NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Girgiza kai tayi tace “Kaji lalacewa, gaba d’aya Shakoor ya bari harshenki ya lalace, kina magana da k’arfi kamar an saki dole, yanzu fad’a min shi yaushe zasu taho?”

Zuru tayi tana kallonta da sauran mutanen dake d’akin ma, Aba ne a harshen french yace “Tambayarki take yaushe Abbhinki zai zo?”

Yar k’aramar ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi da kyau tana son danne hawayenta tace “Abhina ya rasu, ya rasu watanni kusan biyar yanzu.”

Cikin son kawar da hawayenta tace “Dan Allah bana so ku mishi kuka, dan hakan zai dawo min da mutuwarsu ne sabuwa.”

Duk k’ok’arinta hawayen ne taji sun sulalo mata kan kumatu, da sauri tasa hannu ta goge tana kallon yanda sukayi jugum dasu sai Hajia dake girgiza kai tana fad’in “Ina! Shakoor d’in? Shine ya mutu ban sani ba.”

Da sauri Sarah ta matsa kusanta ta jawo kanta ta d’ora a k’irjinta ta shiga bata hak’uri, kuka Hajia tayi kamar yarinya har saida Aba shima ya zubar da hawaye saboda ganin kukan mahifiyarshi.

Wunin ranar Hajia a d’aki tayi shi duk da kuwa dangi dayawa sun dinga zuwa gidan ganin Sarah, amma wasu basu damu ba tunda shi kanshi ubanta haushi yake basu, duk Sarah sai taji ba dad’i ganin Hajia a wannan halin, amma tayi niyyar idan suka wayi gari bata ga wani canji ba dole ta d’ora Hajia akan turban data d’ora kanta ita ma, mantawa da baya da kuma fuskantar gaba.


Sun sauka lafiya amma cikin dare, sun samu tarba daga mutanen gidan, saida suka cika cikinsu suka shiga ciki bayan sun juye musu tsarabar da Hajia ta basu tare da wanda suka siyo a hanya, suna shiga suka samu sukayi wanka suka fito, tana shirin yin kwance ya fito ya lula da ita duniyar manyan mutane, dan dama a kunne yake tun kusancin daya samu da Saratu, hak’uri kawai yayi suka shigo garin lafiya.

Yau fa Farha ta gane kurenta, ka rantse ita ta mishi laifi dan horon daya mata, duk da tayi kewarshi dan tun kafin su bar garin har suka je babu abinda ya shiga tsakaninsu, amma yanzu daya dinga abu d’aya kamar wacce ta b’ata mishi rai saita fara rok’on ya barta kuma ta gaji. Saida ya samu nutsuwa shima ya gane fa haushin can ne ya sauke anan (k’awa zuci), cije leb’e yayi yana yin k’wafa a ranshi da tunanin duk randa ya koma garin nan saita gane shayi ruwane ita, kai in ma yayi niyya nan zata dawowa dan da yana tunanin ya barta can har ta haihu ne. Ga Mama da tun shigowarsu take tambayar ina yar amanar take kuma? Saida suka tabbatar mata lafiya lau take tana wajen dangin Abhi kad’ai ta nutsu.


Da safe ko da suka tashi kamar yanda ta shirya da gudu suka shiga d’akin Hajia da lokacin ke zaune kan sallaya, dukansu rumgumeta sukayi suna sumbatarta ta ko ina suna fad’in “Barka da safiya Hajiarmu.”

Cikin son k’watar kanta tace “….

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:21 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 5锔忊儯6锔忊儯

“Kai ku rabu dani mana, baku ga abinda nake bane?”

Sarah ce ta sake k’amk’ameta tace “Haba k’awata, kiyi dariya mana.”

Turo baki tayi tace “To nayi a sake ni.”

Basu saketa ba sai cewa suke sai tayi dariya suna kallon fuskarta, fita sukayi dan cin abincin Hajia ta kalli Sarah ta girgiza kai tace “Gaskiya na tsani naga mace da wannan k’ashin na wuya, haba dubeki kamar mai yunwa.”

Sajida ce tace “Hajia wai ina ruwanki da ramarta? Su fa idan kina da jiki kallonki ake ana ganin baki damu da kanki ba komai ci kike, ki barta haka take son ganin kanta.”

Hararanta tayi tace “To kema ina ruwanki? Ai ba dake nayi ba sarkin shishigi.”

