NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Wani huci yayi har saida tayi murmushi yace “Shikenan dani kike magana.” Ko da ya fad’a ya kashe wayar, gwalo ta mishi tana mayar da wayar a jaka tace “Kaji mutum sai jaraba, ni matarka ce da zaka tsareni da bala’i.”

Sajida ce tace “A’a fa yer uwa, matarshi ce ke har yanzu tunda bai sake ki ba, kuma wallahi a yanda dai na ganshi kam ba zai sakeki ba har abada.”

Hararanta tayi tace “Matsalarshi, ba abinda zai hana ni yin wani auren idan na samu wanda nake so.”

Dariya Sajida tayi tace “Ba zai yarda a d’aura ba.”

“Me yasa?” Ta fad’a tana kallonta, murmushi tayi tace “Saboda ni zan fad’a masa, kuma nasan kinsan me zaiyi in har ya sani.”

Tintsirewa sukayi da dariya ita da Sabira da ita dai bata tsoma musu baki a hirarsu, hararanta tayi tace “Duk tsiyarku sai naji dad’in rayuwa nima.”

Wata dariya ta sake yi kafin tayi magana kuma tayi saurin cewa “Ke kinga gidan aunty Bieba bara mu biya.”

Kallonta tayi tace “Wacece?”

Saida tasa driben ya tsaya a k’ofar gidan sannan tace “Ita da Aba cousins ne abokan wasa ne, da Abanta da Hajia cikinsu d’aya.”

Tsayawa yayi k’ofar gidan suka shiga da sallama, da ganin gidan kasan matar akwai tsafta da kama jiki, ai tana ganin Sarah farin ciki ya bayyana a fuskarta ta nuna ta tace “Ita ce mai sunan Hajia ko?”

Sajida ce tace “Eh aunty, ya akayi kika sani?”

Rumgume Sarah tayi tana ta murna kafin ta kalli Sajida tace Wacce aka shelanta mana zuwanta a grp na family, ai nasan da zuwanta yanzu haka shirin tafiya gidan Hajiar na ke, tun jiya na so tafiya dan mai gidan ne baiji dad’i ba shiyasa.”

Ciki suka shiga suka zauna suka bud’a shafin hira Sajida na so su tafi amma aunty ta rik’esu da kayan ciye ciye da hira, ita ma kuma Sarah kanta bata so su tafi saboda tana jin dad’in yau ita ce kewaye da yan uwanta, har saida dreban ya gaji ya tafi suka ce ya dawo da yamma, haka ko akayi inda aunty Bieba ta ma Sarah alk’awarin zuwa ta mata wuri, musamman da Sajida ta fad’a mata tana da aure ai.

Ganin shiru basu dawo ba yasa Hajia bawa mai aikinta waya tace ta nemo mata lambar Sajida, kallonta tayi tace “Hajia wallahi ban iya ba kar na tab’a na b’ata miki kuma.”

Fizgar wayar tayi tana fad’in “Bani nan dan Allah sai z茅ro kawai.”

馃ぃ Dariya Lariya tayi ta fita tana fad’in “Taron zeruna ba.”

Saida tayi sa’a Aba ya kirata ta fad’a mishi ya kira yaji ina suke? Kiransu yayi suka fad’a mishi sannan ya kira ya fad’a ma Hajiar, hankalinta kam ya kwanta da taji inda suke sai kawai ta zuba idon ganin sanda zasu dawo.

Kamar yanda suka ce ya dawo ya je ya d’aukosu, saida suka kai d’inkin sannan suka wuce gidansu Sajida, har magriba suna gidan musamman da suka samu su Hamid da Rufa’i sukayi ta hira har magriba, sai lokacin kad’ai suka koma gida tare da Salim ya kaisu.

Ai fa daga ranar salon cin abincin Sarah ya canza, dan danan taji yunwa ta nemi abinci ta ci, tun tana masifa ita da Hajia tana mitar ita ta jawo mata, har Hajia ta dinga kare kanta da cewa cikin jikinta ne ba ita ba, haka su Sajida ke wuni yi musu dariya, har hutunta ya k’are ta koma wanda daga shi saita shekara biyu kafin ta dawo, Sarah bata ji dad’in tafiyarta ba ko kad’an, gashi ita Sajida ta had’ata da principale d’in yace saboda cikin jikinta ne yasa basu nemata ba saita haihu, idan tana buk’atar ci gaba saita dawo. Haka ta zama yanzu daga ita sai Sabira ita ma kuma kullum a hanyar makaranta da islamiyya take, ita da Hajia ne shiyasa duk inda Hajia zata je bata barinta tare suke tafiya.

Yanzu ma tana fitowa da sauri ta nufi fridge ta bud’e, wata kakkaurar yoghourt ta d’auko ta bud’a ta shanye ta aje robar, juyowa tayi taga Hajia sai dariya take mata, turo baki tayi tana fad’in “Kinji dad’i yanzu ko? Ai na gane so kike na zama kamarki.”

Hararanta tayi tace “Munafuka je ki duba madubi ki kalli kanki kiga ke haka baki fi kyau ba dan Allah.”

