NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Kallon wurin tayi da mamaki, k’asa fa yake nufi kuma idan ta zauna zai zama kamar ta zauna tsakiyarsa ne, ganin bata da niyyar zaunawa yasa shi d’aga gira guda ya mata wani shegen kallo, a hankali ta durk’usa wurin sannan ta gyara ta zauna. Daga yanda take zaune yana hangen k’irjinta daya wani taso yayi pam, lumshe ido yayi ya dafe wuya kamar mai jin zazzab’i yace “Me yasa kika hau rak’umi?”

Kallonshi tayi cikin shagwab’a tace “Saboda ina so ne?”

Ba tare daya kalleta ba yace “Me yasa bakiyi tunanin halin da kike ciki ba?”

Tiro baki tayi ba tace komai ba, jinjina kai yayi yace “Alamu sun nuna baki damu dashi ba, dan haka ki shirya dake zan koma.”

Girgiza kai tayi a hankali tace “Gaskiya ba zan je ba.”

Kallonta yayi yace “Umarni ne na baki ba shawara ba.”

K’asa tayi da idonta tace “Amma ai banga wani abu da kake min ba da zai nuna lallai kai mijina ne ka isa ka bani umarni, idan dai har zaka dinga tunk’ahon kiran kanka da mijina kuma kana bani umarni, ina ga ko a kasuwa ma zamu iya kiran duk wanda muka had’u dashi miji, sannan muyi gaggawar bin umarnin da suka bamu.”

Jin shiru bai ce mata komai ba yasa ta d’aga kai ta ga ko me yake? Idonsu ne suka had’u sai tayi saurin sauke nata, wani murmushi kawai ya saki dan ta gama d’aureshi bai kuma san me zai fad’a ba, saida ya sauke numfashi yace “Shiyasa nake so ki matsa kusa dani, idan har ban sauke hakk’in dake kaina ba sai kiyi k’orafi.”

Tab’e baki tayi tace “Ai duk inda nake zaka iya sauke wasu hakk’ok’in ba sai muna kusa ba, kawai ba so na kake ba nima kuma ba sonka nake ba, munyi aure ne a bazata saboda gudun wata matsala, me yasa yanzu ba zaka sake ni ba.”

Cikin fad’a yace “Ba zan sake kin ba, sai me? Zaki saki kanki ne?”

D’aga ido tayi ta kalleshi sai kuma ta juya mishi baki ta mik’e tsaye, kallonshi tayi tace “Tunda ba zaka sake ni ba saika bani lasisin auren duk wanda raina yake so.”

Juyawa tayi zata fita taji ya rik’e hannunta, matsar daya ma hannun ne yasa ta sakin siririyar k’ara, kallon fuskarta yayi idonshi duk sunyi jawur, a hassale ya mik’e tsaye yace “Ni ne kike fad’awa na yarje miki ki auri wani? Cikina ne fa jikinki Saratu, me kika d’auke ni ne wai? Marar zuciya ko me?”

Sakin hannun nata yayi ya nufi hanya zai fita sai kuma ya tsaya ya kalleta yace “Ki shirya gobe zan zo mu tafi.”

Ficewa yayi ya barta tsaye, ko a jikinta kam tunda dai tasan ba dole zai mata ba ai, sallama yayi da Hajia yace zai zo gobe su wuce, da to kawai ta bi shi tunda ba tada yanda za tayi.

Bayan fitarshi sukayi wayar da Farha suke tattauna yanda akayi har ya ga hoton, saida ta bata Mama take fad’a mata zata zo bikin Mamuh, suna ida wayar ta fita take fad’awa Hajia ta shirya su tafi tare, cewar Hajia “Yo kin d’auka lallen miye na miki kuma nima nayi? Ai na zuwa bikin ne, mutanen da suka rik’eki da amana dole muyi musu kara ai.”

Shiru tayi ita dai har Hajia ta sake fad’in “Kinga idan mijinki ya zo gobe saimu tafi tare kawai, tunda yace gobe zai zo.”

Kallonta tayi fuska a had’e tace “Ki daina ma wannan maganar Hajia, zamu tafi amma sai ana gobe bikin, ki fita harkar mutumin nan kawai.”

Lura da tayi ba da wasa take ba yasa ta cewa “Wani abu ya faru ne? Me ya miki?”

Kuka ne kawai ya k’wace mata ta d’ora kanta a saman cinyarta tana fad’in “Hajia kisa ya sake ni, kawai ni ya sake ni wallahi, ban da mutumi a idonshi, bai d’aukeni bakin komai ba, bai damu dani ba bare abinda ke cikina, banda tsanani da d’acin rai da kafa min doka babu abinda ya iya, ni wallahi ba zan iya zama dashi a haka ba ya sake ni tunda dama ba auren so mukayi ba.”

