NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Ko da ya isa lafiya har an sallamesu suna gida ana danbarwa da Sarah akan bawa yaro nono, da fari tace kunya take ji, sai kuma tace ita ba zata shayar da shi ba sai dai a nemi mai shayarwa da madara, a k’arshe kuma tace ciwo ke akwai, kukan yaron ne ya fara tarbarshi tun a farfajiya, har ya shigo falon duk bai kula da mutanen dake d’akin ba, babu shima wanda ya kula dashi sai kallon Hajia da tayi tsaye gaban Sarah Bieba kuma zaune gabanta da yaron ana ta rarrashi.

Fito da nonon tayi ta saman riga Bieba ta d’ora mata shi akan k’afafu, saida aka wanke mata nonon da sabulu sannan ta dona kanshi, Bieba ce tace “D’an d’aga k’afarki sama dan kan yaron ya kai.”

Hajia ce tace “Nonon ne wani munafiki dashi can cikin k’irjin a tsaye ba lank’wasawa.”

Daga k’ofar d’akin ya kalli Hajia yana murmushi a ranshi yace “Haka nake son shi Hajajju.”

Yanda Bieba ta fad’a mata tayi, cikin tsananin buk’atar nonon uwa yaron ya cabki nonon yana ja da k’arfi, abunka ga fari ne kuma bai tab’a kama nonon ba ai wata k’ara ta saki tare da zabura ta mik’e k’afarta, yanda yaron yayi kamar zai fad’i tare da tsanyara kuka yasa Salahadeen wata irin suka tsakiyar d’akin, har ga Allah babu wanda ya ga shigowarshi, duk kusancin dake tsakanin Bieba da ita da saurinta wajen karb’ar yaron saida ta makara, kawai gani sukayi har ya d’auke yaron a jikinshi yana ma Sarah wani kallo.

Duk da shima ba daidai ya rik’eshi ba amma babu wanda ya iya magana sai zuba mishi ido, tana ganinshi gabanta ya fad’i ta shiga sinne kai tana kallon aunty Bieba, wata shegiyar k’wafa yayi yana mik’awa Hajia yaron yana hararanta yace “Baki san ciwon kanki ba Saratu, amma zan daidaita miki zama wallahi.”

Sunkuya kai tayi tana mishi gwalo a b’oye, dungure kanta aunty Bieba tayi hakan yasa ta bushewa da dariya tana rufe bakinta, saida ya matsa da kyau ya sake tara hannu Hajia ta aza mishi yaron tana fad’in “Wai kai yaushe ka shigo ma kamar wani aljani?”

Bai ce komai ba sai kallon bakin yaron da yake yana kuka har rawa bakin keyi, kallon Hajia yayi yace “Wai me ya same shi?”

Da sauri Sarah ta kalleshi tace “Kawo shi nono zan bashi.”

Rik’e haba Hajia tayi tace “Kinga iskanci ko, kenan mune kika raina Sarah?”

Kallon Hajia tayi ta mata alama tayi shiru kar yaji mana, hararanta tayi tace “Sai na fad’a d’in ba zanyi shirun ba.”

Dariya yan d’akin suka d’auka sai Hajia data kalleshi tace “Kana ji ko Salala, yarinyar nan tun shekaran jiya data haihu har yau bata ba yaron nan nono ba sai madara ake bashi da ruwan zam zam, kai nifa na gaji da iskancin yarinyar nan ma wallahi kawai ka d’auketa ku tafi.”

Wani murmushi yayi ya kalli Sarah yace “Hajia ku bamu wuri dan Allah yanzu zai sha ya k’oshi.”

Mik’ewar da sukayi yasa ita ma ta mik’e zata fita ya tare gabanta, kallon Hajia tayi tace “Kin gani ko Hajia, ai dai ke kika ci yanzu jikina d’anye baya son wahala ko?”

Fita Hajia tayi tana fad’in “Eh mana, amma ni zanji dad’i in ya ci ubanki ai.”

D’ora hannu tayi a kai tace “Shikenan Hajia ta zagi marainiya, shiyasa nake so Mamie wallahi ita tasan hakk’in maraya.”

Ka rantse yanda yake kallonta tirsasata zaiyi, amma ko da suka fita saiya shiga rarrashi da koro mata bayani mai kashe jiki a cikin shayarwa da alfanun dake cikin ita ta shayar dashi da kanta d’in, da taimakonshi ya gyara mata ta d’orashi a nono, kuma ko dama gashi ruwan nonon sun taru saboda tana samun abinci mai kyau tana ci, ya jima d’akin nan har rana tayi kafin ya fita.

Bayan kwana biyu Fatsima ta iso, kasancewar daren jiya ta shigo yasa tayi sammako gidan, Sarah na bacci Hajia ta shiga ta taso ta, d’akin Hajiar suka shiga ta gaishe da matar data gani ta amsa da sakin fuska, kallonta tayi tace “Cire kayanki ko.”

Da rashin fahimta ta kalleta ta juya ta kalli Hajia, kamata Hajia tayi tace “Karki damu takwarata, gyara ne za’a miki kinji.”

Turo baki tayi tace “Kuma sai na cire kayana a gabanku?”

