SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Duk da a lokacin bata jin zata iya magana amma haka ta daure ta k’ak’aro yawun da suka d’an rage mata ta kalleshi, saida ta lashe leb’enta daya bushe sosai har tana jin gishirin jinin daya bushe mata a baki tun marin daya mata jiya sannan tace “Nagode Allah daya saka mahaifina bao so duniya kamar yanda kai ka so ta ba, hakan ya min dad’i sosai, kuma kaima zan zo ka cireta a ranka dan ma batabbata bace, zaka barta duk tsananin son da kake mata, zaka barta ba tare da kasan ranar ba bare lokacin, ita kanta duniyar baka san yaushe za’a nad’eta ba bare kayi shirin tuba a lokacin, Kabeer kaji tsoron Allah, ka sani Allah ya halluceka ne dan ka bauta masa kawai, duk da bana da tabbaci akan aikinka, amma alamu ya nuna kana had’a Allah da wani, zunubin da Allah baya yafewa mai shi idan har bai tuba ba, zunubin da mai yinshi idan har ya mutu akan shi ya kan dawwama a cikin wuta, ka gaggauta tuba Kabeer dan baka san randa zaka bar gidan duniyar nan ba.”
Cike da shak’iyanci yace mata “Na sani mana, na sani.”
A hanjali ta d’aga idonta a wahalce ta kalleshi da mamaki, duk da bata wani ganinshi da kyau haka ta kafeshi da ido tace “Yaushe ne? Waya fad’a maka? Ko masu fad’an za’a tashi duniya a shekara ta dubu biyu yanzu a shekara ta nawa muke? Kabeer a hadisi ingantacce ma an fad’a mana ranar juma’a ne, a cikin kwana d’ari uku da sittin na shekara muna juma’a guda hamsin da biyu, *wace shekara ce? Wane wata ne ko kuma sati? Sannan wace juma’a ce wannan babban rana mai d’auke da babban al’amari zata faru? Abisa rashin sanin wannan kad’ai ya ishi duk wani bawa tashin hankali, karka yaudari kanka da banzayen tunani da surkullen da shaid’an ke raya maka, ka tuba ga Allah kayi sa’a ubangiji mai tausayi ne da jink’ai, idan ya ga dama saiya yafe maka duka kurakurenka.”
Kamar jikinshi yayi sanyi kam dan har k’asan zuciyarshi yaji abinda ta fad’a ya ka bashi kyakyawan muhalli, amma kafin ya shiga tantance abun sai shaid’an yayi gaggawar kautar dashi ta hanyar sakar mata murmushi ya mik’e yana fad’in “Bari na kira miki kakanki, watak’ila zaki fi jin dad’in yi mana wa’azi idan kika ganmu tare.”
Ya fara danna wayar hannunshi tace “Dan Allah ka taimaka min da ruwa, ina so nasha ruwa, sannan ina jin yunwa ma.”
Wata dariya ya kece da ita ya juyo yana kallonta yace “Kin d’auka shak’atawa kika zo yi anan d’in? Kinga Sarah karki ce zaki ribace ni da wannan kalar tausayin naki ki cuce ni.”
Yana fad’a ya juya ya sake bi ta inda ya fito yana kiran Daniel, wayar ta jima tana ringing ba’a d’aga ba, a lokacin kuma Richard nata lalubar wayar a aljihunshi, yana d’aukowa ya bawa Salahadeen, ganin sunan Kabeer ya fito yasa shi saka yatsu biyu ya taushe mak’ogoronshi yanda muryarshi zata canza sannan ya d’auka ya d’ora a kunne, shiru ne ya d’an biyo baya kafin Kabeer ya d’anja tsaki na jin haushi yana tunanin yau gigin tsufa ya motsa mishi yace “Daniel ka zo gida ka same ni yanzu.”
Cikin k’ok’arin son koyar muryarshi yace “Wane daga cikin gidajen naka?”
Jim yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace “Ka manta gidan nawa ne ko me? Gida nawa nace maka ina da?”
Rashin sanin yanda suke mu’amulantar junansu kar kuma ya kwafsa yasa shi yin shiru, jin shirun yayi yawa yasa Kabeer jan wani tsakin ya kashe kiran. Da sauri ya tunkari Daniel ya shiga daddab’ashi yana tambayar ya fad’a masa gidan Kabeer? Cikin magagin baccin da har yanzu bai sake shi fad’a mishi unguwar da lambar gidan, da sauri ya mik’e ya tunkari kan wani tebur ya d’auki bindiga ya d’anata da kyau ya saka a bayan rigarshi k’asan wando, da sauri Richard ya dakatar dashi yana fad’in “Please Salah ka tsaya, ina zaka je haka?”
