NOVELSSALAHADEEN COMPLETE NOVEL

SALAHADEEN COMPLETE NOVEL

Alhamdulillah
13/04/2021 脿 04:22 – Mom Lateef: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
SALAHADEEN
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

           *LABARI*

SAMIRA HAROUNA

  *SADAUKARWA GA*

鉂わ笍 MASOYA NA鉂わ笍

馃挮鉁� TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)馃専
(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)馃

鈽� [ T.M.N.A] 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
          *FIN*

Bismillahir rahamanir rahim

                 6锔忊儯0锔忊儯

Duk wani gata da ake wa yar gata miji da uwar miji da kuma dangi sunyi wa Sarah shi da d’anta wanda ya ci sunan Waleed, iya danginta kawai sukayi walimarsu, kuma komai Salahadeen ne ya d’auke nauyinshi, har bayan biki kuma Fatsima na mata siraci da gyara na musamman, ita kanta taji a jikinta lallai ta banbanta da Sarah baya, yanzu banda wani ni’imataccen d’umi mai surki da k’amshi da ni’ima babu abinda ke fita a jikinta.

Ba iya gyaran kawai take mata ba har da ma koya mata zamantakewa, yanda zata kula da mijinta da kuma yanda zata tafiyar da kishiyarta a siyasance, ga kuma girki da Bieba ta dinga koya mata ita, haka Fatsima tayi sati biyun ta koma suka ci gaba da aunty Bieba.

Daga cikin abunuwan data koya a wajen Fatsima yasa ko da Salahadeen ya fad’a mata yana so ta koma da tayi arba’in bata mishi gardama sai amsawa da ba laifi, yayi mamaki dan Saratun daya sani ta baya zata iya mishi billi tace ba haka ba, shi kanshi yana ganin canji sosai, yanda ko waya suke saita mishi ruwan manya manyan kalamai ta saukar mishi da kasala, haka zata dinga kashe mishi murya kaji kamar tana kuka kamar tana rera wak’a kamar kukan tsintsaye, haka in hotonta zata tura mishi dana yaro saita tabbatar ta d’auki sashen jikinta wanda zai d’aga mishi hankali, shi yasa ya ci alwashi yake kuma hannunta mai sanda data kiyaye ranar da zai matseta a hannunshi.

Yanzu haka maganar auren Sajida ake da wani balarabe da Allah ya daidaita su, tattaki sukayi su ka zo k’asarta neman aurenta, basu bar komai ba daya shafi aladarta saida sukayi, dan su wannan d’in yafi musu sauk’i da auren balarabiya, wacce baka kashe dayawa ba ka kashe million ashirin da biyar, an gama komai an tsayar da lokaci wata takwas mai zuwa lokacin suna hutun k’arshe.

Richard ma an shiryu sosai an zama ustaz ko kuma muce d’alibi, yana d’aukar karatu a wajen limamin nan wanda a k’arshe shima ya tura shi saudia, yana jin dad’in rayuwarshi ta yanzu dan tafi sauk’i da yanci da farin ciki.

Sai Daniel da tunda ya dawo hayyacinshi ya gane me ya faru bai yarda ya b’ata lokaci ba wajen barin k’asar, dan baya so sunanshi ya fito police su kama shi, ya koma da b’acin rai da rashin cikar buri, wannan burin zai dinga tabbata ne kawai a mafarkinshi, amma a zahiri kam ya mishi nisa.

Kafewa da yayi baida hannu a cikin saceta da kuma binciken da sukayi duk bai nuna musu da hannunshi a ciki ba yasa suka sallame shi amma da cewa zasu iya nemashi idan buk’atar hakan ta taso, ko da ya fito daga nan ya wuce gida k’ungiyarsu ya nufa, yana zuwa shugabansu ya tuhumeshi kan rashin cika musu alk’awari, dan haka zasu d’auki fansa a kanshi kamar yanda aka yi, cikin tsafi yayi suddabaru saiga wuta a hannunshi, zai juyar da ita inda Kabeer yake wanda ya gama tsorata kawai wata sarautar Allah ta faru, sai kace wani ne ya busa wutar sai kuwa tayi wuf a hannun rigarshi, tana kama hannun rigar saiya zabura rik’e rigar da hannun mai wuta, sai can ma ya kama sai kawai ya fara sauri wajen ganin ya kasheta, abu kamar wasa sai duk suka mik’e suka tayashi kashe wutar, ba sarki sai Allah suna k’ok’arin kashe wutar ita kuma tana k’ara mamaye jikinshi, ko da suka ga abun ya fi k’arfinsu kawai suka nemi hanyar tsira, yau kuma duk tsafin nasu sai ya k’i fitar dasu daga wurin, ba k’ofa ke akwai ba kuma shiyasa daga su har shi babu wanda ya tsira wannan wuta ita ta cinyesu har tokarsu.

