SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Tab’e baki yayi yace “Babu inda zaki je Sarah, kina gidan nan har sanda nayi niyyar fitarki daga nan.”
Marairaicewa tayi zatayi kuka ya harareta yace “Wallahi kina yarda kika min kuka zan sake komawa dake filin daga, tunda naga fitsararki iya ta bakin k’ofar d’aki ce, da an shiga daga ciki kike saranda.”
Shashek’a ta dinga saukewa irin yaro yayi zuciya yana cika yana batsewa, gwalo ya mata yace “Ki fashe mana.”
Da gudu ta k’arasa gareshi bata tsaya komai ba ta fad’a jikinshi da k’arfi kamar an turata tana fad’in “Bana so fa.”
Rik’eta yayi yana fad’in “Sarah rufa min asiri dan Allah, ya kike min ganganci da cikin nan ne wai? Anya kuwa kina son shi?”
D’agawa tayi daga jikinshi taja baya tana fad’in “Baka son komai ya same shi?”
Girgiza kai yayi yace “Bana so.”
Ai da gudu tayi tsalle ta haye gadon tana tsalle akai tana fad’in “Sai kace zakayi duk abinda nace sannan zan daina.”
Da gudu shima ya bita ya haye yana neman rik’ota ta zille ta sauka, har yana neman fad’uwa ya take rigarshi ya sake saukowa yana son rik’eta, dariya ta shiga yi tana ta zagaye dashi a tsakiyar d’akin tana fad’in “Kama ni mana, zo.”
Wallahi duk yanda ya so rik’eta saita kubce ya rasa yanda akayi haka, ganin zata iya ja mishi asarar da baya so yasa shi durk’ushewa tsakiyar gadon ya had’e hannaye ya marairaice ya kalleta yace “Na rok’eki Sarah dan Allah ki tsaya, wallahi bana son komai ya sameku ke da shi, Sarah kin jijjigashi dayawa ki tausaya mishi mana.”
Tsayen da tayi kam yasa ta jin mararta na d’an k’ullewa, a hankali ta fara matsowa kusanshi tana fad’in “Kayi alk’awarin ba zaka hukunta ni ba idan na zo.”
Girgiza kai yayi alamar a’a, k’arasowa tayi ta mik’a mishi hannun ya jawota ta hau gadon, kwance yayi yana d’orata kan k’irjinshi, numfashi suka shiga saukewa wani bayan wani sukayi shiru kowa da abinda yake ji kuma yake tunani.
Kai ganin shirun yayi yawa yasa Mama kiranshi a waya, yana d’auka Mama tace “Ina yar amana ta taho su Hajia zasu koma.”
Murya k’asa k’asa yace “Mama nan yar amanarki zata kwana, su tafi kawai.”
Sororo tayi tace “Ina take?”
Saida ya kalli Sarah dake kwance k’irjinshi yace “Mama gata nan bacci ma zata yi, Mama su tafi kawai ita fa ta zo kenan.”
Da mamaki tace “Ban gane ta zo ba? Haka akeyi a garinku to? Kai ba ruwana da iskanci.”
Kallon Hajia tayi ta kashe wayar tace “Ku zo muje idan ya ganku ya bari ku koma tare, ni ba zan iya da fitsararsa ba.”
Cike da dattako Hajia tace “A’a to miye laifinshi? Muje dai naji in da gaske yake saiya mana alfarma mu rakata d’akinta madadin ta shiga ita kad’ai.”
Rankaya sukayi har da Aba dake binsu a baya da Mama tace ya shigo, a k’ofar Mama ta shiga bubbugawa hakan yasa shi sakin murmushi ya mik’e ya kalli Sarah yace “Ko zaki yi kukan jini Sarah sai kin kwana gidan nan yau.”
Sama da k’asa ta kalleshi hakan yasa ya nuna kanshi yace “Ban isa ba kenan kike nufi?”
Girgiza kai tayi tace “Ni ban ce ba ai.”
Fita yayi ita ma ta mik’e ta bi bayanshi, tana ganin sun shigo ta tafi da sauri ta rumgume Hajia tana fad’in “Yawwa Hajia gwara da kika zo, kinga wai ya kulleni babu inda zan tafi.”
Kallonshi Hajia tayi tace “Kai shikenan haka zamuyi da kai, ka samu amarya ka manta dani tsohuwar zuma.”
Murmushi yayi kawai suka sake gaisawa da Aba wanda shi ya shigo dashi da yamma, duk wuri ya nuna musu suka zauna inda Hajia ta tambayeshi wai da gaske nan zata zauna? Saida ya kalli Mama ya kalli Hajia yace “Eh Hajia, ta zauna yanzu, amma zan kai miki ita ta haihu acan.”
