SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Dakatar dasu Kabeer yayi hakan yasa suka sauke bindigoginsu, a lokacin shima ya sake shi yana fad’in “Ka fito min da ita kaji, bana so ka kaini mak’ura muyi abinda bai dace ba.”
Hannu Kabeer ya mik’awa d’aya daga cikin s茅curit茅 d’in ya karb’i bindigar, bai ankara ba kawai ya doka mishi bakin bindigar a goshi, cikin rashin tsammani yayi baya kamar zai fad’i yana dafe da goshin, d’aga hannunshi yayi yaga har jini ya fito, wani kukan kura yayi rai a b’ace ya kai mishi naushi a kumci. Shima zafi yaji sosai hakan yasa s茅curit茅 d’in azamar rirrik’e Salahadeen, motsa bakinshi yayi ya tofar da yawun bakinshi da sukayi jawur dasu, kallon Salahadeen yayi yana murmushi da jinjina kai yace “Lallai ka iso inda bana iya jura, ka shigo har komata amma ka nemi cin zarafi na, k’arya kake, yanzu zan kasheka sannan na shiga ciki na kashe Sarah, ban damu da hakan me zai janyo min ba…”
Ya k’arashe maganar yana d’ora bindiga akan goshin Salahadeen, rufe ido yayi yana kalmar shahada a zuciyarshi, sai dai baiji gabanshi na fad’uwa ba bare hakan ya tsorata shi, da sauri ya bud’a ido saboda k’arar bindigar da yaji, Kabeer dake gabanshi sai yanzu ya ganshi durk’ushe gabanshi yana rik’e hannu da jini, da sauri ya kuma kallon police d’in da suke shigowa da bindigogi. Wanda suke ganin duk abinda ke faruwa ta k’aramar camera da suka saka mishi a mab’allin riga dake d’aukar hoto mai motsi da sauti.
Sakinshi s茅curit茅 d’in sukayi inda yasa k’afa ya harbe bindigar dake gaban Kabeer, k’arasowa Insp. d’in yayi yana fad’in “Mun kamaka malam Kabeer.”
Da kanshi ya saka mishi ankwa suka mik’ar dashi tsaye, kallon sauran jami’an yayi yace “Ku zagaya duka gidan nan ku duba mana miss Sarah.”
Salahadeen na jin haka ya tafi da gudu ya haura sama ya shiga bincika d’aki d’aki tare da sauran police d’in, a dai nan ciki kam kowane d’aki sun duba amma basu samu komai ba bayan kayan d’aki, sanda suka sauko suna fad’a mishi ne Kabeer yayi wata dariya ta mugunta, wani kallon tsana ya bi Salahadeen dashi yace “Tabbas Sarah tana cikin gidan nan, amma ba zaku tab’a ganinta ba, ku manta da ita har abada, Sarah tana wurin da ko da tsafi ba zaku iya ganinta ba, tsananin tsoron Allahnka da kuma yawan ibadarka ne kawai zai iya kub’utar da ita, wanda na tabbata kafin lokacin da addua’rka zata risketa yunwa da k’ishin ruwa sun kasheta murus.”
Wata dariya ya sake kecewa da ita sanda suka nufi fita dashi Insp d’in na fad’in idan yaje ofishi zaiyi magana, dab’as ya zauna kan kujerar dake bayanshi yana dafe kanshi, rintse ido yayi sosai tare da kame kanshi da yaji yana wani harba mishi, dafashi Richard yayi yana fad’in “Sorry Salah, za’a ganta ka kwantar da hankalinka.”
A tsawace ya d’ago yana fad’in “Ban gane za’a ganta ba? Kai nan kaga alamar za’a ganta? Baki ji me yace bane?”
D sauri yaja baki yayi shiru saboda hawayen da yake ta k’ok’arin rik’ewa ne yaji sun gangaro mishi a idon damanshi, da sauri ya share yana jan tsaki ya juya mishi baya, Richard zaiyi magana wayar Salahadeen dake hannunshi ta shiga k’ara da yake datarshi a bud’e take, Zeid ne ke kiranshi kiranshi ta WhatsApp.
Sake dafa kafad’arshi yayi yana mik’a mishi wayar, juyowa yayi yasa hannu ya karb’a yana dubawa, saida ya sauke numfashi ya saita nutsuwarshi sosai dan ko da yaga appelle vid茅o (vid茅o call) ne ya tabbatar da Mama ce tasa a kirashi, dan ita tafi son ta ganka ido da ido hankalinta yafi kwanciya.
