NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Da kai kawai ya masa alama da yawwa, d’an satar kallonta yayi sai yaga tuni ta sake komawa jikin Aba, d’an guntun tsaki yayi yana jin shi fa ba zai juri wannan bak’ar al’adar ba, duk da uba ne gareta baya zargin komai, amma dai yana da kishi ba zai so hakan ya ci gaba da faruwa ba.

Haka duk suka shiga motocin suka nufi gidan Hajia, ba wani jimawa suka sauka gidan, tare da Aba suka shiga ciki su Sajida kuma suka dinga fito da kwanukan abincin da suka shirya, dan Aba yace dole ta fara sauka gidan Hajia. Suna shiga da sallama Hajia ta tarbe su, ganin Sarah yasa ta fashe da kuka suka rumgume juna sosai, irin kukan da sukayi har saida Farha ta zubar mata da hawaye, duk da ita ma marainiya ce kamar Sarah ba uwa ba uba, ama taji tafi ta gata tunda ta tashi zagaye da dangin iyayenta, ita kuma sai yanzu ne suke bayyanar mata, da k’yar suka tsagaita da kuka kuma suka fara gabatar da sallah isha’i, zaune sukayi akan lallausan shinfid’ar carpet suka ci suka sha, suna kammalawa hira aka dasa inda Salahadeen ya fita tare dasu Salim. Ganin dare ya fara yi yasa Sajida kallon Sarah tace “Yer uwa mu tafi gida ki kwanta ko?”

Kallonta tayi ta mak’ale kafad’a alamar a’a, wata harara Hajia ta zabga mata tace “Ke baki san inda kanki yake ciwo ba, ki tashi ki bi ubanki ku koma gida ni takwarata ta zo kenan.”

Sakin.baki Sajida tayi tace “Hajia ban gane ta zo ba kenan? Kina nufin bata tafiya can?”

“Haka nake nufi.” Ta fad’a tana ciccib’awa ta mik’e tsaye kasancewarta mai k’iba, kama hannun Sarah tayi tace “Tashi muje ki kwanta kinji, karki kula da ita ma.”

Murmushi Aba yayi ya kalli Sajida yace “Tashi mu tafi ke barta nan.”

Turo baki tayi tace “Um um! Ni ma na zan kwana wallahi tunda ba zata koma ba.”

Sabira ma dariya tayi tace “Aba nima nan zan kwana tare da aunty Sarah.”

Tashi yayi tsaye yace “Shikenan to, ni zan tafi gobe nima saina dawo nan da kayana.”

Kallonshi Hajia tayi tace “Karka fara ma wallahi, kayi k’ok’ari ka nemi mata kayi aure kaji na fad’a maka.”

Yana jin haka yasa kai ya bar d’akin, da kallo ta bishi tana fad’in “Yayi kyau Abdel, ba dai ni ka mayar mahaukaciya ba, akan maganar aure har muryata ta k’are saboda kai, ba matsala zaka sani.”

Farha dao dariya tayi saboda ganin yanda suke rayuwarsu hankali kwance, duk tashi sukayi inda Hajia ta nuna ma Sarah da zata kwanta ita da Farha, amma Sajida tace ita ma nan zata kwana, haka kuwa akayi sai Sabira kawai ta kwana tare da Hajia.

Salahadeen kam basu dawo nan ba dan tunda Aba ya fad’a musu sun kwanta anan, tare da Salim ya kwana a d’akin shi inda ya cika dare yana magana da Richard akan abinda ya dace ya fara sani, tare da had’ashi da limamin masallacin kusa da gidan Sarah dan ya koyi abubuwan da suka dace.

Washe gari tana tashi sukayi wanka suka shirya, suna zauna suna karin kumallo Salahadeen tare da duka su Salim suka shigo gidan, saida suka shigo kuma sai yaji da ma basu shigo ba, a cikin kayan data taho dasu ne, rigar siraran hannaye ne da ita amma bata kamata ba, sai dogon wandon mai taushi shima sai rawa yake a jikinta, kanta kuma bud’e yake ta saki gashin ya kwanta duka bayanta. Tana kallonshi da idonta masu kalar k’asa k’asa ta d’auke lokaci d’aya, saida taji Farha tace “Ina kwana yaya Salahadeen?”

Saida ya zauna inda Hajia ke nuna musu kafin yace “Kin tashi lafiya?”

“Lafiya lau, ya gajiya?” Ta fad’a tana kallonshi, saida ya saci kallon Sarah data rik’e kofin tea d’inta a hannu tana kurb’a a hankali, sake kallon Farha yayi yace “Idan kin gama saiki shirya zamu wuce ko.”

Jinjina kai tayi cikin jin dad’i tace “To yaya, na ma ida ai, tare da Sarah zamu tafi ko?”