Da wani kallo ya kalleshi yace “Ban gane ba? Gidanshi mana, zan je na k’wato matata ko da zan rasa raina nima.”
“To idan fa ya kasheta?” Ya tambaye shi, wani marayan kallo ya masa sai kuma ya furzar da iska yace “Saina kasheshi shima.”
Girgiza kai yayi yace “A matsayina na abokinka ban baka wannan shawarar ba? A gani na kaje ka had’u da Insp. James ka sanar dashi abinda ke faruwa, ko da wani abu zai faru marar kyau zai fi ace hukuma na cikin lamarin, amma bana so ka d’auki doka a hannunka.”
Girgiza kai yayi kamar ba zai iya ba sai kuma ya kalleshi yace “Muje mu same shi.”
Basu yarda sun jima ofishin ba suka fad’a mishi komai dake faruwa, tsari sosai sukayi na yanda zasu kama shi a hannu sannan suka tafi gidan, a k’ofar tabkeken gidan aka tsayar dasu, wayar Daniel ce tasa suka umarce shi ya jira su kira mai gidan su sunar dashi, cikin sa’a kuma ana kira kamar a hassale ya d’auka sai cewa yayi “Ku barshi ya shigo mana nasan da zuwanshi.” Shi kanshi Salahadeen saida ya sauke ajiyar zuciya, izini suka mishi amma Richard dole ya tsaya a waje ya jira shi, har k’ofar b’angaren ya isa da motar ya tsaya, fitowa yayi yana sake k’arewa gidan kallo, lallai idan aka ce ka fad’i gidan Shakoor da gidan Kabeer wanene yafi kyau da girma? To tabbas an baka jarabawa mai wahala, dan duka gidajen sun had’u sun tsaru sosai.
K’ofar falon yayi nocking wata ma’aikaciya ta bud’e k’ofar, gaisheshi tayi tare da nuna mishi wurin zama tace “Ka zauna yallab’ai yana fitowa yanzu.”
Kallon k’aramin falon yayi inda ta nuna mishi bayan k’aton falon da suke tsaye yanzu, k’ala bai ce mata ba shi dai ya wuce inda ta nuna mishi, tsaye yayi yana k’arewa wurin kallo musamman kwabat dake shak’are da barasa d’an lemun kad’an ne, rik’e k’ugu yayi yana tab’e baki yana ci gaba da kalle kalle har zuwa sama da d’akuna suke, daga bayanshi yaji an ce “Me ya kawo ka? Ina Daniel?”
Juyowa yayi suka had’a ido, sake tab’e baki yayi ya sauke hannayenshi daga k’ugu ya zuba aljihu, a hankali ya dinga takawa cikin isa har saida ya tsaya gabanshi daf dashi sosai yana kallon idonshi yace “Ina matata take?”
Wani murmushi ya sakar mishi ya matsa daga kusanshi, kusan kayan shaye shayen ya nufa ya d’auki tangaran na glass ya d’auki kwalbar barasa mai kyau da tsada ya bud’a ya tsiyaya, saida ya kurb’a kafin ya kalleshi yace “Matarka, waya fad’a maka tana nan? Ba saceta akayi ba?”
Fito da hannayenshi yayi daga aljihu yace “Ba wasa na zo muyi ba, na sani kai ka saceta kuma ba zan bar nan ba har sai na ganta.”
Wani kallo ya masa tare da d’aga gira sama, tab’e baki yayi ya samu kujera ya zauna yace “Shikenan, ni kuma idan har ka ga matarka zan barka ka tafi da ita harda gudummuwar kayan beby zan baku ma.”
Yanda ya k’arashe maganar da yar dariya yasa ranshi b’acewa, har zai tunkareshi a hassale sai yayi saurin d’aga mishi hannu yace “Karka soma yaro, nan ba can bane da nake zuba maka ido, shima ina yi ne saboda akwai abinda nake so na cimma, amma yanzu da barewata ta shigo hannu na kana gigin yi min haukan nan zan had’aka kai da barewar na b’atar daku.”
Da kallon tuhuma ya bishi yace “Sarah tana raye?”
Saida ya wani d’aga kafad’a kafin yace “Watak’ila, amma ina tabbatar maka ba zata mutu ba har sai mun sha jininta, sai dai k’ishin ruwa ya galabaitar da ita.”
Cikin jin haushi ya k’arasa gareshi ya shak’o wuyan rigarshi da hannu biyu yana jijjiga shi da fad’in “Ina take? Ka fito min da ita ko kuma na kasheka kaima, wallahi ba zan barka ba inhar ka cutar da ita.” Dan danan sai ga s茅curit茅 biyu sun shigo da gudu suna d’ana bindiga a kan shi suna bashi umarnin ya sake shi ko su harbe shi.