NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Bai gama fad’a ba Mama ta bud’e k’ofar d’akin tana sauke ido akan shi, kamar wacce Allah ya aikota sai kuwa tasa hannu ta bangajeshi yayi baya ya dangane da bango ta rumgume Mama, Mama da ba taga fahimtar wacece ba tana jin ta fara fad’in “Mamie mamie, i miss u i miss u so much, Mamie i love u.”

Rumgumeta Mama tayi suka k’arasa shiga d’akin tana fad’in “Saratu ke ce? Yaushe kika dawo?”

Sakin juna sukayi tana rik’e da hannayen Mama ta kalleta tace “Mamie shigowata kenan.”

Hararanta tayi tace “Ke da kika tafi kika manta dani ma ko kirana baki tab’a yi ba, ni nayi hushi ma fita ki bani wuri.”

Fahimtar abinda Maman ta fad’a yasa ta saurin sake rik’e hannunta tace “A’a Mamie kar ki min hushi mana, kiyi hak’uri kinji ki yafe min.”

Fizge hannayenta tayi ta juya baya tana rumgume hannaye ita a dole tayi hushi, da azama ta juya ta fuskanceta tana dafa kafad’arta cikin hausarta tace “Indai kina so na fad’a miki wani abu da zai saki farin ciki to ki min dariya mana.”

Hararanta mama tayi k’asa da sama tace “Ki fara fad’a min sannan.”

Da sauri ya k’arasa shigowa d’akin yana mata alama da yatsanshi akan bakinshi ma’ana tayi shiru, matsawa baya tayi dan yanda ta ganshi tasan zai iya toshe mata baki, kallon mama tayi tace “Mamie i am pr茅gnant.”

Rashin fahimta da mama tayi ne yasa ta kalli Salahadeen tace “Me take nufi?”

Da wani irin k’arfi ya cabko Sarah a hannunshi, matseta yayi a jikinshi yasa d’aya hannun ya rufe mata baki yana kallon Mama cikin rashin gaskiya yace “Ba komai mama, wasa take miki kinsan watan april (avril) muke.”

Wani kallo mama ta masa da tunanin to me ya d’auketa? Watan juillet fa ake har yana daf da k’arshe ma shiyasa yanzu ake ta samun ruwa akai akai, amma ya zai ce april? Hannun Sarah ta kamo dake ta mutsumutsu tana fad’in “Saketa to ta fad’a ko menene, sai kace zaka kasheta wannan matsa haka kamar ka samu gyad’ar k’uli-k’uli.”

Sakinta yayi yana zazzare mata ido, mak’alewa tayi a wuyan Mama tace “Kawo kunnenki na fad’a miki.”

“Ke! Wai baki da lafiya ne?” Ya faka mata tsawa, a harzuk’e Mama ta kalleshi tace “Bata da lafiyar ina ruwanka, ka fita a d’akin nan yanzu fa, miye matsalarka da abinda zata fad’a?”

Tsaki tayi ta mik’a mata kunnenta tana saurare, cikin rad’a tace mata “Mamie yaro zan haifa miki.”

Kallon fuskarta tayi da tsananin mamaki ta kalli Salahadeen, alamar tambaya ne pal a bakinta amma dan kar Sarah ta fahimta sai kawai tayi murmushi ta shiga nuna mata murna, cikin shagwab’a ta kalli Mama tace “Mamie zan iya bacci? Na gaji sosai tafiyar nan babu sauk’i.”

Da kanta ta cire hijab d’in jikinta tana fad’in “Kwanta anan ki huta kinji, bari ina zuwa yanzu.”

Kwance tayi kan gadon data nuna mata ita kuma ta ma Salahadeen alama da ido ya biyota suka fito falo, zaune tayi shi kuma ya zauna k’asa kusanta kanshi k’asa, cike da mamakin al’amarin tace “Nasan kasan me nake son sani, zaka iya fad’a min gaskiyar abinda ke tsakaninka da Saratu? Salahadeen karka min k’arya dan wallahi in ba haka bane ranka zai mugun b’acewa, ka fad’a min ya akayi ta samu ciki bayan anan banga wata alak’a data shiga tsakaninku ba, ko kuma dama dai can rufemu kukayi amma akwai wata b’oyayyar alak’a a tsakaninku? Ko kuma dai bayan ta koma ka sake binta can har haka ta faru ne?”

D’aga kai yayi yana girgiza kai yace “Allah Mama ba haka bane, abun ya faru ne nima ba wai na shirya ma zuwanshi ba, ranar da muka je k’auye ne su baffa suka ce sai mun kwana, a ranar ne…”

Hararanshi tayi tace “Kuma kasan da haka shine baka fad’a min ba kuma har ka barta ta tafi, kenan dai a tak’aice matarka ce ita ma?”