Ajiyar zuciya kawai Hajia ta sauke ta shiga shafa kanta tana fad’in “Kiyi hak’uri kinji Sarah, kowace mace da kalar ta ta jarabawar da take fuskanta a nata rayuwar auren, kinyi dacen kishiya da uwar mijin kam, amma miji tunda ban zauna dashi ba ba zan iya yanke mishi hukunci ba, sai dai nasan zaiyi wuya ace marar kirki ne, ki k’ara hak’uri Sarah ki bari ki haihu sannan, idan har babu abinda ya canza sai a mishi magana ya sallame ki.”

Ba race komai ba sai shasheka data dinga saukewa, sun jima haka babu wanda ya sake magana.

Tunda sanyin safiya ta shirya tare da Sabira da dreba ya kaita gidan aunty Bieba aka wuce da Sabira makaranta, ta taho ne dan tasan zai je kuma ba lallai ta iya bijire masa ba, shiyasa ko sauraran Hajia ba tayi ba tana tambayar inda zata je bare ita ta fad’a masa ma idan ya zo, suna tsaka da hira Bieba na farin cikin ganinta kasancewar mijinta ba mazauni bane, tunda ya samu lafiya ya koma yana can, wayarta dake cikin jaka ta shiga kururuwa, ko da ta ciro taga lambar Hajia da sauri ta d’auka tana fad’in “Takwara ya akayi?”

Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace “Ina kika je?”

Kamar tana gabanshi sai kawai ta had’e fuska tace “Ina wani wuri.”

“Wani wuri bashi da suna?” Ya fad’a cikin taushin murya, ita ma a sanyaye ta amsa da “Yana da, amma me yasa kake ka sani? Dan Allah Slahadeen ka rabu dani ka k’yale ni, wallahi na maka alk’awarin baka bebynka da na haifeshi.”

Cikin murya kamar mai shirin fashewa da kuka yace “Sarahhhh! Me yasa ba zaki fahimci ina damuwa sosai akan ki ba? So kike sai na fito na fad’i abinda ke raina ne?”

Da wani mamaki a fuskarta tace “Kai kuma fad’an abinda ke ranka ne kake ganinshi a matsayin k’ask’anci ko? To ka rik’e abinda ke ranka bana so naji nima, amma dai dan Allah ka bari, kaji Abban Waleed.”

Saida ta gama fad’a sannan ta fahimci abinda ta fad’a, da sauri ta rufe bakinta sai ji tayi yace “Please Sarah say it again.”

Cikin basarwa tace “Na ga kamar sunan da kake son saka mishi kenan ne.”

Daga inda yake yayi murmushi yana kallon Hajia dake kai kawo yace “Ke me kika fi so? Mace ko namiji?”

A tak’aice tace “Duk wanda Allah ya bani.”

“Baki da zab’i kenan?” Ya fad’a a hankali, cikin mak’oshi ta amsa da “Um um.”

Cikin lumshe ido yana shafar k’irjinshi yace “Na rok’eki ki zo Sarah, ki dawo mu tafi kinji.”

Kamar zatayi kuka cikin muryar shagwab’a sosai tace “Ba zan bika ba yanzu Slahadeen, ka sani ina girmamaka ne kawai saboda Mamie, baka kasance mai kirki a tare dani ba, Mamie da Mamuh ne kad’ai masu tausayin gidanku, me zaisa na sake komawa inda ake wulak’anta ni? Me zaisa na sake shiga rayuwar wanda bai damu dani ba? Me yasa zan sake kai kaina inda bana da kowa? Bak’in ciki da kuka sune suke zama abokan tarayyata, kayi hak’uri idan maganganuna sun b’ata maka rai, amma ba zan iya tafiya da kai ba.”

Bubbuga k’irjinshi yayi yana jin kamar ya kwala ihu, rufe idonshi yayi dan in baiyi da gaske ba hawaye ne zasu taho mishi, da k’yar ya furta “Sarah kin tsananta min dayawa, dan Allah ki sassauta min ko naji dad’i, ji nake kamar na kashe kaina saboda abinda le fitowa daga bakinki.”

Kawai fashewa tayi da kuka mai sauti har yana jin sautin a kunnenshi, cikin rarrashi da ban baki yace “Ki taimake ni Sarah ki daina kukan nan, ba dai nine na b’ata miki rai ba? Yi hak’uri to daina kukan zan kashe wayar, zan koma gidan ni kad’ai kinji, amma kiji wani abu guda.”

Shiru yayi na kusan second sha biyar kafin yace “Mama tana matuk’ar son ki zama surukarta ta din din din, Mama na sonki fiye da tanda take sona Saratu, Mama tana so ki zauna kusa da ita danta kula dake da kanta, kullum maganarta d’aya ‘yar amana ‘yar amana.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button