D’auka yayi sai dai ya kasa nasarar jawo murmushi a fuskarshi ko kawar da damuwar dale kan fuskar, suna had’a ido da Mama yayi k’asa da nashi saboda ladabi yana fad’in “Mama barka, ina wuni?”
Cikin damuwa tace “Salahadeen lafiyarku k’alau kuwa? Ina Farhanatu da Sarah suke? Kwana biyu duk na jiku shiru.”
Ba tare daya yarda ya kalleta ba yace “Mama lafiya lau, Farha tana gida.”
Cikin rashin yarda tace “To suna lafiya? Kai kuma kana ina ne?”
Jin kamar zuciyarshi zata karye ya fashe da kuka yasa shi komawa ya zauna, kallonta yayi sosai yace “Mama akwai matsala ne? Sarah aka sace kuma duk da an kama wanda ya sacenta amma har yanzu bamu sameta ba.”
Cikin razani ta dafe k’irji tace “Me? Yar amanar aka sace? Yaushe?”
Girgiza kai yayi cike da damuwa yace “Mama kusan kwana biyu kenan yau.”
Da sauri tace “To yanzu ya ake ciki? Kana nufin an rasata kenan?”
Kamar mai shirin fashewa da kuka yace “Mama ban sani ba nima, duk mun duba gidan amma bata nan, kuma ya tabbatar mana tana cikin gidan nan, amma kuma bamu ganta ba.”
Cikin fitar da k’walla Mama tace “To ka sani ko k’arya ya fad’a muku? Salahadeen ka ci amanata da kasa na yarda d’ari bisa d’ari zaka kula da ita, yanzu kenan sai a barta ta mutu ko me kake nufi? Duk da babu cikinka jikinta ai da aurenka kanta, ko kuma shima auren ka gimtse shi ban sani ba?”
A hankali yace “A’a Mama, wallahi ban sake ta ba har yanzu, kuma ma cikin na nan bai zube ba, Mama ki taimaka mana da addu’a Allah yasa kar komai ya sameta, dan ya fad’a min k’ishin ruwa da yunwa ma kawai zasu iya kasheta a inda take.”
Da sauri ta sake fad’in “Kun tabbata kun duba duka ko ina? Ku duba har bayan gidan mana da k’ark’ashin k’asa ko yana da d’akin k’asa ne.”
Saida ya d’an d’aga murya yace “Mama yace fa ko tsafi zamuyi ba zamu iya ganinta ba, ya fad’a min kawai mu manta da ita, wai tsaron Allah na da kuma yawan ibadata da addu’a ne kawai zasu kub’utar da ita.”
A take tace “To sai me? Ka nuna masa kai mai tsoron ubangijinka ne mana, ka nuna masa kai bawan Allah ne mana ta hanyar duk’ufa da addu’a, tabbas babu abinda yafi k’arfin ubangiji, dashi da ita da kuma kai dukanku kuna k’ark’ashin ikonsa ne, babu wani abu dake b’uya daga gareshi, babu abinda ke motsi a k’ark’ashin k’asa bare kuma wanda ke ban k’asar. Salahadeen tashi kayi alwala kayi sujada gaban sarkin sarakuna ka mik’a mishi kukanka, nayi imani da zai saurareka ya kuma dubeka da tausayawa, indai har babu hakk’in kowa a kan ka haka ita ma Sarah, to insha Allah zata bayyana a gabanka kafin ka sallame sallarka, daga nan nima zamu tayaka insha Allahu zata fito lafiya.”
Wani irin k’arfin gwiwa yaji tare da dakewar zuciya, har yana jin tsigar jikinshi na tashi, mik’ewa yayi ya kashe kiran ya nufi hanyar daya tabbatar madafa ce, alwala ya d’auro ya fito Richard na kallonshi ya kabbara sallah akan wankakken tilles d’in dake ta k’yalli.
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:21 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LABARI*
SAMIRA HAROUNA
*SADAUKARWA GA*
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
5锔忊儯4锔忊儯
Ya jima a wurin, sallah yake yi yana kai kukanshi ga mahallicinshi, karatu yake sosai da addu’a duk wacce ya isa ya kuma sani, tun Richard na kallonshi daga tsaye har ya gaji ya zauna bayanshi yana kallonshi, har Malik d’an Kabeer ya diro gidan saboda samun labarin abinda ya faru a gidan, hakan baisa ya gintse sallah shi ba sai Richard ne ya dinga tare haukan da Malik d’in ke yi na tambayar su waye su? Me kuma suke yi? A hakan dan bai gane Salahadeen ne wanda ya b’alle masa hak’ori ba.