Yanda ta tsura mishi ido yasa dole ya kalleta yana sosa kai yace “To Mama haka dai abun ya nuna.”

Da sauri ta kai mishi bugu a k’eya tana fad’in “Uwaka Salahadeen, ya kake neman ka mayar dani wata shashasha, kana son yarinya kana son zama da ita amma kana so ka cuci kanka.”

Dariya yayi yana sunkuyar da kai yace “Ba haka bane Mama.”

Ajiyar zuciya ta sauke mai k’arfi tana fad’in “To Allah yasa alkairi, amma abinda zan fad’a maka shine saika kawar da kai daga abinda zaka fuskanta, dole daga ni har kai zamu ji ba dad’i akan al’amarin yarinyar nan, kaga kuma babu yanda za ayi daya wuce hak’uri tunda har wannan rabo mai tsanani ya shiga, amma kafin a kwantar da hankali a fahimci haka nasan dole za asha daga.”

Jinjina kai yayi yace “Insha Allahu mama.”

D’orawa tayi da “Sannan kuma Farhanatu ka sanar da ita dan tasan abinda ke faruwa, kayi hak’uri da duk abinda zata maka, kar kayi saurin b’ata ranka kayi k’ok’arin shanye komai, duk abinda zatayi dole kuma kowace mace zata iya yi.”

Nan ma kai ya jinjina amma bai ce komai ba, tashi tayi tana fad’in “Je ka kwanta saida safe, zanje naga yar amana har tayi bacci ne.”

Murmushi yayi ba tare da Mama ta fahimta ba har saida ya ga shigewarta d’aki, tashi yayi ya nufi nashi d’akin yana kallon d’akin yana jin kamar ya shiga ya sake ganinta har ya samu ya ga cikin nata, samun kanshi yayi da sake sakin murmushi sanda ya bud’a k’ofar ya shiga d’akin, bacci take kamar yanda ya barta saidai ta gyara kwanciyarta. Alwala ya d’auro ya dawo ya kabbara sallah da rok’on Allah ya kawo mishi komai da sauk’i yanda zai iya d’auka.

Mama na shiga ta sameta ta cire doguwar rigarta sai bras d’inta da kuma dogon wandon da take sakawa, bacci har ya fara d’aukarta Mama ta ja zani zata rufeta, da sauri ta tashi zaune tana jan zanin ta rufe k’irjinta, cikin shagwab’a da gigin bacci ta kalli Mama tace “Mamie ai ke mahaifiyata ce ko?”

D’aga mata kai tayi tace “Sosai ma Saratu.”

D’orawa tayi da “Kuma mahaifiya kamar k’awa ya kamata ta zama ko? Wacce zaka iya yin sirri da ita?”

Nan ma jinjina mata kai tayi tace “Hakane Sarah, sai uwa ta zama kamar k’awa ga ‘yarta ne zata samu damar yin sirri da ita.”

Murmushi tayi ta kamo hannun Mama ta d’ora kan mararta da babu abinda ya mata shamaki da marar, marairaicewa tayi ta kalleta kamar zatayi kuka tace “Mamie anan ina jin ciwo, sannan ina jin kamar wani abu na d’an motsawa ya tare min mara, Mamie haka ciki yake dama?”

Dariya mama tayi ta shafa marar ta ta tace “Kiyi hak’uri kinji Sarah na, insha Allahu daya fara k’wari ai zai daina miki haka, yanzu ai yana kwance a mararki ne sannan ana cikin hallitarshi, kinga dole zakiji ba yanda kika saba ji ba, karki damu kinji.”

Gyara zamanta tayi ta mayar da k’afafunta baya ta d’ora kanta a k’afafun mama tana rik’e da hannunta gam tace “Mamie idan na tashi haihuwa ba zan mutu ba ko?”

Da sauri mama tace ” Ke waya fad’a miki ana mutuwa? Insha Allahu zaki haihu lafiya babu abinda zai same ki.”

Murmushi tayi sai mama da tace “Sarah zuwa yanzu me kika k’ara sani a game da addininki?”

Cikin murmushi ba tare data d’ago ba ta shiga zayyana wa mama duk abinda ya faru bayan tafiyarta da kuma karatunta, duk da wani abun da french ko turanci take fad’inshi amma dai ta fahimceta sosai, taji dad’i sosai da kuma mamaki jin yanda Sarah ke jawo aya da haddisai tana fassara mata, da wannan hirar tasu har bacci ya d’auki Sarah daga nan mama ma ta shiga gyangyad’i daga nan zaunen.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:17 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button