Da sauri ta kalleta da mamaki, Hajia ma kallon Sarah tayi kamar yanda Salahadeen yayi, girgiza mata kai yayi yace “Ita zata zauna nan, daga baya na dawo sai mu tafi tare.”

Da sauri ta mayar da kallonta kanshi kuma tana aje kofin k’asa tace “Zaka dawo kuma? Ni na ce ina so na koma can? Babu inda zanje.”

Tunda ta fara magana ya d’auke kai kamar baisan tana yi ba, saida ya ji ta idar ya kalli Farha ya mata alama da ido ta tashi su tafi, mik’ewa tayi ta shiga ciki dan d’auko kayanta, kallonshi Aba yayi murya k’asa k’asa yanda Sarah ba taji ba yace “Karka damu kaji, kasan yarinta na damunta, idan ka shirya kawai ka zo ku tafi.”

Wani murmushi ya masa kawai bai ce komai ba, dan in ya tashi zuwa ko d’auketa ne zaiyi ba tare da kowa ya sani ba馃榿, Hajia ce ta turo baki kamar yarinya tace “Gaskiya mijin ka tafi ka bar min takwarata anan, idan na shirya sai ka zo ka tafi da ita.”

Yar dariya yayi ya kalli Sarah yace “Ba komai matar, idan kin shirya saiki d’aga min hannu.”

Farha ce ta fito hakan yasa Hajia tashi ta shiga d’aki, duk mik’ewa sukayi suka fita farfajiyar gidan dan raka su, Hajia na fitowa da k’atuwar leda ta bawa Farha tsaraba ta kai gida, Aba ma kud’i ya bata masu yawa yace tasha ruwa a hanya, godiya tayi mai yawa har suka fita k’ofar gida, tana daf da kaiwa k’ofar gidan ita ma taji an fizgota ta dawo ciki, rintse ido tayi saboda fad’awa da tayi jikin wani abu amma kuma mai taushi ne mai kama da mutum, k’amshin turarenshi da taji ne ya tabbatar kanshi ne ta fad’a, bud’a ido tayi da mamakin ba gaba yake duk suna baya ba? To ya akayi har ya dawo cikin gidan ya zama na k’arshe har ya jawota?

Rik’e yake da k’ugunta sosai yana kallon fuskarta yana gyara mata gashin kanta, kallonshi tayi saita had’e fuska tace “Miye haka? Ana jiranka fa.”

Cikin tsatsareta da ido yace “Ni kike ma rashin kunya ko? Har kike fad’a a gaban mutane wai babu inda zaki je? To idan na zo tafiya dake ki tabbatar kin b’uya a wurin da bil’adama baya iya zuwa.”

Kallon rasjin fahimta ta mishi lokaci d’aya kuma ta d’auke idonta, hannu yasa cikin rigarta ya d’ora kan mararta, a hankali ya shiga shafawa wanda hakan ya janyo mata lumshe ido tana jin tsigar jikinta na tashi, tallabo k’eyarta taji yayi ya d’ora bakinshi kan kunnenta cikin rad’a yace mata “Ki kula min da kanki Saratu, ki kula da kanki dan Allah ki taimake ni ki min wannan alfarmar.”

Samun kanta tayi da sauke ajiyar zuciya mai sanyi akan kafad’arshi ba tare da tace komai ba, saida ya sauke mata ajiyar zuciya shima cikin kunne wanda taji ta saukar mata da kasala ya sake cewa “Saratu bana son rumgume rumgumen nan kinji, karki sake ko da yar uwarki mace ne.”

Ba tace komai ba har taji yana neman bakinta zai d’ora nashi sannan ta kawar da kanta tace “Please mr.”

Yatsa yasa ya tallabo hab’arta hakan y tilsta mata kallonshi, a hankali ya kai bakinshi kan nata ya sumbata, kallon idonta yayi yaga ta rufe ido, murmushi yayi yace “Zan tafi, amma duk sand kika gani ki d’auka na zo ganinki ne kawai.”

Ita dai ba tace komai ba dan so take yayi nesa da ita ta samu damar tunanin abinda ke damunshi, raba jikinshi yayi da nata ya fita, bata iya fita k’ofar gidan ba har saida taji tashi motar daya d’auka shata zata kaisu har gida komai dare, tare dasu Sajida duk suka shiga ciki suna musu fatan sauka lafiya.

Ko da suka shiga ciki Hajia ta kalli Sarah tace “Ke ‘yar nan kiji tsoron Allah, yanzu mijin naki kike ma iskanci? Wallahi daina ganin a gabana ne sanda ya kamaki babu ruwana.”

Dariya Sarah tayi cikin hausarta tace “Takwarata karki damu, babu abinda zai min.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button