Tunda yaje ya tura aka d’aukota suka zo gidan yaron ke hannunshi yana kallonta, mamakin yanda daga ita har yaron sukayi wata irin k’iba mai kyau da birgewa, jikinta yayi wani irin luwai luwai sai d’aukar ido take, tsabar yanda tayi yelow mai haske saika rantse babu jini jikinta, shiyasa ma ko da suka shiga d’aki ya shiga mata sharri yana shammaceta da zolayarta, ita kam dariya take tana fad’in kwanciyar hankali ne ya jawo hakan.

Tunda ya shiga ya sauke wata irin ajiyar zuciya tare da k’amk’ame ta, rufe ido yayi yana jin yanda wani d’umi mai dad’in gaske da zautar da tunani ke ratsa shi, lallai ta zo da zuwanta wannan karan, ta zo mishi da salon mugunta da zai bayyanar da wawancinshi a fili, ta zo da salon da zai nuna shi matacce ne akan ta. Ita ma sai lokacin ta fahimci abinda aka mata, lokacin ta k’ara ganin kimar abinda aka mata ta kuma d’auri niyyar ci gaba da yi ba tare da wasa ba.

Har yanzu Sarah bata san wahalar raino ba, dan yaro na yin kuka mama zata d’auka, in ba mama ba kuma Farha wacce ke fama da kanta, inba ita ma Uffa wacce har yanzu ita ma ba tsayayyen saurayi, rayuwa suke cikin farin ciki da k’aunar juna. Bayan wata shida Farha ta haihu, saida aka gama hidimar komai Sarah ta kai mishi abun kari b’angarenshi, tana aje kwanukan ya kalleta yana zama kan kujera yace “Me kika dafa?”

Za tayi magana kawai taji bakinta ya cika da yawu, cikin jin haushin tunanin abunda ya sameta na wannan tofe tofen yawu ta wuce toilet d’in dake falon, saida ta tofar ta kuskure bakinta ta fito tana fad’in “Abinda auntyna take so na dafa.”

Kallonta yayi yace “Allah ni ma ka bani auntyn nan ko zan huce takaici.”

Dariya tayi tace “Ameen.”

Tana cikin zuba mishi taji yace “Yaushe zaki ji asibiti su fad’a miki ranar da zaki fara zuwa awo?”

Da wani irin fad’uwar gaba da tsoro ta saki cokalin hannunta, yanda ta kalleshi kamar yace zai kashe d’anta ne yasa shi tintsirewa da dariya, rufe baki yayi yana kallonta yace “Miye?”

Numfashi ta sauke tace “Sai naji kace awo.”

“Um! Haka nace.”

Kafeshi tayi da ido tace “Awon me?”

“Na me kika sani?” Ya fad’a kanshi k’asa, a hankali tace “Na ciki dana yaro, saina awon hawan jini ko ciwon sugar.”

“To ke wane kike tunanin zai iya samunki yanzu?”

Rarraba kdo tayi sai kuma ta matsa kusanshi tace “Gabana fad’uwa yake, fad’a min dan Allah.”

Saida ya mik’e daga kujerar yaja baya sosai sannan yace “Hajia Saratu ciki ne da ke in baki sani ba, kuma a k’alla wata biyu dana lura da hakanan, kije a duba min ke dan mu tabbatar.”

Sam bata da hujjar da zata k’aryata hasashenshi, dan abubuwan da take ji ita kanta suna bata mamaki, canjin data gani ko take gani yana bata mamaki, sannan ranar Mama ke wasa da Waleed take fad’in ai an kusa fiddaka a nonon ma ka ba wasu wuri suma su sha, hannaye biyu duka ta d’ora akai ta durk’ushe tana zabga wata uwar ihu da fad’in “Wayyoooooooooooo!”

Tintserewa ya sake yi da dariya ya juya ya fita da gudu, mik’ewa tayi ta bi bayanshi da gudu tana kuka da iya gaskiyarta, falon mama ta isa shi kuma tuni ya fice a gidan, kuka ta azawa mama wai sai taje likita an tabbatar mata, in gaske ne gaskiya akwai matsala, taya zata yarda ta samu ciki duka yaronta watanshi cikin na bakwai, haka ta kira Hajia tana kuka tana fad’in “Ai duk ke kika cuce ni, nace zan d’auki maganin asibiti kika hana kika zigashi ya hana ni wai sai dai na hausa, gashi yanzu na samu ciki dan Allah ya zanyi, ke ce zaki haife shi ko wa?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button