NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Murmushi tayi cike da b’oye abinda ke ranta, ita da ko zuwanshi gidan bata sani ba, sai dubawa tayi ta ga motarshi sannan taga amaryarshi ta b’ata, a k’arshe aka sanar da ita suna tare, amma ji ya murshe ido yana kallonta, wata ajiyar zuciya ta sauke tana sakin murmushin jinjina rashin kunyar maza, kallon kwanukan tayi tana fad’in “Ga abincin nan na kawoma maman jaririna.”

Kallonta yayi ya had’e gira sama da k’asa yace “Ni kuma fa?”

Murmushi tayi tace “Idan maman jaririna ta ci ta k’oshi ta rage saita bawa Abban jaririna.”

Sakinta yayi ya zauna kan kujera yana d’ora k’afa d’aya kan d’aya yace “Sai kije da kanki ki kai mata to.”

Kallon tausayi ta masa tace “Ayya, wai hushi ne wannan? To ayi hak’uri na tuba.”

Turo baki yayi yace “Um um, ba an nuna min banda mahimmanci ba.”

Dariya tayi ta kamo hannunsa tana fad’in “Yanzu dai ka fara kai mata abincin ta ci dan Allah, daga baya sai kayi shagwab’ar taka dan na lura ka fara sangarce mana.”

Dariya yayi yace “Zaku d’auki mataki ne?” Jinjina kai tayi tace “Sosai ma, wasu biyu zamu nemo mu had’aka dasu.”

Dariya yayi sosai ya d’auki kwanukan yana fad’in “Lallai zaku sake min gata a karo na ba adadi, ai ni da banzata in haka ta faru.”

Hararanshi tayi tace “Wai kana nufin zaka so yanzu in aka k’ara maka?”

Shima hararanta yayi yace “Me kuwa zai hana uwar gidana.”

Tab’e baki tayi tace “Humm! Ba kuwa za’a d’auki matakin ba.”

Tana fad’a ta nufi k’ofar fita tana fad’in “Saida safe, ka gaishe min ita.”

Tsabar dukan cikinta kawai yace “Wane saida safe kuma? Ina nan tafe zuwa wajenki ai, kin tab’a ganin na kwana ba tare dake ba?”

Girgiza kai tayi ta kalleshi tace “Dan Allah kar ka zo, ita ma hakk’inta ne a kan ka, na barta mata kai har sanda zata koma, dan naji Hajia tace tana so ta je can ta haihu.”
Girgiza kai kawai yayi yana murmushi har ya koma d’akin ita ma ta fita a d’akin.

Anyi bikin Mamuh lafiya lau kuma kowa ya koma inda yake, sanda su Hajia zasu tafi su barta saida tayi kukan tab’ara Mama kuma na biye mata tana rarrashi, haka suka juya suka tafi sai dai a sirrance Salahadeen ya wa Hajia alk’awarin kai mata Sarah ta haihu acan, amma yace kar ta bari Sarah ta sani dan yana so ya wahalar da ita kawai.

Daga ranar zamanta ya koma nan cikin kulawar suruka kuma uwa da kuma miji da kishiya, Farha ta ladabtu sosai ta b’angare d’aya kuma tana azabtuwa da yanda take iya hango fifiko tsakaninta da yar uwarta a idon mijinsu, ba zata tab’a kiranshi marar adalci a tsakaninsu ba, amma dai yanda ta saka ido a kan kowane motsinshi yasa take ganin yafi rawar k’afa akan Sarah. Kulawa suke bata sosai wanda yanzu take shiga madafa tare da Mama da Iffa wani lokacin ma tare da Farhar dan koyon girki, tana mayar da hankali akan komai amma tana da son wasa da farin ciki da ganin ta kaucewa kowace damuwa, k’iba kawai take k’arawa wacce ta dinga kuka tana damuwa tana wa Mama k’orafi, ita kawai bata so tayi k’iba, ranar data shirya fara motsa jiki dan ta rage ranar gidan kamar zai kama da wuta, dan kaca kaca Salahadeen ya mata da masifa da sababi, ita kuma ta dinga billi tana cewa sai tayi, daya je kamata kuma ta b’oye bayan mama, saida yace ko bayan idonshi ta motsa jikin da zai cutar da ita da abinda ke cikinta bai yafe ba, dariya ta masa ta nuna ko a jikinta, a k’arshe tace ai mijin biza ne dan haka babu umarnin sa wa ko hanawa.