Saida ta juya mata baki ta koma d’aki dan bacci ne take amma yunwa ta tasheta, ai kam gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta, a gaskiya ba laifi in dai gaskiya zata fad’a kam yanzu tafi kyau, tsayinta yana nan daram dashi, fad’in cikinta da mara da k’ugunta duk suna nan, amma k’ugun sai yayi tudu hakan yasa yanzu ya kasance mai d’aukar hankali, wuyanta ya shafe sosai kumatunta sun taso, ga kuma cikinta da yanzu wata hud’u da kusan sati biyu kenan shima, ajiyar zuciya kawai ta sauke ta koma kan gadon ta kwanta.

Hajia ce ta shigo tace “Idan bacci zakiyi taso ki rufe d’akin naki fita zanyi ni, kuma kinga Lariya bata zo ba yau sai anjima.”

Da sauri ta zabura ta taso tana fad’in “A’a Hajia jira ni, tare zamu tafi.”

Nunata tayi tace “Ke ki rufa min asiri ki dinga yin komai a hankali, kinsan da mijin nan naki kullum saiya min gargad’in na kula dake.”

Cikin sauri ta shiga neman doguwar rigar da zata aza akan riga da wandon dake jikinta tana fad’in “Rabu dashi Hajia dan ya takura min ne.”

Jinjina kai tayi tace “Haba dai ba ruwana, kinga yace ya so ya zo wannan satin dan za ayi auren k’anwarsa ne yasa ya d’aga tafiyar, ina tsoron idan ya zo yace dake zai koma, ni kuma ina so ki haihu anan dan akwai tanadin dana miki.”

Kallon Hajia tayi sanda take gyara zaman hijab d’inta tace “Wai Hajia har bikin Mamuh ya matso ne?”

D’aga kai tayi tace “Eh mana, tsakanin gobe da jibi ne zata shiga lalle.”

Jinjina kai ta shiga yi tana fad’in “Kinga kuma daga shi har Mama da Farha babu wanda ya tuna min, bare kuma ita amaryar kanta.”

Saida ta nufo hanyar fita tace “Zasu yabawa aya zak’inta idan naje.”

Dukan kafad’arta Hajia tayi tana fad’in “Ja’ira taji hausa yanzu ita ma.”

Dariya kawai tayi suka fita bayan Hajia ta rufe d’akin da gidan, dreba suka samu yana jiransu suka tafi, tafiya mai nisa sukayi kafin suje gidan wani malamin sukayi barkar data kaisu ta haihuwa, sun d’an jima zaune kafin kuma su fito zasu koma, da yake babu gidaje wajen sosai sai fili ga rak’uma nata yawonsu da masu su suna wasa dasu yasa Sarah kallon Hajia tace “Wai ni yaushe zan hau rakumi ne Hajia? Ko baki so na shaida a Agadez nake?”

Dariya tayi tace “Gashi can kije ki hau mana.”

Ai tana fad’in haka mik’a mata jakarta tayi tace “Bari ki gani kuwa.”

Wani matashin saurayi dake kan rakumi ta kalla cikin d’aga murya tace “D’an uwa zan iya hawa nima?”

D’aga mata kai yayi da cewa “Zaki iya?”

Ita ma daga mishi
kai tayi alamar eh, cikin sabo da dubara ya tsayar da rakumin ya gurfanar dashi duk tana kallo har ya dirko ya sauko, kallonta yayi yace “To hau mu gani.”

Ganin da gaske zata hau ne yasa Hajia takowa da sauri tana fad’in “Na shiga uku na lalace, Saratu rufa min asiri na mutu gida maza su binne ni.”

Bata saurareta ba saida kuma ta dafe kan rakumin ta zauna kan siddin ta d’ora k’afafunta a inda taga ana d’orawa, har zai kama rakumin ya tashi tace “Kaga karb’i wayata a hannun tsohuwar nan d’auke ni hoto na tarihi.”

Hajia da duk ta k’walalo ido ta kalli matashin tace “Yaron nan wallahi ciki gareta, inka bari wani abu ya sameta mijinta mahaukaci ne, babu ruwana idan ya kasheka.”

Dariya yayi yace “Insha Allah babu abinda zai faru Hajia, kawo wayar.”

Bud’a jakar tayi ta mik’a mishi wayar, saida ya d’auketa hoton sannan ya tashi rakumin tsaye, tuni yan kallo suka dawo kanta da mamaki dan abune a yanzun da ba a cika gani ba, haihuwar nan girman nan amma sai kaga wata tsoronshi ma take, duk da gabanta na fad’uwa daga cikin k’irjinta, amma ta k’i nuna tsoro a fili saima dad’in tafiyar da take ji da rakumin, yanda yake tafiyar d’aya bayan d’aya duk sai take dariya. Saida ta gama zagaya matashin na rik’e da akalar kafin ya tsayar dashi, wajen zaman rakumin ne fa saida tayi kamar zata fad’o tayi saurin rik’e siddin da take zaune akai, saida taji ta taka k’asa ta sauke ajiyar zuciya tana dafe da k’irjinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button