunan da yake burin sawa d’ansu amma ta watsa mishi k’asa a ido, zai je yaji dalilin daya sa suka mishi haka, bata fahimci me yake nufi bane? Ko kuma wanda take hira dashi ne a waya ya d’auki hankalinta har tayi banza da lamarinshi?

Yana tura k’ofar ba tare da neman izini ba ya mayar ya rufe, saida ya tako har tsakiyar d’akin yana kallon kayan data cire, daga ban d’aki ta fito daga ita sai rigar data saka mai siraran hannu amma irin ta sauko fiye da k’ugu, amma da zata duk’a duk wani abu dake k’asa saiya fito, sark’ar wuyanta take k’ok’arin cirewa tana fad’in “Granny taimaka cire min abun nan na kasa.”

A zatonta Kaka ce, saida taji k’amshin turaren ya matso kusa da ita tayi saurin juyowa hakan yasa gashinta saida ya shafi fuskarshi…

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:20 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 4锔忊儯6锔忊儯

Da sauri taja baya tana sauke hannayenta daga wuya tana fad’in “Me ka zo yi a d’akina yanzu?”

K’ala bai ce mata ba sai zagayawa da yayi bayanta, hannayenshi yasa da nufin cire mata sark’ar, da sauri ta juyo ta juyo zata fuskanci sai yayi saurin kama kafad’arta ya juyata baya, sark’ar ya kama ya shiga kiciniyar cire mata, cikin dakakkiyar murya yace “Me yasa kuka min haka? Ta wulak’anta ni ita dake babba, ke ma kuma dake amarya sai kika biye mata, me nai muku da kuka min haka?”

Jin ya cire sark’ar yasa ta taka zata matsa daga kusanshi, hannunshi ya zura ta cikinta ya jawo kukuminta ya had’a da jikinshi, da k’arfin bala’i ta rintse idonta sakamakon abinda taji yana tab’a ta a jikinta, wata rawa rawa taji jikinta ya d’auka, bakinta taji yana shirin fara kakkarwa kamar yanda in ta shiga halin firgici take yin haka. Hannunta ta d’ago ta dafe mararta da taji wani abu na neman k’ulle mata, bata bud’e ido ba har taji ya d’ora hab’arshi a saman kafad’arta, bakinshi ya shiga yawo dashi inda ya shiga shinshina wuyanta bayan kunnenta har zuwa saman kanta ido rufe, cikin tsananin firgita baki na rawa rawa tace “M….r, p..lea..s..e.”

Cikin wani yanayi da kai tsaye ba zaka iya cewa ga yanayin da yake ciki ba ya rad’a mata a kunne cewa “Me yasa ba zaki d’aukeni mijinki ba matar Sla?”

Bud’e idonta tayi ta tattaro sauran k’arfin daya rage mata ta ture shi, juyawa tayi ta kalleshi cikin rawar baki tace “Me ye haka? Me kake so a gare ni? Bana son muna samun kusanci irin haka da kai, dan Allah ka rabu dani.”

Juyawa tayi zata zagaya wajen gadonta taji ya fizgo hannunta, fad’o mishi tayi inda ya shiga k’arewa fuskarta kallo yana fad’in “Me yasa? Me yasa princess? Nace me yasa?”

Lumshe ido tayi tana had’e yawu a matuk’ar wahale, hannunshi taji cikin rigarta yana shafa mararta, da sauri ta bud’a ido zatayi magana taga ya zube gwiwoyinshi k’asa yana d’aga rigar sama, da sauri taja ja baya amma saiya rik’e k’ugunta gam ta yanda ta kasa motsawa, ganin bai bata damar gusawa ba sai ta sa hannaye ta shiga jan rigarta dan yana d’agawa pant d’inta ne ya fito da dogayen k’afafunta.

Tana janyo rigar shi ma yana jayeta sama, ya k’urawa mararta ido sai shafawa yake yana kallo, d’an d’ago kanshi yayi ya kalleta yace “Ya fara motsi ne?”

Cike da jin a takure take tace “Dan Allah ka fita daga nan.”

Tab’e baki yayi ya sake shafa marar har inda shatin pant d’inta ya tsaya, tana kallo ya d’ora bakinshi akai inda take taji wani zuuuu har cikin cikinta da k’asanta zuwa tafukan k’afarta, d’umin lemar labb’anshi ne ya daki mararta a lokacin, saida ya d’auke labb’anshi ya sake d’ago idonshi ya kalleta, cikin shafa mararta yace “Sarah ina so naga abinda ke cikinki, ina son shi sosai duk da ban ganshi ba, tun ranar da kika fad’a min ya samu naji soyayyarshi ta gauraya da jinina, ki tayani da addu’a Allah ya fito min dashi lafiya.”

Tunda ya fara magana ta shiga had’e yawu tana lumshe ido, kasa cewa komai tayi sai ja baya da tayi shima ya mik’e tsaye, kama hannayenta yayi ya zaunar da ita bakin gadon yana fad’in “Zauna kar k’afarki tayi ciwo.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button