馃ぃ Zo kaga kuffan baki wajen Salahadeen har dare yana nanatawa mama wai ta kirashi mijin biza, shi fa in bai b’alle mata hak’ora ba ba zai huce ba, kasancewar kwanta ne bata yarda taje d’akin ba, banza yayi da ita kamar gaske har aka shiga bacci, Mama tayi tayi da ita ta koma d’akinta saita fashe da kuka tace ai cutarta zaiyi, haka suka kwanta lafiya lau cikin sallama. Ita dai a bacci taji ta d’anyi sama kad’an kuma ta bud’e ido amma taga duhu, saita d’auka ko mafarki ne take kawai ta ci gaba da bacci, tana bud’a ido ta sauke akan Salahadeen daya k’ura mata ido, ai zabura tayi sai taga ashe d’akin ne ya maido ta.

A tsorace ta tambaye shi “Mr. me ya kawo ni nan? Ya akayi na zo nan?”

Mik’ewa yayi yana cire doguwar rigarshi yace “Kin manta mijinki ya k’ware wajen canzawa mutane wurin zama.”

Tab’e baki tayi tace “Wallahi dai kaji tsoron Allah wannan ba sarar k’warai bace, in bakayi hankalin ba wata rana zaka jefa kanka a matsala.”

Kallon daya mata yasa ta saukowa daga kan gadon tana fad’in “To ni zan tafi saida safe.”

Juyowa yayi ya rumgumota ta baya ya rad’a mata a kunne “Ki tafi ina? Ai sai kin gama karb’ar hukuncinki Hajia, kina nufin duk kin tattaka ni a banza kenan yau? Ai abinda kika min ko kare ba zai ci ba Hajia.”

“Ahhhhh..wayyo mamie cikina, cikina mr…” Ta dinga ihu tana dafe ciki, rudewa yayi kuma yana tambayar lafiya? Da haka ta shirgashi tace ai cikinta ke ciwo dole ya manta da maganar hukunci. Cikinta yanzu wata bakwai kenan ya girma sosai kamar ba cikin farko ba, shi da mama na mata shirye shiryen tafiya amma basu bari ta sani ba ko ta fahimta, so yake kawai ya bata mamaki.

Ranar da suka shirya tare da Mama da Salahadeen suka kaita, tsabar murna da farin cikin da Sarah tayi saida Salahadeen ya k’waci kanshi sanda ta cumimiyeshi tana sumbatar bakinshi a gabansu, kwana biyu sukayi amma kuma da zasu tafi duk sai taji ba dad’i, dan har k’asan zuciyarta tana son Mama saboda kamar uwa take kallonta, Salahadeen kuma tana son shi da gaba d’aya zuciyarta. Saida ya tabbatar ya ajiye mata duk wani abun buk’ata na ci da sha da abinda zata iya buk’ata idan lokacin haihuwarta yayi sannan suka tafi bayan ya lodawa Hajia isassun kud’in da zasu ishe su, duk da dai yace zai riga lek’owa kuma yana fatan ta haihu sanda yake nan, amma dai bai bar komai ba saida ya tabbatar yayi.

Suna komawa gida kuma sun samu Farha a asibiti tare da Iffa an mata k’arin ruwa, labarin da likita ya basu yasa Salahadeen kamar ya k’urma ihu dan dad’i, ita ma tana da juna biyu tsawon wata biyu, yayi farin ciki sosai yayi godiya da ubangijin daya azurtashi arzik’in da ba kowa yake wa ba. Kulawa ita ma ta dinga samu daga b’angarenshi da Mama.

Cikin hikimar ubangiji ranar da Sarah ta koma awo aka bata sati biyu ta fad’a mishi yace zai zo nan da kwana biyu, ranar da sukayi wayar a yammacin ranar nak’uda mai tsanani ta taso mata, da taimakon Lariya Hajia suka kaita asibiti sai Aba daya same su acan, kafin ta haihu kusan dangin duk sun hallara, dan yanzu har wanda basa k’aunar mahaifinta a da yanzu suna son ta, ba dan komai ba sai dan kyautarta gare su da kuma girman da Hajia ke da shi a dangin, Sarah tasha wahala sosai dan tun da aka kaita da yammar nan saida asuba ta haihu, kuma nak’uda ce ba mai kwantawa ba, amma a k’arshe Allah ya sauketa lafiya ta haifi d’anta namiji kyakyawa sak ita.

Saida ta haihu kad’ai Hajia ta yarda Aba ya kirashi, dan cewa tayi kar a tayar musu da hankali a bari har aga abinda Allah yayi kawai, murna kam ba’a magana musamman Salah daya rasa inda zai saka kanshi, tabbas da yasan tana can tana nak’uda daya tafi, duk da babu abinda zai iya mata amma zai je ya tayata yin ihu a sanda rad’ad’i ya mintsineta, ko da rana ta fito Salah na kan hanyarshi ta tafi Agadez dan ganin matarshi da jaririnshi, sai Mama da tace zata je bayan kwana biyu ita ma.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button