NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Ba tare daya daina kallonta ba yace “Sarrah, me ye laifina a ciki? Me yasa zaki ce saboda ni ya mutu?”

Kallonshi tayi sosai tace “Oui, ce toi qui a caus茅 la mort de mon p猫re.”

Da k’arfi yace “A’a Sarah, banda laifi.”

Ko kula shi ba tayi ba sai ci gaba da kukanta da tayi, har ya juya zai fita sai kuma ya tsaya ya juyo, da sauri ya dawo ya hau gadon sosai ya rik’o hannunta, d’agowa tayi ta fara k’ok’arin k’watar hannunta, rik’eta yayi gam bai sake ta ba a k’arshe sai ma ya jawota jikinshi ya rumgume, cikin murya kamar wanda zaiyi kuka yace “Kiyi hak’uri ki gafarce ni, banda masaniya akan mutuwar mahaifinki, labarin mutuwarshi kawai na gani.”

Cikin kuka tare da son raba kanta dashi tace “Jamais, jusqu’脿 la mort.”

Sake matseta yayi sosai yana fad’in “Je t’en prie Sarah, qu’es ce que tu veux de moi apr猫s tu me pardonner?”

Saida tasa k’arfi sosai ta raba kanta dashi ta kalleshi tace “Je ne peux pas, ce toi qui a tu茅 mon p猫re et tu veux me tu茅 aussi.”

Baisan sanda ta d’auke fuskarta da mari ba, saida ya gama kashe da marin yaji wani abu yayi barazanar fitowa ta k’irjinshi tsabar yanda aka doka masa, da k’arfi ya idasa hawa kan gadon ya fincikota a jikinshi. Cikin tsoro da frgicin marin daya mata tayi shiru ta biyoshi kamar yanda ya so, tallabo fuskarta yayi yana kallon cikin idonta idonshi jawur rai a b’ace yace “Ni ba mugu bane, ba d’an ta’adda bane bare makashi, karki sake fad’a min wannan banzar maganar, kin fahimta?”

Da sauri ta d’aga mishi kai alamar eh, d’ora kanta yayi kan k’irjinshi ya ci gaba da shafa kanta, tsoronshi ne yasa ta yin shiru ta kasa motsawa sai sauke ajiyar zuciya da take, duk numfashin da yake saukewa mai zafi zafi a kanta yake sauka kuma tana ji, cikin muryar da tasha kuka sosai har tana shashek’a tace “Me yasa baka sona? Me yasa ba zaka barni na tafi daga nan ba? Na rok’eka mr. ka d’auke ni daga nan.”

Ba tare daya d’auke bakinshi daga kanta ba yace “Zan d’aukeki daga nan princess, zan mayar dake k’asarki kinji.”

A hankali tace “Yaushe? Ni ina so nayi jana’izar Abhi na, ni kad’ai gareshi fa baya da wanda zai masa, bana so mahaifina ya mutu a k’asar da ba tashi ba kamar wani kare.”

A hankali ya sake matseta a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya yace “Gobe, idan mama ta dawo saiki tafi.”

Ba tare data tashi daga jikinshi ba ta d’ago kanta tana kallon fuskarshi tace “Ni kad’ai zan tafi? Kai fa?”

Ba tare daya kalli fuskarta ba yace “Ba zan iya tafiya tare dake ba.”

Cikin marairaicewa tace “Mais pourquoi?”

Saida ya d’an matse bakinshi kad’an yace “Akwai ginin da ake min na gida da ake daf da kammala shi, sannan Mama ma ta tafi dan gabatar da wata harka ne, dole idan ta dawo zata buk’ace ni har komai ya daidaita.”

Saida ta sunkuyar da kanta ta zagaya hannayenta ta bayanshi ta k’amk’ameshi, wanda shi kuma yaji dad’in hakan sosoi har zuciyarshi, cikin taushin murya tace “Matsalar kud’i ce?”

Shi ma a tausashe yace “A’a, muna shirin kafa kasuwanci ne tare dasu Zeid.”

D’agowa tayi tace “A k’auyen.”

Girgiza mata kai yayi yace “A’a, mama taje duba gonarmu ne da mahaifinmu ya bar mana.”

Da sauri ta tashi daga jikinshi tana fad’in “Wow, kuna da gona, ina son noma sosai da manoma, dan Allah zaka kaini na gani, ina son ganin kore a rayuwata.”

Sagalele ya kalleta ya rasa ta yanda zai fad’a mata su fa za’a siyar da gonar ne, rik’e hannunshi tayi tace “Dan Allah mr., idan ka amince zan fara zuwa na ga gonat kafin na tafi.”

Cikin rashin karsashi yace “Shikenan zan kaiki, amma ba gobe ba.”

Yamutsa fuska tayi tace “To amma ai ni gobe ne zan tafi.”

D’aga kafad’a yayi tare da tab’e baki, langab’e kai tayi tace “Zan fara zuwa na ga gonar, idan na dawo saina tafi, please kar kace A’a.”