Dak’uwa ta mata tace “Gidanku, can garin naku ba da d’an wandon wanka kuke wutsilniya a gaban mutane ba.”

Dariya kawai tayi dan ba zata ce bata tab’a ba, amma ai a da ne kafin ta musulunta, a hankali ta shiga zame rigarta har ta cireta, mararta data d’an taso ta dafe sai k’irjinta daya d’an cicciko shima, bata ankara ba Hajia ta kai hannu kan nononta na dama tana fad’in “Haba dubi nonon shiyasa tunda kika haihu har yanzu yaron baisha ya k’oshi ba.”

Dariyar da Fatsima tayi ce tasa ta kallonta tace “Allah kuwa Fatsima irin nawa ne, kinga idan ina bawa yaro nono saina d’aga kanshi sosai yake iya tsotsa.”

Sarah dai turo baki kawai take yi ta shiga zame dogon wandon, saida ta rage daga ita sai pant d’inta bak’i da kunzugunta tq nuna mata leda tayi data shinfid’a tace “Zauna.”

Matsawa tayi ta zauna ita kuma ta matsa ta shiga shafeta da wani had’i, saida aka gama kaf ta zauna gabanta da tarin robobi da k’aton gwangwanin madara, haka ta shiga had’a mata wasu gari tana bata tana sha, saida Hajia tayi ta lallab’ata tasha, minti talatin aka samu sanna tace ta shiga tayi wanka akwai ruwa masu d’umi, mik’ewa tayi ta shiga tayi wankan ta fito, sake nuna mata ledar tayi tace “Zauna.”

Komawa tayi ta zauna aka shiga shafa mata wani had’in, sai taji na yanzu yafi dan tana jin k’amshin kamar lemun tsami a ciki sai kuma k’arnin man kad’e (blanga), tana gama shafa mata ta d’auko roba da ruwan zafi da kunnen turare da k’aton bargo, zaunawa tayi ta jibga mata bargon ta rufeta sai inda ta zura hannunta tana juya ruwan kawai.

Ba’a kai ko ina ba Sarah ta shiga ihu tana fad’in “Hajia na mutu, na mutu Hajia, k’onewa nake fa, zafi zafi Hajia bana so.”

Cikin rarrashi Hajia tace “Haba takwarata kunya zaki bani, kiyi hak’uri mana kinsan dai ba zan cutar dake ba ko?”

Duk kururuwar da take Fatsima bata saurareta ba dan ita inta fara aiki to bata jin bari saita gama, saida ta tabbatar suracin ya shiga jikinta ta d’auke mata bargon, tuni Sarah ta canza kala ga masara na abinda aka shafa mata ga ja na wahala, wanka ta shiga inda ta samu ruwn lalle da sabulun karanfani tayi wanka sosai, tana fitowa towel na musamman ta bata ta goge jikinta da wani mai shima na musamman, sannan ta bata shi tace ya zama na shafawarta sannan karta yarda ta fita a rana, in ya zama dole to ta rufe fuskarta, tana cikin saka kaya ta bata robar dake d’auke da yankakkar kankana da garin raihan a ciki da madara peak ta bata ta shanye, daidai ta gama saka kayan kuma Hajia ta zaunar da ita ta ci naman da tuni dama ta dafa mata shi, ta d’auka dad’i ke akwai amma ba haka bane, shima kamar sauran lallab’ata tayi ta daure ta ci.

Saida ta idar suka fito daga d’akin tana sauke ajiyar zuciya tana fad’in “Nagode Allah angama, wannan abu ai sai ka mutu aka sake yi gobe.”

Dariya Hajia tayi tace “Kinga kuma sati biyu za ati ana miki.”

Zaro ido tayi ta kalleta tace “Hajia sati biyu? Tabb ashe zan bar miki gidanki.”

Dariya sukayi inda Sajida na d’ora ido a kanta tace “Kai yer uwa amma wallahi kinyi kyau, wai kin ganki kuwa?”

Cike da kuri Hajia ta kalli Sarah tace “Uhum kinji ko? Kad’an ma kenan yarinya, ai sai mijin nan naki ya ban tukuici ko na k’i bashi ke.”

Kallon Sajida tayi tace “Ina lallen?”

Mik’o mata robar tayi data kwab’a ita ma ta amsa ta bawa Fatsima, zaune tayi kusan Sarah ta nuna mata ta zauna kan pillown data d’ora mata, zaune tayi inda ta mik’e k’afafunta cikin nutsuwa Fatsima ta shiga yi mata lallen nan da shi kanshi wani sirri ne a cikin k’unsashi, sun jima suna lallen da ba irin kawai mai sauk’in nan bane, da k’yar aka gama na k’afafu aka koma kan hannaye suma tas aka zane mata yatsunta da jan lallen na hausa, zuwa lokacin da aka idar rana tayi abinci Hajia ta dinga bata a baki saboda lallen dake hannunta, saida ta ci ta k’oshi a madadin ta bata ruwa kawai ta bata wasu ruwa masu kama da tea, minanas ne tare da karanfani aka dafa da d’an ganyen anana a ciki sai zuma da aka saka a madadin sugar, duk da basu da zafi sosai amma dai bata ji dad’in sha ba dan kamar shayi ne kasha bayan ka ci abinci mai zafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button