NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Haka suka shiga mota dreba ya jasu Hajia na fad’in “Wallahi ba zaki ja mijinki ya dinga ganin laifina ba, haka kawai wani abu ya same ki ace ni ce, to ki koma can gabanshi kinji na fad’a miki.”

Kallonta tayi tace “Wai ke Hajia komai sai ki ce mijina mijina, waya fad’a miki mijina ne na k’warai?”

Mayar da kallonta tayi kan wayar inda ta turawa Farha hotunan tana fad’in “Kinga ni a rakumi yau.”

Jinjina mata Farha tayi inda take cewa da ita ce ba zata iya ba, saida ta bata Mama suka yi magana har take sake nanata ashe bikin Mamuh ya kusa? Tace dai zata zo ita ma ayi da ita, sun gama gaisawa Farha ke nunawa Mama hoton tana fad’in “Kinga wai rakumi ta hau fa yau da suka fita.”

Zaro ido Mama tayi tace “Rakumi fa, in gani?”

Nuna mata tayi ta shiga kallon hotunan tana rik’e baki tana salati, tsaf suka jiyo daga bayansu yace “In gani.”

Mik’a mishi Mama tayi ba tare da tunanin komai ba tana sake fad’in “Kaji yar amana da k’arfin hali, ko ya tayi ma ta iya hawa?”

Kallon hoton yake sosai ranshi na k’ara b’acewa, wannan hoton sanda rakumin ke tafiya ne aka d’aukeshi ta bud’e hannayenta ta saki rakumin, duk da ta mishi kyau ya kuma ga canji a tare da ita, amma cije leb’e yayi saboda masifa, mik’awa Farha wayar yayi yace “Zata san dani take, ni zata mayar d’an iska da baisan ciwon kanshi ba.”

K’wafa yayi mai k’arfi ya fice daga falon suka bishi da kallo, gwaleshi Mama tayi tana fad’in “Yo me zaka mata ita dake can kai kana nan?”

Girgiza kai Farha tayi tace “Um um Mama, yaya ya wuce inda kike tunani fa.”

Sabgar gabansu suka kama basu sake bi ta kanshi ba, sun dai ga har rana lokacin da yake dawowa ya ci abinci amma bai dawo ba, har yamma tayi haka kuma dare yayi har bayan sallah isha’i, Farha ce ta kira shi amma sam bata samu, hankalinta ne taji ya fara tashi ta fad’awa Mama, cewa tayi ta kwantar da hankalinta ta k’yaleshi kawai zai dawo, ta daiyi shiru amma bata iya kwantar da hankalin ba kam.

Sanda suke wannan magana yana can kan hanya yana shan k’ura, kawai shi zai je ya taho da ita tunda ta raina shi, in kuma bata taho ba ya d’aureta ya taho da ita, ya so ya wuce amma dole ya tsaya arlit dan hanyar ma babu kyau ba zai iya kutsa wannan had’arin ba, amma fa ana sallah asuba ya kuma yankar hanya, kafin azahar ya shiga garin kai tsaye kuma ya wuce gidan.

Hajia na zaune ta saka lalle a k’afafunta sai Lariya na gyaran alayahu zata yi girki dashi kawai ya turo k’ofar tare da sallama, Hajia kallonshi take tana so ta tabbatar shi d’in ne, duk da suna gaisawa ta kira mai motsi a wayar Sarah, amma sai take ganin kamar gizo ne, har ya k’araso bata daina kallonshi bata kuma amsa sallamarshi ba, Lariya ce ta gaisheshi ya amsa ta mik’e ta shiga madafa.

Zaune yayi akan kujerar data tashi yana kallon Hajia yace “Matar me kike kallo ne haka? Na miki kyau ko?”

Baki bud’e tace “Wai da gaske kaine? To me ya kawoka yau?”

Murmushi yayi yace “Da fari dai ina kwana?”

Gaisawa sukayi sosai kafin ta sake cewa “Kai da kace ba yanzu ba me ya kawo ka kuma?”

K’asa yayi da kanshi yace “Ba naga kin d’ora min matata akan rakumi ba, shiyasa na zo naji wanda ya bata shawarar hawa da wanda ya bata rakumin.”

Dafe k’irji tayi tace “Na shiga, kai d’an nan kaji tsoron Allah, wallahi ni babu a hanuna a ciki, ita ce kawai ta gani ta hau, kuma saida na hanata amma bata ji ba.”

Kallonta yayi yace “Tana ina? Ko ta fita yawon?”