K’wafa tayi ta shiga d’akinta jim kad’an ta fito, suna kallonta ta bawa Sarah magani data kad’a a cikin madara ta bata tasha, saida tayi kamar zatayi amai ta mik’a mata kofin.

Kallon Sarah tayi tace “Wai ke yanzu da cikin a jikinki ne d’azu kuka shiga d’akin nan da gudu haka? Anya kuwa kina son cikin nan?”

Turo baki tayi ba tace komai ba, kallon jikinta Hajia tayi tace “Ke wai baki da wasu kaya ne sai irin wannan?”

D’aga kafad’a tayi tare da cewa “Eh Hajia.”

Kallon Sajida tayi tace “Ke bani wayata na kira Abanki na fad’a masa sai kuje boutique d’inshi ku zab’o mata kaya.”

Da sauri Sajida ta shiga ta dauk’o mata wayar akan gado ta bata, tana kira bata wani jima ba aka d’auka, gaisawa suka fara yi kafin ta fad’a mishi yace ba damuwa su je zai turo driver ya d’aukesu, tana kashe wayar ta kallesu tace “Je ku shirya kafin drivern ya zo.”

Duk mik’ewa sukayi suka koma d’akinsu suka shirya, Sajida ma data sa aka kawo mata kaya cikin riga kalar ta Sarah ta shirya dan can mekka shigar da suke yi kenan, tsaf sukayi inda suka d’ora baby hijab d’insu suka fito, kallon Sajida tayi ta mik’a mata wayarta tace “Kira min lambar Fatsima.”

Waro ido tayi tace “Hajia Fatsima kuma? Me zata miki? Ko bazawari kika samu?”

Dariya Sabira tayi sai Sarah dake kallonsu da kyau, dak’uwa ta mata tace “Uwaki ke da bazawarin, idan ni na tsufa a gyaran jiki ba ina da ‘ya’ya da jikoki ba?”

Jinjina kai tayi ta kalli Sarah tace “Da alama yer uwa za’a darzu fa.”

Wata dak’uwa ta k’ara mata tace “Ke wai bakinki bai iya cin albasar sautu bane?”

Fizgar wayar tayi sanda ta mik’o mata tana d’orawa a kunne, odar da suka ji tasa Sajida kama hannun Sarah suka yi waje suna fad’in “Sai mun dawo Hajia.”

“A dawo lafiya.” Ta fad’a b’angare d’aya kuma tana amsa sallamar da Fatsima ke yi mata a kunne, bayan sun gaisa take fad’a mata ta zo tana buk’atar ta ma Sarah gyaran jiki, tambayarta tayi kamar me da me? Ita kuma tace komai ma tana so a mata kuma, da yake sun saba sosai cewa tayi ba komai zata zo kawai yaushe take buk’ata, idan zaiyi gobe ko jibi shine abinda ta fad’a, alk’awari ta mata insha Allah zata zo jibi d’in, da haka sukayi sallama Hajia ta tunanin yanda jikarta zata kasance.

Kaya sosai suka d’auko mata daga nan kuma Aba yace su wuce wurin d’inki ta zab’i wanda take so, suna hanyar dawowa wayarta tayi k’ara, dubawa tayi taga bak’uwar lamba ce, d’auka tayi dai ta kara a kunne, shiru tayi ba tace komai ba haka shima daga b’angarenshi, sun d’auki kusan minti biyu ko sautin numfashi babu mai ji kafin yace “Sannu hamshak’iya.”

Da yake da hausa ya mata magana kuma ta gane muryar sai kawai tace “Me?”

K’wafa yayi mai k’arfi kamar zata fasa mata kunne yace “Ai ni kike jira na fara gaisheki ko? Saratu wallahi ki kiyaye ni, in ba so kike yau naje na taho dake ba.”

Cikin mamakin al’amarin bawan Allahn tace “Mr. wai me na maka ne? Daga kira saika balbaleni da masifa.”

Daga b’angarenshi yace “Masifa? Ni ke miki masifar ma, to bari kiji yau zan zo kuma ko kina so ko baki so saina d’aukoki kin dawo nan, tunda dai yawan tsiya kike fita.”

Zaro ido tayi ta kalli Sajida dake gefenta tace “Yawo kuma? Waya fad’a maka?”

Murmushi yayi mai sauti yace “Hummm! Ai daga jin iskan dake shigowa ta kunne na ya nuna min kina waje ne, gashi kuma kin tabbatar min da kanki.”

Hararan wayar tayi tana turo baki tace “To da karna fita kake nufi ko me? Da igiyarka a kai na ne da kake min wannan ikon?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button