Baice komai ba kawai ya kwanta kamar an turashi kan gadon, sama yake kallo amma idonshi rufe yana sauke numfashi a hankali, k’ura mishi ido tayi tana kallo tana jiran taji me zai ce, amma sam babu alamar zai sake mata magana ma, tab’e baki tayi ta d’ora kanta a kan pillown dake can b’angaren inda k’afafunshi suke.

Shiru ko ina ya d’auka kamar bacci ya d’aukesu sai kawai ta tashi zaune, hannu ta zura a hankali zata janye matashin daya d’ora kanshi a kai, bud’a ido taga yayi ya zuba mata wata uwar harara, da sauri ta janye hannun tana zuro baki gaba, ganin ya sake rufe idon sai kawai tace “Gaskiya kayi hak’uri, ni da pillow biyu nake bacci d’aya a k’irjina d’aya a kaina.”

Banza yayi da ita bai kulata ba bare ya tanka mata, hararanshi tayi tana ci gaba da turo baki, mayar da k’afafunta tayi inda nashi suke kawai bata tsaya komai ba tayi luf kan k’irjinshi ta d’ora kanta akanshi.

Da sauri ya bud’a ido tare da fad’in “Ke d’aga ni?”

Ruf ta rufe ido ta bud’e baki ta dinga fitar da sautin minshari ita a dole bacci har ya d’auketa, k’ok’arin tureta gefe ya shiga yi sai kuwa ta rik’e rigarshi gam da hannunta d’aya mai dogayen akaihu, da k’arfi ya tureta yana fad’in “Yau naga jaraba, ke rabu dani mana.”

Tana rabuwa dashi tayi wuf ta d’auke matashin tana dariya, tsaki yayi ya tashi zaune yana kallonta, ita kam ko a jikinta sai ma d’ora pillown da tayi ta kwanta d’aya kuma tayi ram dashi ta rumgume tana matse k’afafunta.

Cike da takaici ya dinga kallonta yana girgiza kai, ganin ita har tayi haramar bacci kawai ya juya kanshi yana jan wani tsakin.

Daga zaune ya d’an gyara zamanshi yanda zaiji dad’i ya rufe ido, a hankali bacci ya sureshi mai dad’i da nauyi, kamar cikin mafarki yaji ana d’an zungurarshi da k’afa, sama sama yaji sauti na d’an tashi na numfashi mai bayyanar da tsantsar wahala. Cikin nauyin ido ya d’aga idonshi ya sauke kan gadon inda yake jin sautin, da k’arfi ya zabura ganin Sarah a wani mawuyacin hali, rik’e take da wuyanta gam idonta duk sun kakkafe alamu k’arara na fitar rai, kamar beby ya fincikota jikinshi ya rumgume yana kallon fuskarta yana girgizata da kiran sunanta.

A hankali numfashinta ya fara yin k’asa sosai yana shirin barin gangar jikinta, tashin hankalinshi ya k’aru ne ganin jini yana fitowa a hancinta, har ga Allah bai tab’a samun kanshi a irin yanayin rud’un daya samu kanshi ba, har gawar mahaifinshi ya gani amma yayi juriya sosai. Cikin tsananin firgita ya k’walla kiran sunanta da iya k’arfinshi wanda hakan yasa Mamuh da Iffa bud’a idonsu suna kallon juna, da gudu suka shigo d’akin suka tsaya kanshi, Mamuh ce ta iya cewa “Yaya lafiya? Me ya sameta?”

Cikin k’araji ya kallesu yace “Kawo min ruwa, ku kawo min ruwa dan Allah.”

Duk a tare suka juya sai kuma Mamuh ta tsaya ganin Iffa harta kusa fita a d’akin, kallonshi take yanda yake ta k’ara mannata a jikinshi, idonshi sun kad’a sunyi ja kamar zaiyi kuka, amma kasancewarshi ba mai saurin zubo da hawaye ba yasa ko k’walla babu a idonshi, cikin fahimtar al’amarin tace “Yaya ka mata addu’a mana, haka na ga mama na mata kwana biyu idan tana firgita.”

Da wani irin sauri ya d’ago ya kalleta kamar wacce ta tuna mishi da wani abu, tabbas gaskiya ta fad’a abinda ya kamata yayi kenan, amma baisan abinda yasa shi rud’ewa ba har ya fita a hayyacinshi ya rasa abunyi ba, kamar yanda ya samu mama a ranar ya mata ya kai bakinshi cikin kunnenta ya shiga mata karatu.

Iffa na kawo ruwan Mamuh ta karb’a ta tofa wasu addu’o’in a ciki, ta jima a haka kafin ta d’an zuba a hannunta ta sake matsowa ta shafa mata a fuska, daga shi har ita k’ura mata ido sukayi suna kallo, ganin ko motsi ba tayi ba yasa Mamuh ja baya ta zaro ido tace “Yaya ko ta mutu? Inna lillahi wa’inna ilaihi…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button