Nuna mishi d’aki tayi tace “A’a tana ciki, ai bata fita sai tare dani.”

Mik’ewa yayi yana fad’in “Kenan da izininki take fita Hajia?”

“A’a.” Ta fad’a tana binshi da kallo harya sunkuya ya cire takalminshi k’afa ciki, duk da yasha k’urar hanya, kafin ya k’araso saida ya gyara jikinshi yayi wanka ya gyara kayanshi, turaren kam dama akwai a mota fesawa yayi kawai ya shigo garin.

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:22 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismillahir rahamanir rahim

                 5锔忊儯7锔忊儯

Dama baiyi niyyar yin sallama ba haka ya shiga d’akinta, kwance take tana baccinta dan tana jin dad’in baccin wannan lokacin, k’afafunta da suka sha jan lalle ya fara kalla, doguwar rigar bacci ce kuma dake ba mai nauyin bacci bace da magagi sai bata janye ba bare harta nuna jikinta ba, gashinta ne kawai a hargitse dan har yanzu ba kitso take so ba, mayar da k’ofar yayi ya rufe ya k’arasa kan gadon, zaune yayi ta b’angaren da fuskarta take, kura mata ido yayi ya shiga kallonta , take tambayar ta zo mishi “Ya akayi tayi k’iba haka?”

Tab’e baki yayi yasa hannu ya daddab’a hannunta, saida ta furta “Uhummm!” Bud’a ido tayi ta kalli inda taji an tab’a sannan ta kalli wanda ta gani zaune, da iya k’arfinta ta saki k’ara ta zabura zaune tana fad’in “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, Hajia fatalwa, aljani ne, Hajia aljani.”

Had’e fuska ya sake yi ya gyara zama ya rumgume hannaye yana kallonta, daga can waje Hajia ta d’ago murya tace “Fatalwa kuma takwara? A gidan nan?”

Zabura ta sake yi ta sauka daga kan gadon a guje ta nufi k’ofa, har ta bud’e k’ofar zata fita yace “Kika fita a d’akin nan sai jikinki yayi tsami.”

Da sauri ta juyo ta sake kallonshi, marairaicewa tayi ta durk’usa k’asa tana kukan da babu hawaye tace “Dan Allah fatalwar mr. ki rabu dani, ni wallahi ban masa komai ba bare abun ya dawo kaina.”

Wata uwar harara ya wurga mata cikin jin haushi yace “Zaki zo nan ko saina takaki.”

Da sauri ta mik’e tana tunkararshi a hankali, kafin ta isa wajenshi wayarshi tayi k’ara, dubawa yayi kai tsaye ya d’auka yana sake kafeta da ido, ita ma kallonshi take tana so ta tabbatar shine ko kuma dai mafarki ne take, amsawa taji ya shiga yi da fad’in “Lafiya lau.”

“Um! Lafiya lau nake, ke fa?”

Gani tayi ya d’an murmusa yace “Ina wajen wannan baturiyar ne, na zo ja mata kunne ne.”

Kallonta yayi cikin ido hakan yasa gabanta fad’uwa, hannu ya mik’a mata alamar ta taho, mak’ale kafad’a tayi alamar a’a ba zata zo ba, wani kallo ya mata yana gyara zaman kanshi dan ta fahimta da kyau, yamutsawar da kayan cikinta sukayi yasa tayi saurin mik’a mishi hannun, janta yayi har saida ya ware k’afarshi ya mata masauki akan cinyarshi, zirrrrr taji wanda ya haddasa mata rufe ido, sunkuyar da kanta tayi hakan ya bashi wata sahihiyar damar k’urawa fuskarta ido yana kallo yana kuma ci gaba da wayar. Duk abinda yake fad’a tana jinshi, abinda yasa ta saurin kallonshi shine da taji yace “Ki daina b’ata yawun bakinki, ba zan yafe mata ba dole na hukuntata, yau zata kwana tare damu sai naga tsiyarta ai.”

Suna had’a ido ya mata kallon ko ban isa ba? Turo baki tayi ta sha’afa a cinyarshi take ta shiga bubbuga k’afafu tana gunguni, kallonta ya shiga yi ganin kamar da gayya ne take abun, d’ifff ya kashe wayar ya kalleta yace “Ke lafiyarki k’alau?”

Dakatawa tayi ta d’aga masa kai alamar eh, sakin hannunta yayi yace “Me kike a jikina?”

Da sauri ta mik’e tsaye tana fad’in “Ai bani na zo ba.”

Gabanshi ya nuna mata yace “Zauna nan?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button