Mak’ale kafad’a tayi tana k’amk’ame Hajia tana cewa “Um um! Um um, ni tare zamu tafi.”
Kallonta Hajia tayi a tsawace tace “Saratu kina lafiya wai, ya mijinki ke fad’in yanda za ayi kina nuna ba haka ba, bana son iskanci fa.”
Kallon Hajia tayi da shagwab’a ta mik’e ta koma kusan Mama kamar zata haye k’afafunta tana fad’in “Mamie kin gani ko? Marainiya ake wa tsawa da fad’a.”
Daddab’a bayanta Mama tayi tace “Yi hak’uri kinji.”
Aba ne yace “Hajiata, me yasa ba zaki zauna gidan mijinki ba to?”
Cikin turo baki tace “Abhi baya so na fa, yanzu ma a d’aki saida ya harareni yace ko kukan jini zanyi bai damu ba.”
Yanda tayi maganar yasa kowa darawa har Sabira da suka shigo da ita, girgiza kai Abhi yayi dan ya gane ina matsalar take yace “Yanzu kenan dan baya sonki ne shiyasa ba zaki zauna ba?”
“Eh Abhi.” Ta fad’a tana kallon Salahadeen da shima yake kallonta, kallonshi Aba yayi yace “To kai kaji, yanzu ya kace kenan? Mu tafi da yarmu ko mu bar maka ita?”
Dariya yayi yana sunkuyar da kanshi yace “Aba shirmenta ne fa, ku tafi ku barta kawai zata maimaita abinda ta fad’a bayan idonku.”
Cikin shagwab’a tace “Ba zasu bar ni d’in ba, tunda dai ba sona kake ba, ga inda ake sona saina zauna wajen wanda baya k’aunata.”
Kallonta yayi yace “Ni kike fad’a ma haka?”
D’aga kafad’a tayi tace “Ai gaskiya na fad’a, baka so na baka sona, ko kana so na d’in ne?”
Cike da shak’iyanci ya d’aga mata gira alamar eh, tab’e baki tayi ta nuna wa Mama tace “Mamie kin gani ko yace wai ya tsane ni.”
Da sauri kamar an tsikareshi yace “Inji wa? K’arya take Mama ba haka na fad’a ba.”
Duk dariya suka kwashe mishi har da ita kanta, sunkuyar da kai ya sake yi sai Mama da tace “To me ka fad’a in ba haka ba?”
Shiru yayi bai ce komai ba, kallonsu Aba tayi tace “Alhaji dan Allah ki tashi ku tafi karsu b’ata muku lokaci, randa ya shirya zama da ita da kanshi zaije ya durk’usa gabanku.”
Zunbur Sarah ta mik’e cikin jin dad’i tana fad’in “Yawwa Mamie saida safe, sai gobe zan zo biki.”
D’aga kai yayi da sauri ya kalli Mama da ita ma har ta mik’e yace “Wallahi Mama ina sonta.”
Da sauri ya sunkuyar da kanshi yana rufe baki cike da kunya, Aba ne yace “To kinji me yace ai.”
Rumgume hannaye tayi tace “Ni banji komai ba Abhi, muje dare nayi fa.”
Kallonshi Aba yayi ya mishi magana da ido, tasowa yayi daga kan kujerar ya tsaya gabanta, kallonshi tayi shi kuma ya kasa kallonta, saida ya sauke numfashi ya kalleta ido cikin ido yace ” Ina sonki.”
Cike da jin dad’i tace “Da gaske?”
Da wani mamaki ya kalleta sai kuma ya kalli Mama yace “Mama ki yafe min dan Allah dan zan make yarinyar nan, ya zan fad’a mata abinda ke raina tana k’aryata ni.”
Tallabo fuskarshi tayi da sauri ta sumbaci labb’anshi, saida ta raba bakinsu ta kalleshi ita ma tace “Waleed yana son Abhinshi.”
Da fari kunyar abinda tayi gabansu ne ta lullub’eshi, amma jin abinda ta fad’a yasa shi kallonta, kecewa tayi da dariya ta koma bayan Hajia da duk sukayi k’ank’ara saboda kunya, Mama tuni ta fita daga d’akin suma sulalewa sukayi suka barta dashi yana binta yana fad’in shi ma saita fad’a masa.
Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:22 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*LABARI*
SAMIRA HAROUNA
*SADAUKARWA GA*
鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍
馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃
鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�
Bismillahir rahamanir rahim
5锔忊儯9锔忊儯
Bayan sallah isha’i Farha da kanta ta k’wank’wasa k’ofar ya bud’e mata ta shiga, wuri ta samu ta aje kwanukan abincin ta d’ago ta kalleshi, duk da yaji nauyi daya ga ita ce amma bai nuna a fuska ba, jawota yayi ya rumgume yana fad’in “Kina can kina ta wahalar min da kanki ko?”